Editor

9513 Posts
Za a ƙara samar da motocin dake amfani da sabbin makamashi a Sin

Za a ƙara samar da motocin dake amfani da sabbin makamashi a Sin

Daga CMG HAUSA Jami’in ma’aikatar sufuri ta ƙasar Sin Li Guoping ya bayyana cewa, gwamnatin ƙasar za ta ƙara samar da goyon baya ga sana’ar ƙera motoci da fasahohin zamani dake amfani da sabbin makamashi. Jami’in ya bayyana haka ne bayan rufe babban taron motoci masu amfani da sabbin makamashi na duniya a jiya Lahadi. Li Guoping yana mai cewa, mataki na gaba shi ne nazari da tsara tsarin rage fitar da sinadarin carbon, kuma za aiwatar da manufar bayar da tallafi don yayata amfani da motoci masu amfani da sabbin makamashi. Li Guoping ya nuna cewa, ma’aikatar sufuri za…
Read More
Siyasar Nijeriya: Har yanzu kamar an gudu ba a tsira ba

Siyasar Nijeriya: Har yanzu kamar an gudu ba a tsira ba

Bisa ga dukkan alamu dai sake maimaita aji za a sayi. Ma'ana a yunqurin talakawa na hutawa da mulkin ɗan Jummai kuma a sake ɗauko ɗan Juma. Al'umman Nijeriya na buƙatar canji, amman har yanzu ba su ɗauko canji ba. Har yanzu al'umma na cikin ruɗu. Kuɗi da ƙabilanci sun yi musu kanwaya, gaba ɗaya kowa ya ruɗe. Wasu suna bin mayaudara, wasu na bin mawaƙa, wasu kam har yanzu suna bin jahilan malamai. Yaushe malamin da ya ke ɗan siyasa zai gaya maka gaskia akan wanda zaka zaɓa? Yaushe mawakin da kuɗi ya ke nema zai gaya maka gaskia…
Read More
Gidauniyar Zakka da Waƙafi ta bai wa ƙungiyar mata tallafin itatuwan waƙafi

Gidauniyar Zakka da Waƙafi ta bai wa ƙungiyar mata tallafin itatuwan waƙafi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato A ƙoƙarin Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato na haɓaka tattalin arzikin al'umma musamman marasa galihu da marayu da zawarawa da inganta yanayin ƙasa, ya sa aka bada iraruwan itace ga wata ƙungiyar mata mai taimakon marayu, zawara da mabuƙata, ƙungiyar ta rayuwar mata wadda ke da makarantar Raoudatoul Ibadurrahmane da ke a garin Maradi jamhuriyar Nijar. A shekara ta 2016 sun ziyarci Jihar Sokoto inda suka ziyarci mai martaba sarkin Musulmi, ma'aikatar lamurran addini da ta mata tare da gidauniyar Zakka da Wakafi ta jihar Sakkwato, inda suka buƙaci haɗa kai da ƙarin…
Read More
Ya kamata a gaggauta hukunta makasan Sheikh Aisami – JNI

Ya kamata a gaggauta hukunta makasan Sheikh Aisami – JNI

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da shugabannin sojoji da su gaggauta gurfanar da sojojin da ake zargi da kisan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Yobe, Sheikh Muhammad Goni Aisami. Ƙungiyar ta JNI ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin ta hannun Babban Sakatarenta, Dokta Khalid Abubakar Aliyu, inda ta ce, ba wai kawai a yanke hukuncin ba har ma da duba yadda aka yi kisan. Ƙungiyar ta kuma ce ya kamata a yi amfani da irin hukuncin ga duk wani lamari makamancin haka a…
Read More
Juyayin kisan gilla ga Sheikh Aisami

Juyayin kisan gilla ga Sheikh Aisami

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Dama kowace rai lalle wata rana za ta ɗanɗani mutuwa, barin duniya ko rabuwar gangar jiki da rai wajibi a rayuwar talikai. Sanadiyyar mutuwa kan bambanta tsakanin masu rai. Wani kan yi doguwar jinya har a fidda rai, wani gajeruwar jinya, wani zai shiga ya rufe ne amma sai a wayi gari rai ya yi halinsa. Akwai waɗanda kan gamu da ajali ta hanyar hatsarin mota ko wasu su samu harin ’yan ta’adda ta hanyar harbi da bindiga. Koma ta yaya lamarin ya faru duk hanya ce ta rabuwa da wannan ran da a ke yi…
Read More
Dalilinmu na umartar ɗalibai biyan Naira 1,000 bayan buɗe Kwalejin da Deborah ta yi ɓatanci ga Annabi – Shugaban Kwaleji, Dakta Hakimi

