Editor

9513 Posts
Kwankwaso bai yi mana adalci ba – Shekarau

Kwankwaso bai yi mana adalci ba – Shekarau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce babu gaskiya a batutuwan da jagoran Jam’iyyar NNPP kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi cewa sun shigo jam’iyyarsa a makare. Sanata Shekarau a wata hira da ya yi da manema labarai bayan taron majalisarsa ta Shura a Kano, ya ce har yanzu suna kan tattaunawa da tuntuɓar juna domin sanar da matsayarsu kan ci gaba da zama a NNPP ko akasin haka. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Malam Shekarau…
Read More
Gwamnatin jihar Anambra za ta rushe haramtattun rumfunan a kasuwar NASPA

Gwamnatin jihar Anambra za ta rushe haramtattun rumfunan a kasuwar NASPA

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnati jihar Anambra a yanzu haka ta shirya tsaf don yin rusau ga wasu rumfunan kasuwa da ta ce ba a gina su kan ƙa'ida ba. Ita dai wannan kasuwa ita ce kasuwar sayar da sassan gyaran mota wadda ake fi sani da NASPA da yake a Zone-14 a yankin Nnewi. Kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar, Dakta Obinna Ngonadi, shi ya bayyana haka bayan ziyarar gani da ido da ya kai na rangadin kasuwar tare da shugaban hukumar tsara gine-gine na jihar, Mista Chike Maduekwe. Kwamishinan ya bayyana rashin jin daɗinsa a kan yadda aka…
Read More
Benzema ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Turai na bana

Benzema ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Turai na bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan gaban Faransa Karim Benzema ya lashe kyautar gwarzon UEFA na bana, bikin da aka gudanar da shi a Istanbul na ƙasar Tukiyya a jiya Alhamis. Baya ga Benzema, ɓangaren mata ’yar Spain Alexia Putellas, ce ta lashe kyautar na wannan karo. Karim Benzema mai shekaru 34, da ke taka leda a Real Madrid ya samun wannan nasara a kan yan wasa da suka haɗa Thibaut Courtois da ke ƙungiyar ta Real Madrid da kuma ɗan ƙasar Belgium daga Manchester City Kevin de Bruyne. Karim Benzema ya zura ƙwallaye 44 a wasanni 46 da ya…
Read More
Ba Gawuna takarar Gwamnan Kano ƙwarewar siyasa ce ta Ganduje – Shinkafi

Ba Gawuna takarar Gwamnan Kano ƙwarewar siyasa ce ta Ganduje – Shinkafi

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano An bayyana cewa zaɓo mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, a ba shi takara ta neman zama gwamnan Kano mai gadar Gwamna Ganduje, iya siyasa ne, gogewa da ƙwarewa irin ta Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Auwal Ahmad Shinkafi, shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar sansanin Alhazai ta Kano a lokacin da yake jawabi a sansanin Alhazan a ranar Litinin da ta gabata. Shinkafi ya ce Gwamna Ganduje da mataimakinsa kuma ɗan takara Gwamnan Kano a 2023 sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkar kasuwanci a…
Read More
Kar ku zama ‘yan bangar siyasa – Gargaɗin Ɗanƙwairo ga matasa

Kar ku zama ‘yan bangar siyasa – Gargaɗin Ɗanƙwairo ga matasa

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Ɗa ga shahararren mawaƙin Hausan nan, Marigayi Alhaji Musa Ɗanƙwairo, wato Alhaji Ibrahim Musa Ɗankwairo, ya gargaɗi matasa, da kar su kuskura su bada kai ga wasu 'yan siyasa waɗanda buqatarsu kawai, su ci zaɓe, su yi watsi da su matasan, bayan sun yi amfani da gumin su. Ibrahim Ɗanƙwairo, wanda shi ne Sarkin Samarin garin Tafa dake Ƙaramar Hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, ya yi wannan gargaɗin ne yayin hira da 'yan jarida a garin Tafa a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin wani taron tallafa wa matasa da ya yi. A cewar shi,…
Read More
Makarantar ST.Lous ta yi walimar ɗalibai 29 da suka yi saukar karatun Alƙur’ani Maigirma

Makarantar ST.Lous ta yi walimar ɗalibai 29 da suka yi saukar karatun Alƙur’ani Maigirma

