02
Apr
Daga CMG HAUSA Yau Asabar 2 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta kira taron manema labarai, inda aka yi bayani kan ganawa karo na 23 a tsakanin shugabannin ƙasar Sin da ƙungiyar tarayyar ƙasashen Turai wato EU. Shugaban hukumar kula da harkokin ƙasashen Turai na ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Wang Lutong, ya yi tsokaci yayin taron cewa, an sake shirya ganawar shugabannin Sin da EU ta shekara shekara, bayan shekaru biyu da suka gabata, ana iya cewa, ganawar ta kasance cuɗanya mafi muhimmanci a tsakanin shugabannin sassan biyu wato Sin da EU a bana, ta haifar da kyakkyawan…
