Editor

9513 Posts
Tantancewa: 10 daga ‘yan takarar Shugaban Ƙasa na APC ba su kai bantensu ba

Tantancewa: 10 daga ‘yan takarar Shugaban Ƙasa na APC ba su kai bantensu ba

Daga BASHIR ISAH Kwamitin tantance 'yan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar APC, ya ce goma daga cikin 'yan takarar ba su cancanci shiga zaɓen fidda gwani na jam'iyyar da zai gudana a makon gobe ba. Shugaban kwamitin tantancewar, John Oyegun, shi ne ya bayyana haka a ranar Juma'a. A cewar Oyegun, 'yan takara 13 daga cikin 23 ne suka tsallake tantancewar da aka gudanar. Shirin tantancewar ya gudana ne tsakanin Litinin a Talatar da suka gabata a Abuja. Ana sa ran waɗanda suka tsallake tantancewar su shiga zaɓen fidda gwanin APC da jam'iyyar ta shirya gudanarwa daga 6 zuwa 8…
Read More
Yadda ƙasar Sin ta yi nasarar sauƙaƙa fatara da raya karkara a gomman shekaru

Yadda ƙasar Sin ta yi nasarar sauƙaƙa fatara da raya karkara a gomman shekaru

Daga: LAWAL SALE Sanin kowa ne cewa Sin ƙasa ce wacce ta ɗauki yaƙi da fatara da muhimmanci, musanmman ma a yankunan karkara inda masu fama da ƙangin talauci suka fi yawa. Sin dai ƙasa ce mai tasowa da ta fi kowace girma a duniya kuma tana gaba-gaba a kan yaƙi da fatara ko kuma talauci a yayin da ta ɗauki matakai waɗanda suka sa ta kawar da ƙangin talauci daga dukkan fannoni zuwa shekarar 2020. Wannan cimma nasara dai yana da inganci mai yawa a rayuwar jama’a, da tattalin arziki, da yanayin tsarin gudanar da mulki. Matakan dai da…
Read More
Osinbajo ka saka baki a sako mu – Cewar ɗalibarsa da ke tsare hannun ‘yan bindiga

Osinbajo ka saka baki a sako mu – Cewar ɗalibarsa da ke tsare hannun ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da ɗimbin fasinjojin da suka yi fashin jirgin ƙasa a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, sun sake sakin wani bidiyo, mai ɗauke da wasu da ke hannun su, su na bayanin Gwamnatin Tarayya ta kai masu agaji, ta cece su daga hannun ‘yan bindigar. Bidiyon wanda su ka saki a ranar Litinin, shi ne na biyar a jerin bidiyon da suka saki, tun bayan kama matafiyan a ranar Litinin, 28 ga Maris. A ranar Litinin ce waɗanda ake tsare da su ɗin suka cika kwanaki 62 a hannun maharan.…
Read More
’Yan sanda sun daƙile yunƙurin IPOB na ƙona gidan rediyo a Anambara

’Yan sanda sun daƙile yunƙurin IPOB na ƙona gidan rediyo a Anambara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'Yan Sandan Jihar Anambara ta tabbatar da wani hari da aka kai wa gidan rediyon jihar Anambra, ABS, da sanyin safiyar Litinin. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambara, DSP Toochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ba a samu asarar rai ba a lamarin. Ikenga ya ce waɗanda ake zargin ba su samu nasarar kaiwa ga ɗakin watsa shirye-shirye, amma kuma sun yi nasarar ƙona wasu motoci guda biyu na tashar. Ya ce, biyo bayan wani kiraye-kirayen da aka yi 30…
Read More
Mun magance kashi 70 na ƙarancin ruwan Ƙunchi da Tsanyawa – Hon. Gwarmai

Mun magance kashi 70 na ƙarancin ruwan Ƙunchi da Tsanyawa – Hon. Gwarmai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano, mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙunchi da Tsanyawa kuma shugaban kwamitin ayyuka da raya birane a majalisa, Hon.Garba Ya'u Gwarmai  ya ce yana mutuƙar alfahari da irin ƙudurorin da yake gabatarwa a matsayinsa na ɗan majalisa don kyautata cigaban al'ummarsa da Jihar Kano bakiɗaya. Ɗan majalisar ya bayyana haka ne yayin da yake hira da manema labarai, inda ya ce cikin kudurorin da ya gabatar  sun haɗa da na neman a bai wa ma'aikata kuɗin rago a zamanin gwamnatin Injiniya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, duk da hakan bai tabbata ba. Ya…
Read More
Bayan kwana 38 a hannun ‘yan bindiga, Ameerah ‘yar Dr Ramatu Abarshi ta shaƙi iskar ‘yanci

