Editor

9513 Posts
Na fuskanci ƙalubalai bayan mutuwar mijina – Hajiya Ramlat Buhari

Na fuskanci ƙalubalai bayan mutuwar mijina – Hajiya Ramlat Buhari

"Burina rayuwata ta amfanar da wasu" Hajiya Ramlat A. Buhari da wasu ke kira da Hajiya Laure, mace ce mai kamar maza, 'yar kasuwa, 'yar jarida, marubuciya, malama, mai kishin ilimi da taimakon raunananu. Ta taso a garin Jos cikin gata da kyakkyawar tarbiyya, daga bisani rayuwa ta yi mata juyin masa, sakamakon rasuwar mijinta, wanda rasuwar sa ya sauya mata rayuwa bakiɗaya. Ta yi fama da raino da tarbiyyar yara marayu da aka bar ta da su, don su zama mutane nagari, sannan ita kanta ta koma makaranta, don kishin da take da shi na samun ilimi, inda ta…
Read More
Badaƙalar biliyan N200: Akanta Janar ya bayyana sunayen wasu a matsayin waɗanda ake zargi

Badaƙalar biliyan N200: Akanta Janar ya bayyana sunayen wasu a matsayin waɗanda ake zargi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Badaƙalar da ta shafi Akanta Janar na Tarayyar Nijeriya da aka dakatar, Ahmed Idris na iya cinye wasu jami’an gwamnati yayin da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta tsananta bincike. Rahotanni sun bayyana cewa, bisa sakamakon binciken da hukumar EFCC ta gudanar, jimillar kuɗaɗen da aka samu a cikin jerin badaƙalar hada-hadar kuɗaɗe da aka dakatar da Akanta Janar akansu ta kai Naira Biliyan 200 (N200,000,000,000). Idan za a iya tunawa cewa, jami’an EFCC sun kama Idris ne a ranar 16 ga Mayu, 2022 kan wasu zamba da aka fara tunanin Naira…
Read More
Tir da kisan gillar ’yan Arewa a Kudu

Tir da kisan gillar ’yan Arewa a Kudu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ina wannan rubutu ne zuciyata cike da ƙunci da ɓacin rai game da kisan gillar da aka yi wa wata mata ’yar Arewa mai suna Harira Jibrin da ke ɗauke da tsohon ciki, tare da yaran ta huɗu, Fatima, Khadija, Hadiza da Zaituna, a yayin da suke kan hanyar su ta komawa gida daga wata ziyara da ta kai wa wata ’yar uwar mijinta a yankin Isulo da ke ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu a Jihar Anambra, a ranar Litinin da ta gabata. A wani gajeren bidiyo da ke yawo a zaurukan sada zumunta na yanar…
Read More
Okorocha ya bayyana wajen tantance ‘yan takara jim kaɗan bayan samun beli

Okorocha ya bayyana wajen tantance ‘yan takara jim kaɗan bayan samun beli

Daga BASHIR ISAH Tsohon Gwmanan Jihar Imo kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar APC, Rochas Okorocha, ya bayyana gaban kwamitin tantance 'yan takarar Shugaban Ƙasa ranar Talata da daddare a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja domin a tantace shi. A makon da ya gabata ne Okorocha ya faɗa a komar EFCC bisa tuhumar almundahana na biliyan N2.9. Tsohon gwamnan na daga cikin 'yan takarar da ke zawarcin shugabancin Nijeriya ƙarƙashin Jam'iyyar APC a 2023.
Read More
2023: Ku haɗa kanku don samar da nagartaccen shugabanci, kiran Buhari ga gwamnonin APC

2023: Ku haɗa kanku don samar da nagartaccen shugabanci, kiran Buhari ga gwamnonin APC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga gwamnonin APC da su zamo madu kiyaye ƙa'idojin jam'iyya yayin zaɓen fidda gwani na APC mai zuwa. Buhari ya yi wannan kira ne yayin wata ganawa da ya yi da gwamnonin na APC su 22 haɗe da Shugaban APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ranar Talata a fadar Villa da ke Abuja. Cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya ce Shugaba Buharin ya ce, "Shirye-shiryen zaɓen 2023 sun kankama, kuma a sanina galibin nasarar jam'iyyun siyasa a sassan duniya ya danganta ne…
Read More
Cutar Ƙyandar Biri ta kama mutum 21 a Nijeriya — NCDC

