02
Jun
Daga CMG HAUSA Wasu kamfanoni biyu na ƙasar Sin, sun baiwa wasu ɗaliban makarantun firamare dake ƙasar Ghana kyauta, albarkacin bikin ranar yara ta duniya da aka shirya a birnin Jamestown, daya daga cikin al'ummomin da ke fama da talauci a Accra, babban birnin ƙasar Ghana. Kamfanin CRCC Harbor da kamfanin CCCC First Harbor Consultants CO., LTD, sun ba da gudummawar gwomman kwallayen kafa, da jakunkuna na makaranta, da fensira masu launi, da abin goge rubuta, da sauran kayan makaranta masu yawa ga makarantar reno ta Chirst the king of kings, wadda ke kusa da tashar kamun kifi ta Jamestown…
