28
Mar
Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi taya murna a hukumance ga sabbin zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyyarsu ta APC ƙarƙarshin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, su 79 da aka zaɓa yayin babban taron jam'iyyar da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata a Abuja. An zaɓi sabbin shugabannin ne don su daidaita wa jam'iyyar APC zama tare da tabbatar da cewa jam'iyyar ta kai ga hayewa tudun mun tsira yayin babban zaɓen 2023. Cikin sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, Buhari ya ce yadda taron nasu ya gudana cikin nasara hakan…
