Editor

9513 Posts
Ban taɓa sa ran zan zama shugaban APC na ƙasa ba, cewar Sanata Adamu

Ban taɓa sa ran zan zama shugaban APC na ƙasa ba, cewar Sanata Adamu

Daga BASHIR ISAH Bayan kwanaki huɗu da zaɓensa a matsayin shugaban APC ƙasa Sanata Abdullahi Adamu ya karɓi ragamar aiki inda zai ci gaba da jagorancin harkokin jam'iyyar tasu ta APC a matsayin sabon shugabanta. Adamu, wanda ya isa sakatariyar Jam'iyya da misalin ƙarfe 10:30am na ranar da ya ƙarɓi ragamar aiki, ya ce kimanin wata guda da ya gabata bai taɓa kawowa a ransa cewa zai zama shugaban jam'iyya ba. Turakin Keffi ya zama ɗan takarar jam'iyya ne ba tare da hamayya ba kasancewar shi ne zaɓin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda daga bisani dukkan masu kwaɗayin kujerar suka…
Read More
Matsalar watsi da manyan ayyukan raya ƙasa

Matsalar watsi da manyan ayyukan raya ƙasa

A cikin wasu ’yan shekaru da suka gabata, Shugaban Ma’aikatar tantancewa tare da kula da kwangilolin gwamnati (Bureau of Public Procurement), Injiniya Emeka Eze, ya bayyana wa Majalisar Dattijai cewa, akwai kimanin ayyuka 19,000 a wurare daban-daban na faɗin ƙasar nan da aka yi watsi da su. Waɗannan ayyuka, sun haɗa da na Gwamnatin Tarayya da kuma na jihohi waɗanda ko dai gwamnati da ta fare su ba ta samu damar kammalawa ba, ko kuma gwamnatin da ta gaji ayyukan ta yi watsi da su. Ko shakka babu, akwai yiwuwar adadin nasu ma ya fi haka da ba don Shugaban…
Read More
DCP Abba Kyari ya ƙi aminta da abincin kurkuku ya dogara ga girkin matarsa

DCP Abba Kyari ya ƙi aminta da abincin kurkuku ya dogara ga girkin matarsa

Daga BASHIR ISAH Babban jami'in ɗan sandan nan da ake ci gaba da tsare shi a gidan yari, wato DCP Abba Kyari, ya nuna shi ba zai ci abincin gidan yari ba sai dai abincin da matarsa ko 'yan'uwansa suka girka. A zaman shari'a na ƙarshe da aka yi, kotu ta ƙi yarda da batun bada belin Abba Kyari tare da wasu jami'ai huɗu da ake tuhumarsu tare. Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta maka Abba Kyari tare da wasu mutum huɗu a Babbar Kotun Abuja ne bisa tuhumarsu da hannu cikin harƙallar hodar ibilis…
Read More
Gwamnatin Jigawa ta raba babura ga ƙungiyar mahauta a ƙananan hukumomin jihar

Gwamnatin Jigawa ta raba babura ga ƙungiyar mahauta a ƙananan hukumomin jihar

Daga UMAR AIƘILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jihar Jigawa, ta raba babura 27 ga shugabannin ƙungiyar mahauta na ƙananan hukumomin jihar nan 27. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a mayankar dabbobi ta Dutse, gwamnan jiha, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce hakan na daga cikin ƙudirin gwamnatin jiha na tallafa wa ’yan qungiyar domin su ji daɗin gudanar da ayyukan su. Gwamnan, wanda ya samu wakilcin kwamishinan ƙananan hukumomi, Alhaji Kabiru Hassan Sugungun, ya ce gwamnati ta sahalewa shugabannin ƙananan hukumomi, su duba buƙatun ’yan ƙungiyar da suka haɗa da gyaran mayankar dabbobi na ƙananan hukumomi, tare da gina…
Read More
Ramadan 2022: A nemi jinjirin wata gobe Juma’a – NMSC

Ramadan 2022: A nemi jinjirin wata gobe Juma’a – NMSC

Kwamitin Neman Wata na Ƙasa (NMSC) na Majalisar Ƙoli na Harkokin Musuluncin Ƙasa (NSCIS), ya bada sanarwar al'ummar Musulmin Najeriya a nemi watan Ramadan gobe Juma'a idan Allah Ya kai mu. Kwamitin ya ce gobe Juma'a take 1 ga Afrilun 2022 wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban, 1443, wanda hakan ya zama ranar farko da ya kamata a nemi watan na Ramadan 1443. NMSC ya bada sanarwar ta hanyar wallafawa a shafinsa na facebook. Kwafin sanarwar Idan Allah Ya sa aka ga wata a goben, hakan na nufin al'ummar Nijeriya za su tashi da azumi Asabar mai zuwa…
Read More
2023: Ƙungiyar Arewa ta buƙaci masu neman shugabanci daga Arewa su zakuɗa gefe

