25
Feb
Daga Umar Garba a Katsina Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana cewar tun da ya zama gwamnan jihar Katsina ba qaramar hukumar da ta gagare shi shiga saboda tsoron ta'addacin 'yan bindiga a jihar. "Zancen banza ne 'yan bindiga ke yi cewar za su kai mani hari, ba inda ɗan ta'adda zai hana ni zuwa a Katsina, ba kuma hanyar da zai hana ni bi." Inji gwamnan. Raɗɗa na mayar da martani ne lokacin da yake zantawa da majiyar jaridar Manhaja ta DW, game da wani rahoto dake cewa 'yan bindiga na shirin kai ma shi hari…
