Editor

9513 Posts
Tsadar Rayuwa: NLC na zanga-zanga a sassan ƙasa

Tsadar Rayuwa: NLC na zanga-zanga a sassan ƙasa

Daga BASHIR A halin da ake ciki, haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta shirya zanaga-zangar lumana a sassan ƙasa domin nuna rashin jin daɗinta game da ƙuncin rayuwar da 'yan ƙasa ke fuskanta. Bayanan da MANHAJA ta kalato a ranar Talata sun nuna an hangi masu zanga-zangar a yankin Ikeja, Jihar Legas. Inda aka ga da damansu ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban kamar "A kawo ƙarshen yunwa da talauci yanzu" da dai sauransu. A Jos babban birnin Filato ma haka lamarin yake, a nan ma an ga ɗaruruwan masu zanga-zangar sun mamaye wasu manyan hanyoyin birnin.…
Read More
‘Yar Nijeriya ta lashe Gasar Karatun Ƙur’ani ta ƙasa da ƙasa

‘Yar Nijeriya ta lashe Gasar Karatun Ƙur’ani ta ƙasa da ƙasa

Daga BASHIR ISAH Wata matashiya mai suna Hajara Ibrahim Dan’azumi daga Jihar Gombe ta lashe Gasar Karatun Ƙur'ani ta Mata zalla ta Ƙasa da Ƙasa da aka gudanar a ƙasar Jordan. Hajara Ibrahim wadda ɗalibar makarantar Islamiyyar Abubakar Siddiq ce kuma 'yar aji biyu a Jami'ar Jihar Gombe, ta zo ta ɗaya ne a rukunin masu karanta izifi 60 da Tajwid a tsakanin ƙasashe 39 da suka fafata a gasar. Wannan shi ne karo na 18 da ake shirya wannan gagarumar gasar karatun Ƙur'ani ta mata zalla a ƙasar ta Jordan. Yayin gasar wadda ta gudana daga 17 zuwa 22…
Read More
Gasiyar abin da ya faru ga jaruma Maryam CTV

Gasiyar abin da ya faru ga jaruma Maryam CTV

DAGA MUKHTAR YAKUBU A 'yan kwanakinnan babu wani labari da ya karaɗe dandalin sada zumunta kamar na haɗarin da jarumar Kannywood Maryam Sulaiman wadda aka fi sani da Maryam CTV ta yi, wadda ta haɗu da haɗarin ne a ranar Asabar da ta gabata 10 ga Fabarairu, 2024. Labarin ya ɗauki hankalin mutane sosai saboda irin yadda aka rinƙa bayar da labarai masu karo da juna da kuma ƙarin gishiri a game da abinda ya faru. Wasu sun rinƙa bada labarin cewa, jarumar ta samu mummanan haɗari ta karairaye a hannu da ƙafa. Wasu kuma suke bada labarin ƙafafun ta…
Read More
Jarumar TikTok Murja Kunya, ta zargi Hisbah da cin zarafin matan da suka kama

Jarumar TikTok Murja Kunya, ta zargi Hisbah da cin zarafin matan da suka kama

Daga AISHA ASAS Shahararriyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta zargi Hukumar Hisbah da cin zarafin mata da sunan gudanar da aikinsu. Ta bayyana hakan ne a wani sautin murya da ta saki, wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta da dama. Duk da cewa, zuwa yanzu babu wani tabbaci da zai iya tabbatar da lokacin da aka yi wannan sautin, wato an yi shi ne kafin ko bayan ta shiga komar hukumar, sai dai an tabbatar da sahihancin sautin da kuma zamewar sautin muryar jarumar. A cikin sautin muryar, Murja ta yi bayyanin irin rawar da ita da abokanenta suka…
Read More
Sake fasalin hukumomin gwamnati: Tinubu ya bada umarnin ɗabbaƙa Rahoton Oronsanye

Sake fasalin hukumomin gwamnati: Tinubu ya bada umarnin ɗabbaƙa Rahoton Oronsanye

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarnin gaggawa jan ɗabbaƙa rahoton Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Sake Fasalin Hukumomin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma'aikatan Tarayya, Mr Stephen Osagiede Oronsaye. Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Mohammed Idris ya sanar da manema labarai hakan jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zatarwa (FEC) a Abuja a ranar Litinin. Idris ya ce matakin zai shafi ma'aikatu da dama inda za a shafe wasu, sannan a gwamasu da wasu daidai da shawarwarin da kwamitin ya bayar. Ya ce, “A yau Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki muhimmin…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 17, sun kashe ɗaya a Katsina

