Editor

9513 Posts
Sin da Indiya sun amince da ƙarfafa tuntuɓar juna domin inganta hulɗarsu

Sin da Indiya sun amince da ƙarfafa tuntuɓar juna domin inganta hulɗarsu

Daga CMG HAUSA Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi dake ziyara a ƙasar India, tare da takwaransa na ƙasar Subrahmanyam Jaishankar, sun amince su ƙarfafa tuntubar juna a tsakanin ƙasashensu, domin ƙara raya dangantakar dake tsakaninsu. Yayin tattaunawar da ministocin biyu suka yi a New Delhi, babban birnin India, Wang Yi ya ce ƙasashen Sin da India da suka kasance maƙwabtan juna dake da jimilar al’umma biliyan 2.8, na da muhimmin ƙarfi na tabbatar da daidaito tsakanin ƙasashen duniya da dunƙulewar tattalin arzikin duniya da kasancewar mutane masu mabambantan al’adu tare da taka muhimmiyar…
Read More
Ci gaban da ke mayar sa hankali kan jama’a na da muhimmanci ga kare haƙƙoƙinsu

Ci gaban da ke mayar sa hankali kan jama’a na da muhimmanci ga kare haƙƙoƙinsu

Daga CMG HAUSA Zaunannen jakadan ƙasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Chen Xu, ya ce ci gaban dake mayar da hankali kan jama’a, shi ne ya kamata ya kasance jigon dabarun kawar da rashin daidaito a tsakanin al’ummun duniya. Chen Xu, wanda ya bayyana haka ga taro na 49 na hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta MDD a Geneva, ya ce annobar COVID-19 ta yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya da ci gaban rayuwar jama’a, musammam ma rayuwar jama’ar ƙasashe masu tasowa. Wannan ya ta’azzara rashin daidaito da haifar da ƙalubaloli masu tsanani ga ci gaban duniya. Don…
Read More
’Yan jarida sun karrama gidan kangararru da gyaran hali a Jihar Bauchi

’Yan jarida sun karrama gidan kangararru da gyaran hali a Jihar Bauchi

Daga ABUBAKAR A. BOLARI Wata ƙungiyar 'yan jarida mai suna ROJOF (Rehabilitations and Orphanage Journalist Covering Forum Bauchi) da suke bayyana aikace-aikacen wani gidan gyaran hali da tarbiyyar kangararru a jaridu da kafafaen yaɗa labarai a jihar Bauchi mai suna 'Malam Kawu Youth Rehabilitation and Orphanage Centre' sun karrama gidan sakamakon gamsuwa da yadda yake gyara tarbiyyar matasan. Ƙungiyar ta karrama mamallakin gidan ne mai suna Dakta Abdullahi Muhammad Tahir da ake kira Malam Kawu, saboda yadda jama’a suka gamsu da yadda yake kula da kangararrun ‘ya’yan su da suka samu matsalar ƙwaƙwalwa sakamakon shaye-shaye da sauran su. A jawabin…
Read More
Gwamnatin Jigawa ta gudanar da rigakafin cutar dabbobi

Gwamnatin Jigawa ta gudanar da rigakafin cutar dabbobi

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jihar Jigawa ta gabatar da rigakafin cutar dabbobi a Ƙaramar Hukumar Kaugama da ke jihar. A jawabin da ya gabatar a lokacin ƙaddamar da allurar rigakafin, shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Idris Mati Hadi ya jaddada ƙudurin sa na tallafa wa makiyaya domin inganta lafiyar dabbobin su. Ya kuma yi kira ga makiyaya da su kai dabbobin su cibiyoyin rigakafi mafi kusa da su domin cin gajiyar shirin. Shi ma a nasa jawabin, shugaban sashin aikin gona da albarkar ƙasa na yankin, Alhaji Ado Musa ya ce kimanin dabbobi dubu 35 da suka haɗar…
Read More
Sin na fatan Amurka da NATO za su koma shawarwari tare da Rasha

Sin na fatan Amurka da NATO za su koma shawarwari tare da Rasha

Daga CMG HAUSA Ƙasar Sin ta yi kira ga Amurka da ƙungiyar tsaro ta NATO, da su hau teburin shawara tare da ƙasar Rasha, ko a kai ga warware ricikin Ukraine yadda ya kamata. Da yake bayyana hakan, yayin taron manema labarai na yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi watsi da zargin da wasu ƙasashe ke yi wa Sin, yana mai cewa, har kullum Sin na kan manufar riko da gaskiya da adalci ne game da batun Ukraine. A jiya Alhamis 24 ga wata, kakakin tawagar Sin a ƙungiyar EU, ya ce sanarwar bayan…
Read More
Ali Nuhu ya zama jakadan wani kamfani a Arewacin Najeriya

