Editor

9513 Posts
Ƙasar Sin ta bayyana ayyukan da ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 za su yi a sararin samaniya

Ƙasar Sin ta bayyana ayyukan da ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 za su yi a sararin samaniya

Daga CMG HAUSA Hukumar kula da kumbuna ta ƙasar Sin, ta ce ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 da za a tura, za su kammala aikin ginin cibiyar binciken sararin samaniya ta Tiangong, wanda ya kunshi muhimman ɓangarori 3, wadanda suka haɗa da babban ɓangaren cibiyar na Tianhe da kumbunan ɗakunan gwaji na Wentian da Mengtian. A cewar mataimakin daraktan hukumar, Lin Xiqiang, ‘yan sama jannatin za su yi aikin gina cibiyar ta sararin samaniya zuwa ɗakin gwaje- waje na ƙasar a sararin samaniya. ƙasar Sin ta shirya harba kumbon Shenzhou-14 ne a gobe Lahadi, daga cibiyar harba tauraron dan Adam…
Read More
Shinkafa mai inganci ta ƙasar Sin ta bada gudunmuwa wajen ƙara yawan shinkafa a Nijeriya

Shinkafa mai inganci ta ƙasar Sin ta bada gudunmuwa wajen ƙara yawan shinkafa a Nijeriya

Daga CMG HAUSA A yayin wani taron da aka gudanar a ranar 2 ga wata dangane da taimakawa ƙasashen yammacin Afirka kafa wani tsarin noman shinkafa, Wang Xuemin, mai taimakawa babban darektan kamfanin Green Agriculture West Africa wato GAWAL ƙarƙashin shugabancin kamfanin CGCOC kuma masanin ilmin noman shinkafa, ya yi ƙarin bayani kan yawan shinkafar da ake girbewa bisa mabambantan fasahohin noma da kuma amfani da mabambantan irin shinkafa a wasu gonaki. A shekarun baya, gwamnatin Najeriya ta bada muhimmanci kan noman shinkafa a ƙasar, ta kara zuba jari da taimakawa masana’antun shinkafa ta fuskar manufofi, sa’an nan ta mai…
Read More
Ina alfahari da Super Eagles duk da rashin nasara a hannun Mexico – Peseiro

Ina alfahari da Super Eagles duk da rashin nasara a hannun Mexico – Peseiro

Jose Peseiro, sabon kocin Super Eagles, ya bayyana cewa, yana alfahari da ƙungiyar duk da rashin nasarar da suka yi a hannun Mexico da ci 2-1 a wasan sada zumunci da sanyin safiyar Lahadi. Har ila yau 'yan wasan na Portugal sun yaba wa ’yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NPFL), saboda rawar da suka taka a wasan. “Ko da ya ke ba mu yi nasara ba a daren jiya, ina matuƙar alfahari da yaran,” Peseiro ya rubuta a shafin sa na twitter. “Ƙungiyar ta nuna hali da juriya. Magana ta musamman ga ’yan wasan NPFL huɗu da suka…
Read More
Kotu ta umarci kamfanin MTN su biya diyyar miliyan 200 ga yarinya ‘yar shekara 4

Kotu ta umarci kamfanin MTN su biya diyyar miliyan 200 ga yarinya ‘yar shekara 4

Daga AMINA YUSUF ALI Wata kotun dake zamanta a garin Damaturu ta jihar Yobe a ranar Litinin ɗin da ta gabata ta umarci hukumar kamfanin sadarwa na MTN (NELMACO) da su biya Hamsatu Abdullahi Naira miliyan 200 saboda sakaci. Ita dai wanna yarinya mai suna Hamsatu ana zargin cewa, ta rasa hannayenta guda biyu da kuma ƙafa guda a sakamakon shokin ɗin wutar lantarki daga wayoyin kamfanin MTN. Alƙalin kotun Mai Shari'a M. Lawu Lawan ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin, wato (MTN) sun riga sun amsa laifinsu a baki da kuma a rubuce kasancewar akwai shaidu masu ƙarfi da…
Read More
Mata zai bar Man United a ƙarshen watan Yuli

Mata zai bar Man United a ƙarshen watan Yuli

Juan Mata zai bar Manchester United a matakin wanda bai da ƙungiyar, idan yarjejeniyarsa ta ƙare a ƙarshen kakar bana. Mai shekara 34, wanda ya taka rawar da ta kai Sifaniya ta lashe kofin duniya a 2010, ya koma United daga Chelsea a 2014 kan fam miliyan 31.1. Mata wanda ya ci ƙwallo 51 a wasa 285 da ya yi wa United, ya buga Premier League ta bakwai a kakar nan da aka kammala ranar 22 ga watan watan Mayu. Ranar Laraba, Manchester United ta sanar da cewar Paul Pogba, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bane, zai bar Old Trafford.…
Read More
Sigari na kashe ‘yan Nijeriya 29,000 a kowacce shekara – Bincike

