26
Mar
*Abinda ya sa gwamnoni na miƙa wuya gare shi – Gwamnan Nasarawa Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da tsare-tsare a taron Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi A. Sule, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnonin jam’iyyar suka amince wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan zaɓar tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaba na gaba na jam'iyya mai mulki. A ranar gobe Asabar ne dai aka shirya gudanar da taron a Abuja. Da ya ke zantawa da manema labarai kan shirye-shiryen kwamitinsa gabanin zaɓen, Gwamna Sule, ya ce, waɗanda…
