Editor

9513 Posts
Buhari bai tattauna batun karɓa-karɓa da ‘yan takara ba, cewar hadimin Sanata Adamu

Buhari bai tattauna batun karɓa-karɓa da ‘yan takara ba, cewar hadimin Sanata Adamu

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, bai tattauna batun tsarin karɓa-karɓa ba a tsakaninsa da 'yan takarar Shugaban Ƙasa na APC. Hadimin Shugaban APC na Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Muhammad Nata'ala Keffi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta ce, labarin da ke karakaina a kafafen sada zumunta na zamani dangane da tsarin mulkin karɓa-karɓa da aka ce Buhari ya zance a kai ba gaskiya ba ne, aikin masharranta ne kawai. Nata'ala ya ce, Shugaba Buhari cewa ya yi, "Ba tare da take cancantar kowa ba, ina kira gare ku…
Read More
‘Yan bindiga sun saki mai yi wa ƙasa hidima bayan biya Naira miliyan biyu

‘Yan bindiga sun saki mai yi wa ƙasa hidima bayan biya Naira miliyan biyu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindiga sun saki 'yar yi wa ƙasa hidima (NYSC) da suka sace a Kaduna, bayan sun cika sharuɗan da suka gindaya masu na biyan kuɗin fansa Naira miliyan biyu da katin waya na Naira dubu 100 da kuma babur. Faith Onoriode, wacce ta kammala Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Otefe, Oghara da ke Jihar Delta, a Tsangayar Nazarin Halittu da Ilimin Kananan Halittu (Biology/Microbiology), an sake ta ne bayan an cimma matsaya tsakanin iyayenta da waɗanda suka sace ta. SaharaReporters ta ba da rahoton cewa, Onoriode, an sace ta ne a kan hanyar…
Read More
Samo ’yanci ga fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da aka sace

Samo ’yanci ga fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da aka sace

Barazanar baya-bayan nan da ’yan ta'adda ke yi na kashe fasinjojin jirgin ƙasa da aka sace idan gwamnati ta gaza biyan buƙatunsu cikin kwanaki bakwai, dole ne a mayar da hankali a cikin gaggawa. ’Yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjojin da suke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022, sun bai wa Gwamnatin Tarayya damar tattaunawa da su tare da neman ganin an sako waɗanda aka sace. Sun yi gargaɗin cewa rashin yin hakan zai sa a kashe Waɗanda aka sacen. ’Yan ta’addan Waɗanda suka gabatar da buƙatar ta hannun Malam Tukur Mamu, kakakin…
Read More
EFCC za ta ƙwace Jami’ar Nok da ke Kaduna

EFCC za ta ƙwace Jami’ar Nok da ke Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata Kotu a Nijeriya ta umarci hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta ƙwace Jami'ar Nok mai zaman kanta mallaki wani tsohon babban jami'in gwamnati da ke fuskantar tuhuma kan rashawa. EFCC ta ce, Anthony Hassan, wanda tsohon darakta ne na harkokin kuɗaɗe a ma'aikatar lafiya, ya gina jami'ar ne da kuɗin rashawa. Sai dai wani abu da ba a fayyace ba, shi ne ko matakin zai shafi karatun ɗalibai a makarantar da ke Arewacin Kaduna. Kuma babu wasu ƙarin bayyanai kan ko Mista Hassan zai ɗaukaka ƙara. Sannan baya ga ƙwace jami'ar, akwai…
Read More
Rikicin APC: Sanata Abdullahi Adamu ya bada haƙuri

Rikicin APC: Sanata Abdullahi Adamu ya bada haƙuri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bada haƙuri a kan rikicin da ya kunno kai a kwanan nan. Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa kwanaki uku da su ka gabata ne dai wasu masu riqe da muƙamai a APC, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Malam Salihu Lukman da takwaransa na Kudu maso Yamma, Isaac Kekemeke su ka zargi Adamu da ajiye su a gefe a al’amuran jam’iyyar ba tare da yi da su ba. Sun zargi Adamu da yin abubuwa da dama waɗanda ba su dace ba…
Read More
Taron kasuwanci a Spaniya: Buhari na yi wa Nijeriya zawarcin zuba jari

