29
Feb
"Wasu ƙungiyoyin ba sa son ɗaukar sabon marubuci" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Baƙon marubucin mu na wannan mako shi ne Malam Sadik Abubakar Abdullahi, shugaban ƙungiyar Lafazi Writers Association, ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin marubuta na onlayin da suke taka rawar gani wajen fitar da littattafai masu ƙunshe da basira da darussa masu yawa, da kuma kiyaye ƙa'idojin rubutun Hausa. Ya kasance daga cikin maza marubuta da suka zama tamkar madubi ko ababen koyi ga matasan marubuta masu tasowa. A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya bayyana masa yadda yadda shi da wasu marubuta suka kafa ƙungiyar…