2023: Ƙungiyar Arewa ta buƙaci masu neman shugabanci daga Arewa su zakuɗa gefe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Yayin da yaqin neman zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2023 ke ƙara ƙaratowa a faɗin Nijeriya, qungiyoyin ’yan Arewa a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar ‘Arewa Coalition for Rotational Residential’ sun yi kakkausar suka kan masu neman shugabancin ƙasar daga Yankin Arewa, inda suka ce babu adalci a Arewa ta ci gaba da mulkin ƙasar bayan shekaru takwas. Ƙungiyar ta kuma sha alwashin cewa a zahiri za ta tashi tsaye wajen tunkarar duk ’yan takarar shugaban ƙasa daga yankin Arewa, waɗanda suka kuskura su tsaya takara a ƙarƙashin kowace jam’iyya a lokacin babban zaɓe. Wata sanarwa…
Read More
2023: Mambobin PDP a Majalisar Tarayya sun goyi bayan Saraki a matsayin ɗan takararsu

2023: Mambobin PDP a Majalisar Tarayya sun goyi bayan Saraki a matsayin ɗan takararsu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Shugaban Majalisar Dattawa na baya-bayan nan, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya gana da gungun ‘ya’yan jam’iyyar PDP da ke majalisun tarayya da na Dattawa a ranar Talata da ta gabata, inda ya dace da samun tagomashin wani ƙuduri na majalisar wakilai da ta ɗabbaka shi a matsayin ɗan takarar neman shugabancin ƙasa a zaɓen shekara ta 2023. Duka tarurrukan guda biyu an gudanar da su ne a gidajen shugabannin marasa rinjaye biyu na majalisun, Sanata Enyinnaya Abaribe da Hon. Ndudi Elumelu baki ɗaya. A yayin ganawar sa da ‘yan majalisar wakilai, wani mamba daga cikin…
Read More
Amurka mai son ƙaƙaba takunkumi ta kawo babbar illa ga duk faɗin duniya

Amurka mai son ƙaƙaba takunkumi ta kawo babbar illa ga duk faɗin duniya

Daga AMINU XU Abokai na, yau “Duniya a zanen MINA” na mai da hankali kan Amurka mai matuƙar son ƙaƙaba takunkumi ga saura. Rahoton da ma’aikatar kuɗin Amurka ta bayar mai taken “Kimanta takunkumin da Amurka ta sanyawa sauran ƙasashe a shekarar 2021” na nuna cewa, shekaru 20 da suka gabata, tun ɓarkewar rikicin “9.11”, yawan takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa sauran ƙasashe ya karu matuka. An ce, ya zuwa ƙarshen shekarar 2021, yawan takunkumin da Amurka ta ƙaƙƙaba wa sauran ƙasashe ya kai fiye da 9400, inda yawansa ya ninka sau 10 bisa na shekaru 20 da suka…
Read More
Ƙasashen Afirka na ƙara amfana daga alaƙarsu da ƙasar Sin

Ƙasashen Afirka na ƙara amfana daga alaƙarsu da ƙasar Sin

Daga IBRAHIM YAYA Tun bayan da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya yi bayani game da manufar ƙasar Sin ga nahiyar Afrika a Tanzania, wadda ta tsara makomar huldar ƙasashen Sin da Afrika a sabon zamani, wadda yanzu haka ta haifar da ƙawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin ɓangarorin biyu. Ita dai wannan manufa da shugaba Xi Jinping ya gabatar, yayin ziyarar farko da ya kai nahiyar Afrika, a matsayinsa na shugaban ƙasar Sin, a shekarar 2013 ta dogaro ne bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna. Bisa waɗannan tsare-tsare, ƙasar Sin da Afrika, sun…
Read More
Ma’aikatar Wajen Ƙasar Sin ta mayar da martani game da ɓarkewar tashin hankali a wasu sassan Sudan ta Kudu

Ma’aikatar Wajen Ƙasar Sin ta mayar da martani game da ɓarkewar tashin hankali a wasu sassan Sudan ta Kudu

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, Larabar nan ya shirya taron manema labarai na yau da kullum. Kuma wani dan jarida ya yi masa tambaya cewa, a baya-bayan nan an samu tashe-tashen hankula a wasu sassan Sudan ta Kudu. Shin mene ne ra’ayin ƙasar Sin? Wang Wenbin ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2020 zuwa yanzu, an samu gagarumin ci gaba a yunƙurin samar da zaman lafiya a ƙasar Sudan ta Kudu, wanda kuma ya dace da muhimman muradun al'ummar ƙasar. Ƙasar Sin tana kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa,…
Read More