Taron kasuwanci a Spaniya: Buhari na yi wa Nijeriya zawarcin zuba jari

• Ya ce Nijeriya ce mafi girman tattalin arziki a Afirka • Ya bada shawarar yadda ƙasashen Afirka da Turai za su fuskanci ƙalubalen yaƙin Rasha da Ukraine • A shirye muke mu tallafa wa 'yan kasuwar Spaniya - Minista Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙalubalanci masu zuba jari na ƙasar Spaniya da su yi amfani da yanayin da Nijeriya ke da shi na rashin biyan haraji da kuma kason ’yan ƙasashen waje marasa iyaka a yankunan cinikayya cikin ‘yanci na ƙasar domin haɓaka kasuwanci tsakanin Nijeriya da Spaniya da kuma bunƙasar tattalin arziki.…
Read More
Sakamakon shaƙar wani sinadari mutane da dama sun fita hayyacinsu a Kano

Sakamakon shaƙar wani sinadari mutane da dama sun fita hayyacinsu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rahotonni daga yankin rukunnin masana’antu na 3 da ke Sharada a jihar Kano na cewa, wasu mazauna unguwar Mundaɗu da dama sun fita daga hayyacinsu sakamakon shaƙar hayaƙin wani sinadari. Da yammacin jiya Juma’a ne dai gidan radiyon Freedom ya fara bada Labarin faruwar lamarin, yana mai cewa iftila’in ya faru ne sakamakon fashewar wata tukunyar sinadari ta masana’antu wadda ke ɗauke da guba. Kazalika Rahotan ya nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga wani wurin masu yin sana’ar gwangwan da ke unguwar inda mai unguwar yankin Malam Magaji Abdullahi ya tabbatar da faruwar…
Read More
Ban aminta da ci gaba da bai wa CBN ajiyar kayan zaɓe ba – INEC

Ban aminta da ci gaba da bai wa CBN ajiyar kayan zaɓe ba – INEC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce, ba za ta ci gaba da kai ajiyar muhimman kayan aikinta a Babban Bankin Nijeriya (CBN) ba. Shugaban INEC na ƙasa, Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan, yana mai cewa daga kan zaɓen gwamna na Jihar Ekiti, INEC ba za ta ƙara kai muhimman kayan aikinta a ajiya a CBN ba. A cewar Yakubu, domin kauce wa samun akasin kayan zaɓe a yayin zaɓuɓɓuka masu zuwa ya sa aka ɗauki wannan mataki. Ana ganin matakin da INEC ɗin ta ɗauka ba ya rasa nasa da bayyana ra'ayin shiga takarar da…
Read More
Masanin ilmin muhalli na Zimbabwe: Hanyar raya ƙasar Sin ba tare da gurɓata muhalli ba ta zama abin koyi Glga duniya

Masanin ilmin muhalli na Zimbabwe: Hanyar raya ƙasar Sin ba tare da gurɓata muhalli ba ta zama abin koyi Glga duniya

Daga CMG HAUSA Masanin ilmin muhalli na ƙasar Zimbabwe, Courage Tavenhave ya yabawa matakan da ƙasar Sin take ɗauka na raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasa da kuma muhalli. Courage Tavenhave, ya bayyana haka ne yayin da ya zanta da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin CMG a baya-bayan nan, yana mai cewa, matakan ƙasar Sin na neman raya ƙasa ba tare da gurɓata muhalli ba, da kuma kyawawan fasahohinta, sun cancanci ƙasashen duniya su yi koyi da su. Masanin ya bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, ƙasar Sin ta rubanya ƙoƙarinta na kara azama…
Read More