Editor

9513 Posts
NED ta Amurka tana aikata mugunta da sunan dimokraɗiyyar ƙarya!

NED ta Amurka tana aikata mugunta da sunan dimokraɗiyyar ƙarya!

Daga CMG HAUSA Kwanan nan ne, shugaban gidauniyar tallafin demokraɗiyya (NED), Dimon Wilson, ya jagoranci wata tawaga da ta kai ziyara yankin Taiwan na ƙasar Sin, inda ya fito ƙarara ya bayyana cewa, shi ne ya haifar da "juyin juya hali" a duniya. Wannan muguwar ƙungiya ta yi tattaki zuwa ƙofar ƙasar Sin, don yin aiki da sunan demokuraɗiyya, a wani yunƙuri na haddasa "juyin juya hali". Yadda take furta kalamai da ayyukanta, zai sa ta ci mummunan tura! Kowa ya san wace ce gidauniyar tallafin demokraɗiyya ta ƙasa. Tun bayan kafuwar wannan ƙungiya mai zaman kanta da gwamnatin Amurka…
Read More
Sin za ta maida martani kan wasu jami’an Amurka

Sin za ta maida martani kan wasu jami’an Amurka

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce ƙasar sa za ta aiwatar da matakan hana wasu jami’an ƙasar Amurka Visa, wadanda suka ƙirƙiri karairayi, masu alaƙa da zargin keta haƙƙoƙin bil adama, tare da sa ƙaimin sanya takunkumi ga ƙasar Sin, da illata moriyar ƙasar. Wang ya bayyana hakan ne, a yayin taron manema labarai na jiya Alhamis, bayan da Amurka ta bayyana aniyar sanyawa wasu jami’an ƙasar Sin takunkumin hana Visa, bisa fakewa da zargin keta haƙƙin bil adama. Jami’in ya ƙara da cewa, Sin ba za ta taba amincewa…
Read More
Wang Yi ya jaddada matsayin ƙasar Sin kan batun ƙasar Ukraine

Wang Yi ya jaddada matsayin ƙasar Sin kan batun ƙasar Ukraine

Daga CMG HAUSA Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi ya bayyana a jiya Alhamis a birnin Tunxi dake lardin Anhui na gabashin ƙasar Sin cewa, ƙasar Sin ta taka rawar da ta dace kan batun ƙasar Ukraine. Minista Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karin haske, kan matsayin ƙasar Sin game da batun ƙasar Ukraine, yayin wani taron manema labarai da aka shirya, bayan taron ministocin harkokin wajen ƙasashen dake makwabtaka da ƙasar Afghanistan karo na uku, da kuma taron ministocin harkokin waje na farko a tsakanin ƙasashen dake makwabtaka da…
Read More
Shuka bishiyoyi jigo ne na bunƙasa rayuwar bil Adama

Shuka bishiyoyi jigo ne na bunƙasa rayuwar bil Adama

Daga SAMINU HASSAN A tsakiyar makon nan, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya halarci gangamin dasa bishiyoyi da aka saba yi duk shekara a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar, a wani ɓangare na faɗaɗa dashen itatuwa da kare su, lamarin da ke taka muhimmiyar rawa wajen kare muhalli, da kyautata iska, da dakile kwararar hamada, da cin gajiya daga tsirrai daga dukkanin fannoni. Shekaru 10 ke nan a jere, shugaba Xi ke halartar wannan gangami na shuka bishiyoyi, matakin da masharhanta ke kallo a matsayin manuniya, ga kyakkyawan misalin al’adar Sinawa, ta wanzar da kiyaye tsirrai domin raya muhallin halittu…
Read More
Ba ma’aikacinmu da ya rasa ransa a gobarar kamfanin simintin BUA a Sakkwato – BUA

Ba ma’aikacinmu da ya rasa ransa a gobarar kamfanin simintin BUA a Sakkwato – BUA

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin Samar da Siminti na BUA dake Sakkwato ya bayyana cewa, mutum uku da suka mutu a sanadiyar gobarar da ta tashi a masana’antar Simintin BUA a Sakkwato, ba ma’aikatan kamfanin ba ne, ‘yan ina-da-aiki ne. Wannan bayani yana ƙunshe ne a wata sanarwa da Sada Sulaiman, Daraktan Gudanarwa na BUA Cement ya aiko wa Jaridar PREMIUM TIMES. Ya qara da cewa,  waɗanda tsautsayin ya ritsa da su, suna aiki ne a ƙarƙashin wani mai aikin kula da gyare-gyare na lafiyar inji. A kwanakin baya da ma jaridar ta buga labarin yadda wuta ta tashi a…
Read More
Ci gaban da ke mayar sa hankali kan jama’a na da muhimmanci ga kare haƙƙoƙinsu

