Editor

9513 Posts
Sin na shan yabo kan gudunmawarta ga kare muhallin duniya

Sin na shan yabo kan gudunmawarta ga kare muhallin duniya

Daga AHMAD FAGAM Muhalli shi ne rayuwa, dukkan halittu na buƙatar kyautatuwar muhalli domin samun rayuwa mai inganci da walwala. A yayin da aka gudanar da bikin ranar muhalli ta ƙasa da ƙasa a ƙarshen wannan mako, masu ruwa da tsaki suna ci gaba da jaddada muhimmancin kare muhalli da yin kiraye-kirayen a kaucewa gurɓata muhallin halittu, domin samun rayuwa mai inganci gami da kaucewa shiga mawuyacin hali a sakamakon gurɓacewar muhallin. A jawabin da ya gabatar a jajiberin bikin muhalli na shekarar 2022, babban sakataren MƊD Antonio Guterres, ya ce ana buƙatar abubuwa masu tarin yawa a wannan duniyar…
Read More
Manoman Jihar Xinjiang suna girbin hatsi

Manoman Jihar Xinjiang suna girbin hatsi

Daga CMG HAUSA A halin da ake ciki yanzu, manoman jihar Xinjiang na ƙasar Sin suna girbin alkaman da aka shuka a yanayin sanyi, kuma an yi hasashen cewa, farashin hatsin da adadin hatsin da za a saya za su karu sannu a hankali. Rahotannin da hukumar adana hatsi da kayayyaki ta jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta fitar sun nuna cewa, sassa daban daban na jihar suna gudanar da ayyukan tattara kudi, da keɓe wuraren adana hatsi, da kashe ƙwayoyin cuta a wuraren, da tantance na’urorin da za a yi amfani da su, da kuma horas da ma’aikatan…
Read More
Zaɓen fidda gwani a APC: Buhari da gwamnonin Arewa sun shiga ganawar sirri a kan tikitin takarar shugaban ƙasa

Zaɓen fidda gwani a APC: Buhari da gwamnonin Arewa sun shiga ganawar sirri a kan tikitin takarar shugaban ƙasa

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi taron ganawar sirri tare da dukkan gwamnonin Arewa na APC a fadarsa ta shugaban ƙasa dake Abuja. Taron ya zo ne sa'o'i kaɗan kafin zaven fidda gwani na ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC wanda ya wakana a ranar Litinin a Eagle Square dake Abuja. Kodayake, ba a samu wani sahihin bayani game da dalilin da ya sa aka yi ganawar ba, amma ana ganin ganawar ba ta rasa nasaba da samun nasara a wajen zaɓen fidda gwanin da za a gudanar ba. Wannan dai shi ne karo…
Read More
Yadda take kulawa da buƙatun ƙasashe masu tasowa ya sa ƙasar Sin ta zama aminiyarsu

Yadda take kulawa da buƙatun ƙasashe masu tasowa ya sa ƙasar Sin ta zama aminiyarsu

Daga BELLO WANG A kwanan baya, ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya ziyarci wasu ƙasashe tsibirai dake yankin tekun Pasific, daga bisani ya bayyana cewa, “ Kar a bar ƙasashe marasa ƙarfi su ci gaba da fama da matsalar koma bayan tattalin arziki.” Maganarsa ta nuna buƙatar ƙasashe masu tasowa ta neman samun ci gaba da wadata, da kuma dalilan da suka sanya ƙasar Sin ke samun goyon baya daga ƙasashen masu tasowa, wato saboda yadda take kulawa da bukatunsu. Wani bayani da wata ƙwararriyar a fannin tattalin arziki ta kasar Kenya Anzetse Were ta rubuta, wanda aka…
Read More
Zaɓen APC: Wakilai 2,340 ne za su tantance ’yan takarar shugaban ƙasa

