Editor

9513 Posts
Mu ’yan Kannywood muna da tsarki kamar ruwan zamzam, inji Halima Atete

Mu ’yan Kannywood muna da tsarki kamar ruwan zamzam, inji Halima Atete

“Dalilin da ya sa ban taɓa tsoma kaina a rigimar Kannywood ba” Daga AISHA ASAS Sananniyar jaruma a masana'antar Kannywood kuma mai shirya fim, Halima Atete, ta shigo masana’antar tun shekaru 10 baya, kuma za mu iya cewa, ta shigo da ƙafar dama, duba da irin nasarori da ta samu, ciki kuwa har da sarautar masana’artar wato ‘Sarauniyar Kannywood” da ake yi mata laƙabi da ita. A zantawarta da Jaridar Blueprint, jarumar ta bayyana cewa, a yanzu ta cika burinta a masana’antar, ta na mai cewa, kwalliya ta riga ta biya kuɗin sabulu a zaman da ta yi a cikin…
Read More
2023: Mulkin Buhari ba komai ba ne face yaudara, inji Saraki

2023: Mulkin Buhari ba komai ba ne face yaudara, inji Saraki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya caccaki jam'iyyar APC mai mulki, inda ya ce jam’iyya ce mai cike da yaudara da mayaudara. Saraki ya bayyana hakan ne a Bauchi, a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, lokacin da kwamitin yaƙin neman zaɓensa ya ziyarci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP domin neman shawari a sakateriyar jam’iyyar a Bauchi. Saraki wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a 2023, Farfesa Tyorwuese Hagher, ya ce APC ta kasa cika alƙawuran da ta ɗauka wa ‘yan Nijeriya a yaƙin neman…
Read More
Ku tsayar da ni takara ku ga yadda zan ci zaɓe cikin ruwan sanyi, Tambuwal ga PDP

Ku tsayar da ni takara ku ga yadda zan ci zaɓe cikin ruwan sanyi, Tambuwal ga PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato, ya roƙi jam'iyya ta duba yiwuwar tsayar da shi takara a babban zaɓen 2023 dake tafe. Tambuwal ya ce matuƙar PDP ta ba shi tikitin takara to zai share mata hawaye ya dawo mata karagar mulkin Nijeriya. A cewar gwamnan, da zaran ya zama shugaban ƙasa zai ɗauko mambobin jam'iyya ya naɗa su manyan muƙamai. Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban mai taimaka masa ta ɓangaren yaɗa labarai, Muhammad Bello, kuma aka raba…
Read More
Kamfanin takin Ɗangote zai bunƙasa harkar noma a Nijeriya – Buhari

Kamfanin takin Ɗangote zai bunƙasa harkar noma a Nijeriya – Buhari

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ce da ta gabata ya ƙaddamar da kamfanin yin takin zamani na hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote, wanda zai riƙa samar da tan-tan na takin zamani na ‘Urea’ ruɓin miliyan uku a kowace shekara, inda Shugaba Buhari ya bayyana ƙwarin gwiwar kamfanin zai yi matuƙar bunƙasa ayyukan gona a ƙasar nan. Sabon kamfanin sarrafa takin zamanin da Shugaba Buhari ya ƙaddamar tare da shaidawar gwamnoni 18 na ƙasar nan, ministoci da jiga-jigan ‘yan kasuwa na ƙasar nan, haɗi da fitattun sarakunan gargajiya, an gina shi ne…
Read More
‘Yan bindiga sun farmaki jirgin ƙasar Abuja-Kaduna

‘Yan bindiga sun farmaki jirgin ƙasar Abuja-Kaduna

Daga BASHIR ISAH Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da harin cikin wata sanarwa da ya fitar a rana Litinin. Kodayake dai Aruwan ya ce jami'an tsaaro sun yi nasarar kuɓutar da jirgin a ƙarshe. A cewar Kwamishinan, "Jami'an tsaro sun sanar da Gwmnatin Jihar Kaduna cewa sojoji sun kuɓutar da jirgin da ya nufi Kaduna daga Abuja daga harin 'yan ta'adda. “Gwamnatin Kaduna ta sami rahotanni da dama a kan harin da 'yan bindiga suka kai wa jirgin Abuja-Kaduna wanda ya auku a yankin Kateri-Rijana." Aruwan ya ci gaba da cewa,…
Read More
Jam’iyyarmu tana buƙatar taimakon kowa – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa

