Editor

9513 Posts
2023: Adamu ya nemi dafawar Ubangiji kan nasarar Tinubu

2023: Adamu ya nemi dafawar Ubangiji kan nasarar Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nemi dafawar Ubangiji don ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyarsu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kai bantensa a babban zaɓe mai zuwa. Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci shugabancin jam'iyyar (NWC) zuwa ofishin kamfe ɗin Tinubu/Shettima da ke Abuja a farkon wannan makon. Sa'ailin da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban APCn ya yaba da tsare-tsare da shirye-shiryen da Tinubu ke yi don gudanar da yaƙin neman zaɓensa. Adamu ya faɗa wa Tinubu, “Duba da ƙoƙarin da ka yi, hakan wata alama ce mai nuni…
Read More
William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Laberiya ƙasa ce ta 'yantattun bayi, wadda aka gina da musguna wa 'yan ƙasar lokacin da aka zaɓi William Tubman a matsayin shugaban ƙasa. Bayan haɗa kan mutane, ya shirya ƙasar bisa tsarin ci-gaba wanda bai samu ba. An haifi William Vacanarat Shadrach Tubman ranar 29 ga watan Nuwamba 1895. Ya fito daga yankin kudu maso gabashin Laberiya, daga garin da ake kira Harper na gundumar Maryland. Sunan wuraren ya yi kama da na Amurka, saboda Jamhuriyar Laberiya ta ayyana samun 'yanci daga Amirka a shekarar 1947 da 'yantattun bayi suka yi, waɗanda suka dawo daga…
Read More
Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ahmed Baba ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai na Afirka a ƙarni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari'a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane. Lokacin da Ahmed Baba ya rayu: An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce a Araouane, kimanin kilomita 250 Arewa maso Yammacin Timbuktu, birnin da ke arewacin Mali. Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunƙasa a matsayin cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara. Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu…
Read More
Hanyoyin magance zargi a zaman aure

Hanyoyin magance zargi a zaman aure

Cigaba daga makon jiya Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da saduwa a wani sabon makon a filinmu na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini, Manhaja. Za mu cigaba daga inda muka tsaya a maudu'inmu na makon da ya gabata. Inda muka bayyana wa masu karatu ma'anar zargi a gidan aure da kuma abubuwan da suke jawo zargi a zaman aure da suka haɗa da: kishi mai tsanani, rashin yarda da kai, rashin fahimtar juna, rashin soyayya, aikata mugayen laifuka a ɓoye, rashin ƙauna, buɗe ƙofar zargi, da sauransu. A wannan mako za mu cigaba. Sannan za mu kawo muku bayanai…
Read More
Ya kasa samun aiki saboda yana da fuskar yara

Ya kasa samun aiki saboda yana da fuskar yara

Wani mai shekara 27 a garin Dongguan a ƙasar Chana yana shan fama wajen neman aiki, saboda fuskarsa tana nuna ta bai kai shekara 20 ba. Matashin mai suna Mao Sheng, ana yi masa kallon ƙaramin yaro da shekarunsa suka gaza ya samu aiki. Duk lokacin da matashin ya ce, ya kai shekara 27, mutane ba su yarda da hakan, inda suke yi masa kallon bai wuce shekara 10 ba. Sai dai yayin da wasu suke ganin hakan a matsayin wata albarka ce, saurayin yana ganin cewa ana aibanta shi, tunda hakan ya hana shi samun aiki. Yawancin masu ɗaukar…
Read More
Waƙa a wurina gado ce, inji Hajara Idris

Waƙa a wurina gado ce, inji Hajara Idris

“Sanadin soyayya na fara waƙa” “Harkar fim aba ce mai kyau, sai dai ga waɗanda suka ɓata ta" DAGA ABBA MUHAMMAD Hajara Idris, wadda aka fi sani da Hajjo a masana’antar waƙoƙi da finafinan Hausa, sabuwar mawaƙiya ce kuma jaruma. Domin bata jima da bayyana a masana’antar, duk da ta daɗe da fara waka. Hajjo dai ɗiya ce ga fitaccen mawaƙin asharallen nan da ke zaune a Kaduna, wato marigayi Idi Moris, kuma ita ce babbar ‘yarsa. Hajara yarinya ce son kowa ƙin wanda ya rasa. Haka kuma ba ta da girman kai, ba ta da ƙin mutane, ga ta…
Read More
Barci ya kwashe wasu matuƙan jirgin sama a sararin samaniya

