01
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mutane bakwai, ciki har da mace mai juna biyu sun rasu a yayin turereniyar sayen shinkafar da Hukumar Kwastam ta yi gwanjo a kan N10,000 kowane ƙaramin buhu a Jihar Legas. Wasu da dama kuma sun jikkata a turereniyar da ta barke a lokacin da wasu bata-gari suka yi yunƙurin shiga ofishin hukumar da ke gwanjon shinkafar da ƙarfin tuwo. Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da hukumar ta fara gwanjon shinkafar a ofisinta da ke yankin Yaba. Gwanjon shinkafar da hukumar ke yi wani ɓangare na yunƙurinta rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin tsadar…