Bayan kwana 38 a hannun ‘yan bindiga, Ameerah ‘yar Dr Ramatu Abarshi ta shaƙi iskar ‘yanci

Daga WAKILINMU Ameerah, ɗiyar Dakta Ramatu Abarshi, malama a Kwalejin Fasaha ta Kaduna ta kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da ita. Jaridar Daily Trust ta ruawaito cewa, an yi garkuwa da Dakta Abarshi da ‘yarta da kuma direbansu Ibrahim ne a ranar 24 ga Afrilu, 2022, a Babbar Hanyar Kachia zuwa Kaduna sa’ilin da suke dawowa daga aikin tallafa wa masara galihu. Masu garkuwar sun sako Abarshi ne kimanin makonni uku da suka gabata, direban nasu a makon da ya gabata, sai ‘yar wadda aka sako ta kwanaki biyar bayan sako direban. Majiya ta kusa da…
Read More
Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta ɗauke sansanin NYSC daga Tsafe zuwa Gusau

Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta ɗauke sansanin NYSC daga Tsafe zuwa Gusau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Zamfara ta sauya wa sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) matsuguni daga Ƙaramar Hukumar Tsafe zuwa Gusau, babban birnin jihar, sakamakon matsalar tsaro a sassan jihar. Manhaja ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Muhammad Nasiha, shi ne ya sanar da haka a lokacin da ya karvi baƙuncin Shugaban Hukumar NYSC Birgediya-Janar M K Fadah. Har wa yau, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi magana da hukumar NYSC kan dakatar da ayyukan sansanin a jihar sakamakon ƙalubalen tsaro da ya ta’azzara. Ya bayyana takaicinsa kan koma bayan da aka…
Read More
INEC za ta haɗa gwiwa da ICPC da EFCC don dakatar da sayen ƙuri’u

INEC za ta haɗa gwiwa da ICPC da EFCC don dakatar da sayen ƙuri’u

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce, za ta haɗa gwiwa da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya domin dakatar da sayen ƙuri’u a zaɓen gwamna da za a yi a Ekiti a ranar 18 ga watan Yuni. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Talata a Ado-Ekiti yayin wani taro da sarakunan gargajiya a jihar gabanin zaɓen jihar. Yakubu ya ce, hukumar za ta haɗa gwiwa da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da kuma Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati…
Read More
2023: APC ta samar da kwamiti na musamman gabanin zaɓen fidda gwani

2023: APC ta samar da kwamiti na musamman gabanin zaɓen fidda gwani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC ta sanar da kafa wasu ƙananan kwamitoci 18 da za su gudanar da ayyuka gabanin babban taronta na zaɓen fidda gwani na ’yan takarar shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranakun 6-8 ga watan Yunin 2022. Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa Felix Morka ne ya fitar da jerin sunayen a ranar Laraba. A ranar Litinin ne dai jam'iyyar APC ta fara tantance 'yan takararta na shugaban ƙasa. Ana sa ran jam'iyyar za ta gudanar da babban taronta inda ɗan takarar zai fito daga cikin 'yan takara kusan 23. A halin da…
Read More
Yaƙi da COVID-19 a Shanghai: Kwalliya ta biya kuɗin sabulu

Yaƙi da COVID-19 a Shanghai: Kwalliya ta biya kuɗin sabulu

Daga SAMINU ALHASSAN Tun bayan fara aiwatar da matakan kullen annobar COVID-19 da ta ɓarke a birnin Shanghai na ƙasar Sin, kimanin watanni 2 da suka gabata, a yanzu haka mahukuntan birnin mai yawan al’umma sama da miliyan 25, sun ce matakan da aka ɗauka sun haifar da “da mai ido”, kuma “kwalliya ta biya kuɗin sabulu”. Tuni dai aka sanar da tsara sake buɗe birnin, inda ake sa ran daga Alhamis din nan 2 ga watan Yuni, za a buɗe hanyoyin shiga unguwanni, kana za a dawo da ayyukan sufuri da zirga-zirgar ababen hawa, waɗanda dukkanin su matakai ne…
Read More