Ci gaban da ke mayar sa hankali kan jama’a na da muhimmanci ga kare haƙƙoƙinsu

Daga CMG HAUSA Zaunannen jakadan ƙasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Chen Xu, ya ce ci gaban dake mayar da hankali kan jama’a, shi ne ya kamata ya kasance jigon dabarun kawar da rashin daidaito a tsakanin al’ummun duniya. Chen Xu, wanda ya bayyana haka ga taro na 49 na hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta MDD a Geneva, ya ce annobar COVID-19 ta yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya da ci gaban rayuwar jama’a, musammam ma rayuwar jama’ar ƙasashe masu tasowa. Wannan ya ta’azzara rashin daidaito da haifar da ƙalubaloli masu tsanani ga ci gaban duniya. Don…
Read More
Sin da Indiya sun amince da ƙarfafa tuntuɓar juna domin inganta hulɗarsu

Sin da Indiya sun amince da ƙarfafa tuntuɓar juna domin inganta hulɗarsu

Daga CMG HAUSA Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi dake ziyara a kasar India, tare da takwaransa na ƙasar Subrahmanyam Jaishankar, sun amince su ƙarfafa tuntubar juna a tsakanin ƙasashensu, domin ƙara raya dangantakar dake tsakaninsu. Yayin tattaunawar da ministocin biyu suka yi a New Delhi, babban birnin India, Wang Yi ya ce ƙasashen Sin da India da suka kasance maƙwabtan juna dake da jimilar al’umma biliyan 2.8, na da muhimmin ƙarfi na tabbatar da daidaito tsakanin ƙasashen duniya da dunƙulewar tattalin arzikin duniya da kasancewar mutane masu mabambantan al’adu tare da taka muhimmiyar…
Read More
‘Yan Kano da Gombe sun lashe musabaƙar Ƙur’ani a Abuja

‘Yan Kano da Gombe sun lashe musabaƙar Ƙur’ani a Abuja

Daga BASHIR ISAH An kammala musabaƙar Ƙur'ani na 2022 wanda gidan talabijin ɗin Gaskiya TV ya shirya da aka gudanar a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja. Gasar wadda aka kammala ta a ranar Alhamis da ta gabata, ita ce irin ta ta farko da aka taɓa samu wata hukuma ko cibiya mai zaman kanta ta gudanar a ƙasa. Alhaji Hamza Tanko wanda ɗan kasuwa ne kuma ɗan asalin ƙasar Ghana kuma ya shahara wajen hidimta wa al'umma da dukiyarsa, shi ne ya ɗauki nauyin gudanar da wannan musabaƙar karo na farko a Nijeriya. Inda ya bayyana cewa, soyayyarsa ga…
Read More
Rikicin manoma da makiya ya ɗaiɗaita al’amura a Ƙaramar Hukumar Guri

Rikicin manoma da makiya ya ɗaiɗaita al’amura a Ƙaramar Hukumar Guri

Daga UMAR AKILU MAJERI  a Dutse Rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadin mutuwar mutane tara a yankin Ƙaramar Hukumar Guri da ke Jihar Jigawa a arewacin Nijeriya. Rikicin da ya ɗauki tsawon kwanaki uku ana yi a yankin ya yi sanadin kashe Fulani shida da manoma uku, wasu a gonaki wasu a daji wajen da suke kiwon shanu.  Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar Jigawa ASP Lawan Shisu Adam ya tabbatar da cewar 'yan sanda sun kama mutum goma da ake zargi da hannu dumu-dumu akan rikicin, kuma yanzu haka mutane uku suna asibitin Haɗeja suna karɓar kulawa. Ya kuma…
Read More
Tsadar abinci da fetur duk duniya ne, ba Nijeriya kawai ba – Lai

Tsadar abinci da fetur duk duniya ne, ba Nijeriya kawai ba – Lai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce tashin farashin  kayan abinci, man fetur, dizel da sauran kayayyaki ya zama ruwan dare gama duniya, ba wai kawai wata ƙasa guda ɗaya ba. Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Litinin a Abuja, ya ƙara da cewa taƙaita matsalar ga Nijeriya kaɗai to ya zama yarfe da tsabagen yaɗa kalaman ƙarya. Ya ce ƙididdiga da 'yan adawa da wani vangare na kafafen yaɗa labarai da su ke kwatanta farashin wasu kayan abinci, man fetur, dizel, kafin shekarar 2015 da…
Read More