28
Aug
Babban Magatakarda na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine a matsayin wani yanayi na bacin-rai, a dai dai wannan lokaci da yaƙin ya cika watanni 6. Guterres dai na gabatar da jawabi ne a gaban kwamitin tsaron majalisar da ke birnin New York a ranar Larabar da ta gabata, ya yi amfani da wannan damar domin jinjina wa Turkiya dangane da rawar da ta taka don sake buɗe tashoshin jiragen ruwan Ukraine don ci gaba da raba abinci zuwa sassan duniya. A cewar Guterres, ziyarar da ya kai ta kasance muhimmiya…