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Makarantar ST Lous mai tsohon tarihi da ke Unguwar Bamfai a birnin Kano, ta yi bikin walimar taya ɗalibanta 29 murna da suka samu falalar rabauta da sauke karatun Alƙur'ani maigirma, a walimar da hukumar makarantar ta shirya musu wadda aka yi a harabar makarantar a ranar Larabar da ta gabata, kamar yadda Malama Halima Baba Yaro, mataimakiyar shugabar makarantar kuma wacce ta jagoranci bikin walimar ɗaliban 29, ta bayyana a lokacin walimar. Har ila yau, Malama Halima Baba Yaro, ta ce wannan ranar ba ƙaramar rana ba ce ga hukumar makarantar da malamai, da…
Read More
Kamfanonin siminti na BUA da Ɗangoten suna kashe kaso 41.33 na cinikinsu a kan wutar lantarki da makamashi

Kamfanonin siminti na BUA da Ɗangoten suna kashe kaso 41.33 na cinikinsu a kan wutar lantarki da makamashi

Daga AMINA YUSUF ALI Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanonin siminti na Ɗangote da BUA suna kashe kaso 41.33 na cinikinsu wajen samar da wutar lantarki da sayen makamashi. A yayin da shekarar nan ta 2022 ta raba, waɗannan manyan kamfanonin Sumuntin da suka fi kowanne a Nijeriya Ɗangote da BUA sun kashe kimanin Naira biliyan 173.537 a kan samar da wutar lantarki da makamashi. Wato kaso 41.33 daga cikin jimillar kuɗaɗen cinikin da suka yi tun daga farkon shekarar zuwa wannan lokaci, Naira biliyan N419.965. Wato abinda kamfanonin biyu suka kashe ya qaru da kaso 38.34 a kan Naira biliyan…
Read More
An fara gasar Firimiya ta Ukraine yayin da ake ci gaba da yaƙi

An fara gasar Firimiya ta Ukraine yayin da ake ci gaba da yaƙi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumomin ƙasar sun haramta taruwar mutane a wuri guda, gudun kada Rasha ta harbo maikaman roka, hakan ya sa aka hana 'yan kallo shiga filayen wasanni. An buɗe gasar ƙwallon ƙafa ta Premier a Ukraine yayin da ƙasar ke ci gaba da gwabza yaƙi da Rasha. A ranar Talata aka buɗe gasar ta 2022, amma an haramtwa masu kallo zuwa filayen wasanni. Wasan farko an buga ne a filin wasa na Kyiv mai ɗaukar mutum dubu 65 tsakanin Shaktar Donetsk da Metalist 1925, inda aka ta shi canjaras. Ƙasar ta Ukraine na ƙarƙashin matakin soji na…
Read More
Ina firgita idan na kalli teburin Firimiya – Klopp

Ina firgita idan na kalli teburin Firimiya – Klopp

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya ce, teburin gasar Firimiyar Ingila babu daɗin kallo a yanzu, bayan da ƙungiyar tasa ta rikito zuwa matsayi na 16 sakamakon shan kaye a hannun Manchester United da ƙwallaye 2 da 1 ranar Litinin ɗin da ta gabata. Har zuwa yanzu Liverpool ba ta samu nasara a ko da wasa guda daga cikin 3 da ta doka ba, a wasannin sabuwar kakar gasar ta Firimiya da aka faro, yayin da yanzu haka ta ke da tazarar mai 7 tsakaninta da Arsenal wadda ke jagorancin teburi.…
Read More
Ranar HAUSA: Lokaci ne na tunawa da harshe da adabi da al’adun Hausawa – Farfesa Ibrahim Malumfashi

Ranar HAUSA: Lokaci ne na tunawa da harshe da adabi da al’adun Hausawa – Farfesa Ibrahim Malumfashi

"Bikin Ranar Hausa zai sa wa 'yan gida da baƙi shauƙi da sha'awar harshen" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Farfesa Ibrahim Malumfashi fitaccen malami ne kuma masani a harshen Hausa da harkokin adabi, Marubuci, manazarci, ɗan jarida, masanin tarihi da rubuce rubucen mata a ɓangaren adabi, wasan kwaikwayo da tarihin gudunmawar marubuta a harshen Hausa. Duk wani wanda ya kwana ya tashi a fannin nazarin harshen Hausa da rubutun adabi a cikin Nijeriya da ƙasashen waje, babu shakka ya sallama wa Farfesa Ibrahim Malumfashi, saboda ɗimbin sanin da Allah ya bashi da a kan rayuwar Hausawa da harshen Hausa da kuma…
Read More