Jam’iyyarmu tana buƙatar taimakon kowa – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullah Adamu ya buƙaci masu son tsayawa takara da su nuna halin haƙuri da kuma karɓar sakamakon taron hannu biyu-biyu. Hakan na ƙunshe ne a jawabin karɓarsa bayan ya lashe zaɓen shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a ranar Asabar a Abuja. Sanata Adamu wanda ya taya maza da mata na jam’iyyar APC murna, ya kuma ja hankalin ’yan takarar da ba su yi nasara a wannan karon ba, ya ƙara da cewa nan da lokacin da Allah ya ƙayyade za su aiwatar da burinsu. Ya ce, “a madadin takwarorina, zaɓaɓɓun…
Read More
Haɗarin shigar da addini cikin siyasa

Haɗarin shigar da addini cikin siyasa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙarshen makon da ya gabata ne wata sabuwar muhawara ta kunno kai a cigaba da shirye shiryen Babban Zaɓen 2023, bayan wani rubutu da wani fitaccen malamin Jami'a da ke zaune a ƙasar Amurka, wanda ya yi fice wajen rubuce-rubuce a shafukan jaridun Nijeriya game da batutuwan da suka shafi ilimi, siyasa da zamantakewa a ƙasar nan, wato Farfesa Farouq Kperogi, ya yi.  Shi dama wannan marubuci ba ɓoyayye ba ne wajen rubuce-rubuce masu rikitarwa da sanya ruɗani, wanda wasu ke yi masa kallon ɗan adawar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ko kuma ɗan koren Yahudawa,…
Read More
Kotu ta tura DCP Abba Kyari da wasu mutum shida  kurkuku

Kotu ta tura DCP Abba Kyari da wasu mutum shida kurkuku

Daga BASHIR ISAH Alƙali Emeka Nwite na Babbar Kotun Abuja ya hana belin DCP Abba Kyari a ci gaba da shari'ar da ake yi na zarginsa da badaƙalar safarar miyagun ƙwayoyi. Kotun ta yi matsayar cewa hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta gabatar da wadatattun hujjojin da suka hana a bayar da belin babban jami'in ɗan sandan wanda aka dakatar da shi daga aiki. Daga cikin bayanan da NDLEA ta gabatar wa kotu har da cewa ba daidai ba ne a bada belin Kyari duba da yanayin shari'ar da ke gaban kotu. Mutum na biyu…
Read More
Sanusi Rikiji ya fito takarar cike gurbin Majalisar Dattawa a Zamfara

Sanusi Rikiji ya fito takarar cike gurbin Majalisar Dattawa a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Rt. Hon. Sanusi Garba Rikiji ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Zamfara ta tsakiya gabanin zaɓen cike gurbi da za a yi a jihar. Idan za a iya tunawa, Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya naɗa Sanata Hassan Muhammad Nasiha wanda yake wakiltar yankin a matsayin mataimakin gwamnan jihar. Rikiji wanda ya riqe muƙamin kakakin majalisar dokokin jihar na tsawon wa'adi biyu, har zuwa lokacin da ya bayyana tsayawa takarar cike gurbin kujerar Sanata Hassan Muhammad Nasiha, shi ne shugaban ma'aikata na kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi…
Read More
Madarasatul Irshad Littahfizul Ƙur’an ta yaye ɗalibai sama da 30 a Legas

Madarasatul Irshad Littahfizul Ƙur’an ta yaye ɗalibai sama da 30 a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Makarantar Madarsatul Irshad Litfahfizul  Ƙur'an dake lamba 9, kan titin Olowolagba a babbar kasuwar ƙasa da ƙasa wadda aka fi sani da suna kasuwar Mile1 da ke Legas ta yaye ɗalibai yara maza da mata sama da talatin. Taron ya gudana ne a harabar makarantar firamari dake kan titin Maidan a ranar Lahadin ƙarshen makon jiya.  Babban sakataren kasuwar ta Mile 12, Alhaji Idiris Balarabe Kano shi ne ya wakilci babban shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam (Dallatun Egbaland Abeokuta) a wajen taron kuma shi ya jagoranci shuwagabannin ɓangarorin kasuwar a wajan taron. Tunda…
Read More