06
Jun
Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al'umma, Blueprint Manhaja. A yau dai za mu kawo wasu daga cikin hanyoyin da za a bi don kare leɓe daga matsalolin da muka ambata a makon da ya gabata. Idan kun shirya, mu tsunduma cikin darasin: Leɓe na ɗaya daga cikin gaɓoɓin jiki da ke bayyane ba tare da kariya ta tufa ko makamancin su ba, don haka, haƙƙi ne da ya rataya akan mammalinsa samar masa kariya ta hanyar kulawa. Akwai hanyoyi da dama da za ki iya kula tare da kuvutar da leɓenki,…