Cutar Ƙyandar Biri ta kama mutum 21 a Nijeriya — NCDC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC), ta ce, mutum 21 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Ƙyandar Biri a faɗin qasar ta kuma yi ajalin mutum ɗaya daga farkon 2022 zuwa yau. Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, NCDC ta ce, “zuwa yanzu, daga cikin mutum 21 da suka kamu da cutar babu wata alamar cewa sun yaɗa ƙwayoyin cutar, kuma babu wani sauyi da ya afku dangane da bayanan cutar da kuma yadda ake kula da ita. Hukumar ta ƙara da cewa, Ƙyandar Biri cuta ce da ake samun…
Read More
Rage raɗaɗin fatara ta hanyar ciyar da ‘yan makaranta

Rage raɗaɗin fatara ta hanyar ciyar da ‘yan makaranta

Daga IBRAHIM SHEME Sanin kowa ne cewa Nijeriya na cikin tarnaƙin fatara da yunwa. Ba kowa ba ne ya ke iya ciyar da kan sa da iyalin sa, ballantana ya gudanar da wasu harkokin na rayuwa. Akwai ma masu cewa Nijeriya ta fi kowace ƙasa fama da fatara a duniya. Duk da yake hakan ba gaskiya ba ne, amma yanayin da ake ciki ya sanya tilas shugabanni su fito da hanyoyin rage halin ƙunci da ake fama da shi. A daidai lokacin da gwamnatin Buhari ta zo, duniya gaba ɗaya ta auka cikin halin karayar tattalin arziki saboda faɗuwar farashin…
Read More
Shin ko kun san mece ce 13×13 da manufarta?

Shin ko kun san mece ce 13×13 da manufarta?

Daga HASHIM ABDALLAH Daga masu son shigarta, har zuwa kan masu rarraunar fahimta gare ta da masu neman fahimtar mece ce ko kuma dalilan adafin sunanta da sha'uku-sha'uku, duk ku buɗe kunnuwanku. Ma'anar 13x13 Thirteen-Thirteen ko in da Hausa ne, wato sha'uku-sha'uku. Ƙungiya ce samarwar mutane 13. Haƙiƙa kuma alkhairi ne, kamar yadda taken tafiyar yake, da aka yi imani zai 'yanta 'yan Najeriya domin samar da rayuwa mai inganci ko inganta rayuwar ta fuskoki daban-daban gaba da siyasa ko waƙar siyasa ko kamfe. Ba ta da wani maqiyi sai maƙiyin al'umma. A dalilin hadafi na 'yanta ƙasa, lallai 13x13…
Read More
‘Yancin mallakar makamai barazara ce ga yara a Amurka

‘Yancin mallakar makamai barazara ce ga yara a Amurka

Daga AMINA XU Abokai, yau na zana wani Cartoon dangane da harbe-harben bindiga da suka yi ta faruwa a ƙasar Amurka, kuma da hakan ina nuna alhini ga yaran da suka rasu sakamakon harbe harben bindiga da suku rutsa da su a Amurka, musamman ma yara 19 da suka rasa rayukansu kwanan baya a jihar Texas na ƙasar. ‘Yancin mallakar makamai na samar da sauki ga masu aikata laifuka a ƙasar, matsalar da ta addabi yaran ƙasar sosai. Bai kamata irin wannan matsala ta bullo a cikin wata ƙasa dake iƙirarin kare hakkin Bil Adama da martaba dimokuraɗiyya ba. Dole…
Read More
Masanan ƙasar Sin na cigaba da gabatar da abubuwa na ban mamaki ga duniya

Masanan ƙasar Sin na cigaba da gabatar da abubuwa na ban mamaki ga duniya

Daga FAEZA MUSTAPHA A karon farko, ƙasar Sin ta ƙaddamar da wata sabuwar tashar samar da lantarki daga hasken rana da ƙarfin igiyar ruwa, wadda ke da ƙarfin samar da lantarkin da ya zarce kilowatt miliyan 100 cikin shekara guda. Haƙiƙa wannan wani ƙarin nasara ce ga ƙasar Sin a ƙoƙarin da take ci gaba da yi na rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli. Haka kuma nasara ce ga duniya domin ta gabatar musu wani abun misali da koyi a ɓangaren amfani da makamashi mai tsafta domin raya muhalli da biyan buƙatun al’umma. Abun da ya burge ni cikin…
Read More