Zaɓen APC: Wakilai 2,340 ne za su tantance ’yan takarar shugaban ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau litinin ne jam’iyyar APC za ta gudanar da babban taronta a filin taro na Eagle Square da ke Abuja domin fitar da ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa. Ziyarar da wakilin jaridar Blueprint ya kai wurin taron ya nuna cewa, jam’iyyar a shirye ta ke domin gudanar da wannan zaɓe wanda da yawa suka yi imanin cewa babu wani abin da zai iya hana wannan taro kasance ko kuma taɓarɓare taron. Baya ga aikin tabbatar da tsaro, an riga an yi ado a wurin da kuma ware wa wakilan jihohi…
Read More
’Yan bindiga sun kai hari rukunin gidaje mafi girma a Abuja

’Yan bindiga sun kai hari rukunin gidaje mafi girma a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu gungun ’yan ta'adda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a rukunin gidaje na Gwarinpa, wanda shi ne rukunin gidaje mafi girma a babban birnin tarayya, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna. Rahotanni sun bayyana cewa, ’yan bindigar sun kai farmaki ne a safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, 2022 tsakanin ƙarfe 1 na safe zuwa 4 na safe. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, ’yan bindigar da ke da yawan gaske suna ɗauke da wuƙaƙe da adduna, suna shiga gida-gida cikin rukunin gidajen. Ya ci gaba…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 23 a Zamfara

Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 23 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Aƙalla mutane 23 da suka haɗa da mata biyu da ’ya’yan tsohon akawun jihar Zamfara, Alh. Abubakar Bello, wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Furfuri da ke ƙaramar hukumar Bunguɗu a jihar ta Zamfara. Wani mazaunin yankin mai suna Malam Haruna Manaja Furfuri a wata tattaunawa ta wayar tarho da Blueprint Manhaja, ya ce ‘yan bindigar sun yi wa garin ƙawanya ne da misalin ƙarfe 2:30 na safiyar Litinin. A cewarsa, ‘yan bindigar sun je kai tsaye gidan tsohon Akanta-Janar na Zamfara, Alh. Abubakar Bello, inda suka yi garkuwa da matansa…
Read More
Gwamnonin APC na Arewa sun amince Buhari ya zaɓi magajinsa a Kudu

Gwamnonin APC na Arewa sun amince Buhari ya zaɓi magajinsa a Kudu

Daga BASHIR ISAH Gwamnonin APC na jihohin Arewa da wasu masu faɗa a ji a jam'iyyar, sun buƙaci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya zaɓi wanda zai gaje shi daga cikin takwarorinsu na Kudu. Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne yayin zaman da suka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Yayin zaman nasu, gwamnonin sun buƙaci 'yan takarar Shugaban Ƙasa daga yankin Arewa a kan su janye su bai wa 'yan Kudu wuri su fafata. "Muna roƙon dukkan 'yan takara daga jihohin Arewa a kan ku janye ƙudirin takararku don amfanin ƙasa, sannan ku bar 'yan takara daga Kudu kaɗai…
Read More
Za mu ladabtar da Tinubu kan kalaman da ya zazzaga wa Buhari – Adamu

Za mu ladabtar da Tinubu kan kalaman da ya zazzaga wa Buhari – Adamu

Daga BASHIR ISAH Jam'iyyar APC ta ce za ta ladabtar da jagoranta na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, saboda kalaman da ya zazzaga wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kwanan nan. Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a babban ofishin jam'iyyar da ke Abuja a ranarAsabar da ta gabata. Idan za a iya tunawa, a kwanan nan aka ga wani bidiyon Tinubu na yawo yayin ziyarar neman ƙuri'un daliget da ya kai Jihar Ogun, inda a ciki bidiyon aka ji shi yana kalamai kan taimakon…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ƴan Bindiga sun sace mahaifiyar ɗan takarar sanatan Kano ta tsakiya A.A Zaura

Da ɗumi-ɗumi: ƴan Bindiga sun sace mahaifiyar ɗan takarar sanatan Kano ta tsakiya A.A Zaura

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun yi garkuwa da mahaifiyar ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura, wanda aka fi sani da A.A Zaura. Rahotanni sun nuna cewa da sanyin safiyar Litinin din nan ne aka sace mahaifiyar ɗan siyasar, Hajiya Laure Mai Kunu kafin kiran Sallar Asubahi. Shugaban ƙaramar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Solacebase, ya ce jami’an tsaro sun sanar da shi lamarin a hukumance. Ya ce an yi garkuwa da Hajiya Laure ne a gidanta da…
Read More