Editor

9513 Posts
Za a gudanar da taron ƙolin Sin da EU ta kafar bidiyo a ranar 1 ga Afrilu

Za a gudanar da taron ƙolin Sin da EU ta kafar bidiyo a ranar 1 ga Afrilu

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya sanar yau Laraba cewa, za a gudanar da taron ƙoli na Sin da EU karo na 23 ta kafar bidiyo a ranar Juma'a. Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da kuma firaministan ƙasar Li Keqiang, za su gana da shugaban majalisar gudanarwar ƙungiyar Tarayyar Turai Charles Michel da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar, uwar gida Ursula von der Leyen yayin taron. Mai fassarawa: Ibrahim
Read More
Ku haɗa kai wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da ta’addanci, Shugaban APC na ƙasa ga ‘yan Nijeriya

Ku haɗa kai wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da ta’addanci, Shugaban APC na ƙasa ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi kira ga 'yan Nijeriya da a haɗe kai wuri guda sannan a yaƙi 'yan ta'adda da ta'addancinsu a faɗin ƙasa. Sanata Adamu ya yi wannan kira ne biyo bayan mummunan harin da 'yan bindiga suka kai wa jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da ta gabata. Cikin sanarwar da ya fitar a jiya Laraba, Shugaban APCn ya ce lokaci ya yi da ya kamata 'yan ƙasa su haɗa kai wajen yaƙar maƙiyan ƙasa. Daga nan, ya nuna alhininsa dangane da rashe-rashen da kuma…
Read More
Al’ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nufe a Nijeriya (II)

Al’ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nufe a Nijeriya (II)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamar yadda jaridar Blueprint Manhaja ta fara kawo wa mai karatu tarihin asalin Ƙabilar Nufawa a makon da ya gabata, a wannan makon za ta cigaba daga inda ta tsaya. Masarautar Bida ta zama ta farko a lokacin Turawan mulkin mallaka, a lokacin ’yancin kan Nijeriya sarakunan ƙasar Bida sun ba da gudunmawa wajen haskaka bikin ’yancin ƙasar nan. Har zuwa yau, masarautar Bida na shirya bikin gargajiya da ake wa laƙabi da ‘Nupe Cultural Day’ don tunawa da gudunmawar da sarakunan masarautar suka bayar da ake wa laƙabi da ‘Etsu’. Sarakunan ƙasar Nufe daga shekarar…
Read More
Shugaba Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 92.1 don gina titin jirgi na biyu a filin jiragen Abuja

Shugaba Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 92.1 don gina titin jirgi na biyu a filin jiragen Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 92.1 domin gina titin jirgi na 2 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa majalisar ta amince da hakan ne sa’o’i 24 bayan ƙaddamar da sabon ginin tashar jirgin sama na Murtala Mohammed International Airport, (MMIA), Legas, da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi. A wajen bikin qaddamar da tashar ne Buhari ya faɗa wa Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa da ta samo wasu kuɗaɗe na musamman domin gina titin jirgi…
Read More
PDP ta zargi Kwankwaso da haɗama

PDP ta zargi Kwankwaso da haɗama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar PDP ta zargi tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da yin ƙarfa-ƙarfa da babakere a zaɓen shugabannin jam'iyyar a Kano. Tsohon Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati, Adamu Yunusa Ɗangwani, tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ɗanburam Abubakar Nuhu da Yusuf Bello Ɗambatta, Kwamishinan Ma'aikatar Ƙasa, su ne suka bi sahun sauran 'yan jam'iyyar PDP a Jihar Kano wajen zargin tsohon mai gidan su, Sanata Rabi'u Kwankwaso da yin ƙarfa-ƙarfa a jam'iyyar. Ɗangwani da Ɗanburam da Ɗambatta jiga-jigan 'yan ɗariƙar Kwankwasiyya ne, kafin a kakar siyasa ta bana su raba gari da jagoran nasu, Rabi'u Musa…
Read More
Zargin karkatar da kuɗaɗe: Kotu ta wanke Sanata Umar Tafida

Zargin karkatar da kuɗaɗe: Kotu ta wanke Sanata Umar Tafida

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alƙalin babbar kotun Jihar Sakkwato, Mai shari’a Mohammed Mohammed a ranar Litinin ya kori shari’ar karkatar da kuɗaɗe da Hukumar Yaqi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu'annati (EFCC) a madadin gwamnatin tarayya ke yi wa Sanata Umar Tafida tare da sallamar Sanata Tafida babu laifi. A hukuncin da kotun ta yanke, Mai shari’a Mohammed ya caccaki EFCC a matsayin mai shiga tsakani da ta ƙi yin aikinta kafin ta gurfanar da mutane a kotu. A cewar mai shari’a Mohammed, EFCC ta gaza bin ƙa’idojin da doka ta shimfiɗa wajen gabatar da tuhumar da ake wa…
Read More
Yadda ɗan shekara 18 ya kashe matar aure da taɓarya a Kano

Yadda ɗan shekara 18 ya kashe matar aure da taɓarya a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 18 bisa zarginsa da kashe matar aure a jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun 'yan sanda reshen Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Kumbotso. Wanda ake zargi da aikata kisan mai suna Abdulsamad Suleiman, ya amsa laifin ga 'yan sandan inda ya ce tun da farko ya shiga gidan matar inda ya same ta a kan gado, bayan ya gaishe ta sai ya ga wayoyi uku sa'annan ya sace…
Read More
Tsadar abincin kifi zai haddasa rashin sa a Ramadan – PFFAN

Tsadar abincin kifi zai haddasa rashin sa a Ramadan – PFFAN

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano  Ma su sana'ar kiwon kifi sun koka kan yadda kamfanonin sarrafa abincin kifi ke tsawwala farashin kayan abincin kifi, inda suka bayyana cewa hakan zai iya kawo matsanancin tsadar kifi a watan Ramadan mai zuwa. Wannan koke ya fito ne daga bakin shugabannin ƙungiyar masu sana`ar kiwon kifi a Nijeriya na ƙasa reshen Jihar Kano, wato Piratic Farmers Fish Association Of Nigeria, PFFAN a lokacin taron ƙungiyar da suka gabatar a Kano cikin makon jiya. Hudu Salisu Khalid, shi ne kakakin ƙungiyar ta PFFAN, ya ce suna fuskantar ƙalubale da matsaloli masu yawa a wannan…
Read More
A daina yaɗa bayanan ƙarya kan sabbin shugabannin APC

A daina yaɗa bayanan ƙarya kan sabbin shugabannin APC

Daga SADIQ ABDULLATIF A duk lokacin da aka saki wani bayani, galibi ba mu cika damuwa da bincikar sahihancin bayanin ba kafin yaɗawa. Wannan kuwa, na ɗaya daga ciki ƙalubalan soshiyal midiya da kafafen yaɗa labarai na zamani. Don haka, na shigo ne domin in taimaka wa 'yan Nijeriya wajen fahimtar abubuwan da ke tattare da babban taron jam'iyyar APC da ya gudana kwanan nan. Kuma ina yin hakan ne da kyakkyawar niyya don faɗakar da mu da kuma ɗora komai a mizani a matsayina na tsohon Editan Labarun Siyasa. Da farko dai ba gaskiya ba ne cewa an miƙa…
Read More