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 17, sun kashe ɗaya a Katsina

Daga SANUSI MUHAMMAD Wasu gungun ‘yan ta’adda sun kai farmaki garin Burdugau da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi a jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da mutane sama da 17 tare da kashe mutum ɗaya. Wakilinmu ya rawaito cewa, yayin farmakin ‘yan bindigan sun isa garin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren Lahadi inda suka shiga gida-gida. Majiya ta ce 'Sun yi awon gaba da ɗaruruwan dabbobin da suka haɗa da awaki, tumaki, shanu, sun yi garkuwa da mata sama da 17, musamman matan aure da wasu 'yan mata, sun kashe mutum ɗaya da aka fi sani da suna Uban…
Read More
‘Yunwa ta sa kan ‘yan Nijeriya ya haɗu’ – Obi

‘Yunwa ta sa kan ‘yan Nijeriya ya haɗu’ – Obi

*Ya cacaki gwamnatin Tinubu Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ƙalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan tsadar kayan abincin da ake fama da ita a ƙasa, yana mai cewa a halin da ake ciki "yunwa ta haɗa kan 'yan ƙasa." Obi ya bayyana haka ne a ranar Litinin, inda ya ce gwamnati ta gaza daƙile matsalar hauhawar farashin kayan abincin da ke ci gaba da addabar 'yan ƙasa. A cewarsa, “A yau, mun zama ƙasa wadda yunwa ta haɗe kanta lamarin da ya kai wasu na mutuwa saboda yunwa da wahala. "'Yan…
Read More
Mun canja rayuwar ’yan shaye-shaye fiye da ɗari – CAWI

Mun canja rayuwar ’yan shaye-shaye fiye da ɗari – CAWI

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wani ɓangare na cigaba da ƙoƙarin ganin an dawo da hankalin matasa da hankalin su ke neman ɓacewa ta dalilin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sinadarai masu bugarwa, wasu matasa a Jos babban birnin Jihar Filato sun yunƙuro domin wayar da kan sauran matasa 'yan uwansu da suka ɗauki hanyar shaye-shaye, da nufin canja musu tunani da salon rayuwa, ta yadda za su zama mutane nagari waɗanda al'umma za ta yi alfahari da su. Muhammad Lawal DeeDee Abubakar shi ne jagoran waɗannan matasa da suka kafa ƙungiyar 'Community Aid Workers Initiative' (CAWI) a ganawarsa da wakilin…
Read More
Dandalin shawara: Ina matuƙar ƙyamar matata a lokacin da ta ke shayarwa

Dandalin shawara: Ina matuƙar ƙyamar matata a lokacin da ta ke shayarwa

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Asas ya yau. Kwana da yawa. Ya iyali. Kin dai san na yi amarya a kwanan baya, kuma kamar yadda muka tattauna a lokaci da yawa Ina matuqar ƙyamar matata lokacin da ta ke shayarwa, dalilin kenan ma da na nemi shawararki a baya, saboda na ce, ba zan iya kusantar matata a lokacin. To yanzu amaryata ta haihu har an yi arba'in, shi ne da sunka yi maganar dawo wa na ce, ta zauna gida tukuna, daga baya ma sai na yi shawarar ta zauna gida har ta yaye jinjirin kana ta dawo. To fa…
Read More
Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin NARTO da NURTW a Nasarawa – Muhammadu Maikwarya

Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin NARTO da NURTW a Nasarawa – Muhammadu Maikwarya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Sabon Shugaban Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri, NURTW, na ƙasa reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Muhammadu Maikwarya ya bayyana cewa, ba shakka kawo yanzu da ya kama aikinsa a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ta Nasarawa ana cigaba da samun kyakkyawar dangantaka tsakanin ƙungiyar tasa da takwararta ta NARTO. Alhaji Muhammadu Maikwarya ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke hedikwatar NURTW a birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar ranar Litini na mako da ake ciki. Ya ce kasancewa shi shugaban NARTO a jihar ɗan uwa ne a gunsa sannan dukan…
Read More