Sigari na kashe ‘yan Nijeriya 29,000 a kowacce shekara – Bincike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani mai bincike kan ci gaban tattalin arziki a Afirka ya ce taba sigari na sanadin rayukan 'yan Nijeriya 29,000 a kowacce shekara. Austin Iraoya da ke aiki da cibiyar tattalin arziki ta Afirka ya ce 'yan Nijeriya na kashe Naira biliyan 526 wajen shan sigari da neman maganin cututuka da taba ke haifarwa. Jaridar Daily Trust a Nijeriya ta rawaito, Mista Austin na cewa wannan al'amari na yin mumunan illa ga tattalin arzikin ƙasa.Kuma a cewarsa gwamnati na samun harajin kashi 10 cikin 100 ne kacal, na waɗannan kuɗaɗe da ake varnatarwa wajen…
Read More
Ba don ni ba da Buhari bai ci zaɓen 2015 ba – Tinubu

Ba don ni ba da Buhari bai ci zaɓen 2015 ba – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jagoran Jam'iyyar APC kuma ɗaya daga cikin na kan gaba da ke neman takarar shugabancin Nijeriya a ƙarƙashin jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya ce, shi ne ya zama ja gaba a yaqin neman zaɓen Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi nasara a 2015. Tinubu ya ce shi ne ya bayar da sunan Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari. Jaridar Dailay Trust ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a masaukin shugaban ƙasa a birnin Abeokuta na jihar Ogun, yayin da yake tattaunawa da daliget ɗin APC gabanin zaɓen fitar da gwani…
Read More
Kamata ya yi ‘yan siyasar Amurka masu cewa suna martaba al’ummar Sinawa su dakatar da kitsa ƙarairayi

Kamata ya yi ‘yan siyasar Amurka masu cewa suna martaba al’ummar Sinawa su dakatar da kitsa ƙarairayi

Daga CMG HAUSA Cikin jawabin sa na baya bayan nan game da manufofin ƙasar Sin, sakataren wajen Amurka Antony Blinken, ya ce Amurka na da manyan bambance bambance tsakanin ta da JKS, da ma gwamnatin ƙasar Sin, amma waɗannan bambance bambance na da nasaba ne da gwamnatocin ƙasashen, da tsarin gudanarwa, ba wai da al’ummun sassan biyu ba. Sai dai waɗannan kalamai na Mr. Blinken, ba za su samu karɓuwa a kunnuwan Sinawa, da al’ummun ƙasa da ƙasa, da ma shi kan sa Blinken ba. Kasancewar su ƙarya ce tsagwaron ta! Idan da gaske ne, kamata ya yi ‘yan siyasar…
Read More
Kalaman Xi Jinping game da kishin ƙasa

Kalaman Xi Jinping game da kishin ƙasa

Daga CMG HAUSA A bana yau Juma’a ce ranar da Sinawa ke murnar bikin Duanwu. An fara gudanar da wannan biki na musamman ne, domin tunawa da wani shahararren marubucin rubutattun waƙoƙi mai kishin ƙasa mai suna Qu Yuan, wanda ya rayu a zamanin daular Zhanguo wato the Warring States Period a Turance wato tsakanin shekarar 475 zuwa 221 kafin haihuwar Annabi Isa A.S. Qu, ya rubuta waƙoƙi da dama game da rayuwar al’umma da kishin ƙasa, kuma shugaban ƙasar Sin, babban sakataren kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin ƙasar Xi Jinping, ya kan tsamo wasu kalmomin dake…
Read More
‘Yar shekara huɗu ta mutu a Kano bayan faɗa wa Kano

‘Yar shekara huɗu ta mutu a Kano bayan faɗa wa Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano  ta tabbatar da rasuwar wata yarinya 'yar shekara 4, mai suna Amina Abdullahi Garba bayan ta faɗa cikin rijiya da ke Ƙofar Waika, daura da Masallacin Karmawi a Ƙaramar Hukumar Ungoggo. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi ya bayyana cewa, hukumar kashe gobara ta Ƙofar Nasarawa ce ta samu kiran waya na gaggawa da misalin ƙarfe 2:05 na rana, daga wani Alkasim Ibrahim. Ya ci gaba da cewa da isar su, tawagar ceto ta gano cewa wata yarinya 'yar shekara huɗu ta faɗa cikin rijiya.…
Read More