Ali Nuhu ya zama jakadan wani kamfani a Arewacin Najeriya

Daga AMINA YUSUF ALI An naɗa fitaccen jarumin finafinan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, a matsayin jakadan kamfanin Checkers Custard na Arewacin Najeriya. Jaridar yanar gizo ta Labarai24.com ta rawaito cewa, an yi naɗin ne a wani taro da kamfanin Checkers Africa suka shirya a jihar Kano da ke Arewa maso yammacin ƙasar. A cewar babban Manajan Kamfanin Checkers da ke nahiyar Afirka, Mista Karan Checker ya bayyana cewa, la’akari da irin shaharar da jarumin ya yi a masana’antar Kanywood da arewacin Najeriya ya sanya kamfanin na Checker ya naɗa shi a matsayin jakadansu na shiyyar Arewa. A yayin  da ya…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 50 a Giwa, Jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 50 a Giwa, Jihar Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindiga sun kai wasu manyan hare-hare kan ƙauyuka shida a Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, inda suka kashe gwamman mutane a yankunan. Gwamnatin Kaduna ta bakin Ma'aikatar Tsaro ta tabbatar da kai harin a ranakun Alhamis da Juma'a, amma ba ta bayyana adadin waɗanda aka kashe ba, tana mai cewa suna jiran cikakken rahoto kan lamarin. Wasu rahotanni da Manhaja ta tattara a ta bakin yadda mutanen yankin ke bayyanawa, sun ce an kashe mutum kusan 50 tare da yin garkuwa da fiye da mutum hamsin. Garuruwan da lamarin ya shafa sun…
Read More
Da ɗumi-ɗuminsa: Masu neman shugabancin APC sun janye wa Abdullahi Adamu

Da ɗumi-ɗuminsa: Masu neman shugabancin APC sun janye wa Abdullahi Adamu

Ana gab da soma kaɗa ƙuri'a ne shida daga cikin 'yan takarar shugabancin jam'iyyar APC da suka shirya fafatawa da zaɓin Shugaba Muhammadu Buhari, suka miƙa wuya suka janye takararsu. Da wannan, ya tabbata cewa Sanata Abdullahi Adamu da ya kasance zaɓin Shugaba Buhari, shi ne zai zama shugaban jam'iyyar APC na ƙasa na gaba. Wasiƙar da ta nuna janyewar 'yan takarar Wata wasiƙa da ta sami sa hannun Sanata Geoge Akume, a madadin 'yan takarar ta nuna yadda baki ɗaya 'yan takarar suka yi wa zaɓin Buhari mubaya'a.
Read More
Yadda ’yan bindiga suka kashe hakimi suka tayar da gari a Zamfara

Yadda ’yan bindiga suka kashe hakimi suka tayar da gari a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 25 da su ka haɗa da hakimi da kuma wasu sarakunan gargajiya a Ƙaramar Hukumar Bukkuyyum da ke a Jihar Zamfara a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya. 'Yan bindigar dai sun afka ƙauyen Ganar Kiyawa ne a ranar Lahadi kuma suka kashe mutanen, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC. Mutanen garin sun ce 'yan bindigar sun shiga garin na Ganar Kiyawa ne saman babura, kuma bayan mutane sun tsorata sun fara tserewa, 'yan bindiga suka dinga harbinsu, cikin waɗanda aka kashe har da hakimin garin Bala…
Read More
Sharhi: Yadda ƙasashen yamma suka nuna fuska biyu ga ‘yan gudun hijira

Sharhi: Yadda ƙasashen yamma suka nuna fuska biyu ga ‘yan gudun hijira

Daga LUBABATU LEI Jama’a, shin a ganinku akwai bambanci a tsakanin ‘yan gudun hijira? Bayan ɓarkewar rikicin soja a tsakanin Rasha da Ukraine, dimbin ‘yan gudun hijira sun kwarara daga Ukraine zuwa sauran ƙasashen Turai da ke maƙwabtaka da ita. Ƙididdigar da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta yi ta nuni cewa, ya zuwa ranar 15 ga wata, kusan ‘yan gudun hijira miliyan uku ne suka gudu daga Ukraine, ciki har da dimbin ‘yan ƙasashen Afirka da ke ɗalibta a ƙasar, kuma dan Nijeriya Alexander Orah na daga cikinsu. Sai dai Alexander Orah ya fuskanci dimbin matsaloli…
Read More