Dalilinmu na umartar ɗalibai biyan Naira 1,000 bayan buɗe Kwalejin da Deborah ta yi ɓatanci ga Annabi – Shugaban Kwaleji, Dakta Hakimi

Daga AMINU AMANAWA SOKOTO Shugaban Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari dake Sakkwato Dakta Muhammad Wadata Hakimi, Walin Wazirin Sakkwato ya bayyana dalilan da suka sanya hukumar gudanarwar makarantar sanya kowane ɗalibin kwalejin biyan Naira 1000 dama rattaba hannu kan cewa ba za su sake tayar da tarzoma a kwalejin ba, irin wacce aka samu a watannin baya. Shugaban ya dai bayyana hakan ne a tattaunawa ta musamman da wakilin Blueprint Manhaja na Sakkwato, Aminu Amanawa ya yi da shi a ofishinsa. BLUEPRINT MANHAJA: Waɗanne irin matakai ne kwalejin nan ta bi kafin kai wa da sake buɗe kwalejin, biyo bayan…
Read More
Garkuwa: Bayan mako uku ’yan sandan Zamfara sun ceto wasu mata

Garkuwa: Bayan mako uku ’yan sandan Zamfara sun ceto wasu mata

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta ceto wasu mata biyu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Litinin. “A ranar 20 ga watan Agusta, 2022, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara yayin da suke sintiri tare da Nya Mango a ƙaramar hukumar Bungudu, sun ɗauki matakin ceto wasu mata biyu da aka yi garkuwa da su ba tare da wani…
Read More
Yadda sabon Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyi na Ƙasa ke canja fasalin hukumar – Mista Kalu Emetu

Yadda sabon Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyi na Ƙasa ke canja fasalin hukumar – Mista Kalu Emetu

Daga JOHN D. WADA a Lafiya An bayyana sabon Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyi na Ƙasa wato Road Traffic Services (DRTS) a turance wato Dokta Abdul-lateef Bello a matsayin ƙwararren shugaba da a cikin watanni ƙalilan da ya yi a matsayin daraktan hukumar ya cimma nasarori da dama dake cigaba da kawo sauyi mai ma’ana da kuma canja fasalin hukumar a yanzu. Shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Kulu Emetu ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilin mu a ofishinsa dake babbar sakatariyar hukumar a Abuja ranar Laraba 24 ga watan Agustan shekarar 2022 da…
Read More
Atiku ya taya Sarkin Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Atiku ya taya Sarkin Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ɗan takarar Shugabancin Nijeriya na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya aike da saƙon taya murna ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar bisa zagayowar ranar haihuwarsa. Mai Alfarma Sarkin na Musulmi wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a Nijeriya, ya cika shekaru 66 a duniya ranar 24 ga watan Agustan 2022. A saƙon taya Sarkin Musulmin murnar ranar haihuwarsa a shafin sa na Tiwita, Wazirin Adamawa ya ce a madadinsa da iyali, yana taya murna gare shi sannan yana addu'ar Allah Ya ƙara masa lafiya…
Read More
Gwamna Ganduje zai samar da ƙarin jami’o’i guda biyu a Kano

Gwamna Ganduje zai samar da ƙarin jami’o’i guda biyu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jiihar Kano ta yi alƙawarin sake samar da jami’o’i guda 2 a Kano domin ƙara bada damar inganta ilimin matasa a jihar. Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi yayin buɗe taron makon matasa, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin duba a kan matsalolin matasa da kuma lalubo hanyoyin da za a magance su. Taron wanda ya gudanar a rufaffen ɗakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake Ƙofar Mata a ranar Laraba da ta gabata. A cewar Gwamna Ganduje, tuni an tura sunayen Kwalejin…
Read More