28
Aug
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa har yanzu akwai makarantun sakandare 75 da suke a rufe sakamakon ayyukan 'yan ta'adda. Hakan ya fito ne ta bakin babban sakataren ma’aikatar ilimi ta jiha Alhaji Kabiru Attahiru cikin saƙon fatan alheri a wani taro na kwanaki biyu a matakin jiha na gidauniyar samar da manufofin ƙasa kan jinsi a fannin ilimi NPGE A jihar Zamfara wanda hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta ƙasa da haɗin gwiwar hukumar UNICEF suka shirya a cibiyar horas da malamai ta Zamfara Gusau ranar Laraba. A cewarsa, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin…