Barci ya kwashe wasu matuƙan jirgin sama a sararin samaniya

Barci ya ɗauke wasu matukan jirgin sama biyu mallakin ƙasar Habasha a yayin da ya ke tsaka da balaguro a sararin samaniya. Jirgin ƙirar Boeing 737 mai ɗauke da fasinjoji 154, ya tashi ne daga birnin Khartoum na Ƙasar Sudan zuwa birnin Addis Ababa na Habasha a farkon makon nan. Masu tuƙinsu na sararin samaniya da nisan kafa 37,000 tsakaninsu da qasa, sai barci ya ɗauke su gabanin isowarsu filin jirgin saman Addis Ababa inda za su sauka. Masu kula da tashi da kuma saukar jiragen sama a filin, sun yi ta ƙoƙarin ankarar da su cewa suna daf da…
Read More
Atiku ya tallafa wa ‘yan Kasuwar Kwari da miliyan N50

Atiku ya tallafa wa ‘yan Kasuwar Kwari da miliyan N50

…yayin da Ibrahim Sekarau ya sauya sheƙa zuwa PDP Daga BABANGIDA S GORA KANO. Ɗantakarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya jajanta wa 'yan kasuwar Kantin Kwari bisa ɓarnar da ruwan sama ya yi musu, tare da ba su tallafin naira milyan hamsin dan rage raɗaɗin asarar da suka yi. Wannan na zuwa ne a lokacin da Wazirin Adamawan yake karɓar tsohon sanatan Kano ta Arewa, Malam Ibrahim shekarau daga Jam'iyyar NNPP ranar Litinin ɗin makon nan a gidansa da ke Mundubawa, Jihar kano. Atiku ya ce, abin a tausaya ne iftila'in da sami 'yan kasuwar na…
Read More
Adalci shi ne tushen haɗin gwiwa

Adalci shi ne tushen haɗin gwiwa

Daga BELLO WANG Yau Litinin ne aka ƙaddamar da bikin makon tinkarar sauyin yanayi a nahiyar Afirka na wannan shekara ta 2022, a ƙasar Gabon. Haƙiƙa batun sauyin yanayi na ƙara janyo hankalin jama’a, musamman ma ta yin la’akari da yadda ake samun abkuwar ƙarin nau’o’in bala’u daga Indallahi a wurare daban daban. A shekarar da muke ciki, ƙasashe da dama dake nahiyar Afrika, irinsu Madagascar,da Mozambique, da Malawi, sun fuskanci raɗaɗin wani nau’i na bala’u. Kana an gamu da matsalar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa dake Najeriya, sai kuma jihohin Zinder, da Maradi, da Diffa a jamhuriyar Nijar. A…
Read More
Ƙasar Sin na taimakawa farfaɗowar tattalin arzikin duniya

Ƙasar Sin na taimakawa farfaɗowar tattalin arzikin duniya

Daga CMG HAUSA Yauzu haka, tattalin arzikin duniya na ci gaba da fuskantar matsin lambar da sauye-sauyen yanayin duniya da annobar COVID-19 suka haifar, lamarin da ya sa ake mai da hankali sosai kan yanayin raya tattalin arziki a ƙasar Sin, wadda ta kasance abokiyar ciniki mafi muhimmanci ta ƙasashe da yankuna fiye da 120. Matakan da ƙasar ta ɗauka wajen tinkarar annobar COVID-19 sun ba ta damar daƙile yaɗuwar cutar gami da raya ɓangaren samar da kayayyaki. Kana yadda ƙasar take ƙoƙarin magance samun masu kamuwa da cutar COVID-19, ya sa ta iya kiyaye wani yanayin tattalin arziki da…
Read More