Editor

9513 Posts
Makamashi: Da sake amba mai kaza kai

Makamashi: Da sake amba mai kaza kai

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI Tsarin mulkin ƙasar nan ya tanadi tsare-tsare masu tarin yawa domin ya daga ƙasar da al’umarta a idan duniya, amma abin takaici abin bah aka yake ba. Babban abin takaici, shugbannin ƙasar tun daga kansila har zuwa shugaban ƙasa babu ruwansu da waɗanda suke shugabanta. Tasarrafi da dukiyar ƙasa, wato bitalmali ya zama abin watanda da ga shugabanni saboda haka kowa sai wasa wuƙaƙensu da gatarai a dandalin siyasa domin kawai su sami dama su gididdibi tasu karfatar yaran su suna biye dasu domin fince. ‘Yan ƙasa sun zama ‘yan kallo. Wannan tasa muke cewa…
Read More
Nijeriya ta sanya harajin dole ga kamfanonin dake ɗaukar ma’aikata daga ƙetare

Nijeriya ta sanya harajin dole ga kamfanonin dake ɗaukar ma’aikata daga ƙetare

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta sanya harajin dole na shekara-shekara ga kamfanonin da ke ɗaukar ma'aikatan ƙasashen waje. Gwamnatin ta buƙacin kamfanonin su riƙa biyan harajin dala 15,000 ga kowane darakta, da kuma dala 10,000 daga sauran ma'aikata. Shugaban ƙasar Bola Tinubu, wanda ke cikin matsin lambar inganta tattali arzikin ƙasar, ya ce matakin zai ƙarfafa wa kamfanonin ƙasashen waje gwiwa wajen ɗaukar 'yan ƙasar aiki. Dama dai kamfanonin ƙasashen waje na biyan dala 2,000 a kowace shekara domin samun izinin zama a ƙasar ga ma'aikatansa 'yan ƙasashen waje. A yanzu kuma za su biya ninki…
Read More
’Yan sanda sun kama mahaifin da ya harbe ɗansa saboda abinci

’Yan sanda sun kama mahaifin da ya harbe ɗansa saboda abinci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Abiya ta kama wani mutum da ake zargi da harbe ɗansa bayan da ya fusata saboda ya cinye abinci. Lamarin ya faru ne a yankin Eziama Lokpaukwu da ke ƙaramar hukumar Umunneochi a jihar Abiya. Shaidu sun ce ɗan ya shiga gidan inda ya ɗauki abincin da aka ajiye a tukunya tare da cinyewa. Lamarin ya fusata mahaifinsa saboda rashin neman izini kafin cinye abincin sai kuma suka ce ya shiga ɗaki tare da harbe ɗansa. Mutanen yankin sun fusata inda suka damke mahaifin tare da ƙulle shi kafin…
Read More
Za mu yi iyakar ƙoƙari wajen kare mutuncin ’yan Arewa a Ogun – Sabbin sarakunan Hausawa

Za mu yi iyakar ƙoƙari wajen kare mutuncin ’yan Arewa a Ogun – Sabbin sarakunan Hausawa

Daga DAUDA USMAN a Legas Waɗansu sababbin tagwayen sarakunan al'ummar Hausawa mazauna cikin garin Muwe da ke cikin jihar Ogun sun bayyana cewar za su yi iyakar ƙoƙarinsu wajen kare martabar masarautar al'ummar Hausawan Muwe tare da kawo ci gaban Hausawan yankin baki ɗaya. Sababbin sarakunan sun yi wannan furuci ne a garin Muwe jim kaɗan bayan tashi daga taron naɗa su muƙamai daban-daban a cikin garin Muwe kuma suka bayyana wa jaridar Manhaja farin cikinsu dangane da wannan al'amari. Taron naɗin sarautun wanda ya gudana a garin na Muwe a ranar Lahadin makon jiya sunayen sababbin tagwayen sarakunan da…
Read More
’Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 a Taraba

’Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 a Taraba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 da aka yi garkuwa da su a sansanin masu garkuwa da mutane da ke tsaunin Gongomaliki a yankin ƙaramar hukumar Yorro da ke jihar Taraba. Kwamishinan 'yan sandan jihar, David Iloyanomon, ne ya bayyana haka cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a birnin Jalingo. Kwamishinan ya ce jami'an sun samu nasarar kuɓutar da mutanen ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukna ɓata-garin a yankin. “Wannan na daga cikin yunƙurin da hukumarmu ke yi na kakkaɓe ayyukan ɓata-gari, musamman garkuwa da mutane…
Read More
Maɗaba’ar Kano ta samu kayan aiki da za ta zama ta ɗaya a Arewa – DMD Adamu

Maɗaba’ar Kano ta samu kayan aiki da za ta zama ta ɗaya a Arewa – DMD Adamu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Maɗaba'ar Gwamnatin Kano KPPC mai buga muhimman takardun sirrin gwanati da sauran takardun amfanin al'umma da wallafe-wallafe na gwamnati da na kamfanoni da sauran al'umma yanzu haka ta farfaɗo da ga dogon suman da ta yi na rashin aikin yi da rashin kayan aiki wanda yanzu ta samu kayan aikin da za ta iya zama ta ɗaya Arewacin Nijeriya kamar yadda Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake son ganinta, wanda hakan ce tasa daga zuwansa ya ba su  dama da busa mata rai ta farfaɗo ta hanyar bada damar a cewa dukka abinda muke…
Read More
Masu ruwa da tsaki sun koka kan garƙame iyakar Nijar

Masu ruwa da tsaki sun koka kan garƙame iyakar Nijar

Daga Jamil Gulma a Kebbi  Tun lokacin da Shugaban Ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tunubu, wanda kuma shine Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ya ayyana cewa, akwai yiwuwar ƙaddamar da yaƙi da sojojin da suka hamɓarar da zavavven Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Bazoum, idan sulhu ya gagara, ba shakka wannan ya tayar da  hankalin dubban ’yan Nijeriya mazauna ƙasar ta Nijar da kuma al'ummomin da ke zaune kan iyakokin ƙasashen biyu kuma ya sanya su shiga wani yanayi na tashin hankali. Wakilin Bleuprint Manhaja ya zagaya  waɗansu garuruwa da ke maƙotaka da Nijar din kuma ya zanta da mazauna waɗannan…
Read More
Kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya yi murabus

Kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya yi murabus

Daga BASHIR ISAH Jose Peseiro ya murabus a matsayin mai horar da 'yan wasan Super Eagles na Nijeriya. Peseiro ya sanar da hakan ne a shafinsa na X a ranar Juma'a, 1 ga Maris, 2024. Ya ce kwatiraginsa da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta ƙare, kuma ba a ƙulla sabo ba. Ya bayyana watanni 22 da ys shafe a matsayin babban kocin Super Eagles, a matsayin sadaukarwa. Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen nuna godiya ga 'yan wasan na Super Eagles da hukumar NFF, yana mai cewa a duk lokacin da aka buƙace za a same…
Read More
Masu zanga-zanga sun daka wawa kan babbar mota mai ɗauke da taliyar BUA a Zaria

Masu zanga-zanga sun daka wawa kan babbar mota mai ɗauke da taliyar BUA a Zaria

Daga BASHIR Wasu masu zanga-zanga a yankin Dogarawa a Zaria, jihar Kaduna, sun daka wawa kan wata babbar motar kamfanin BUA mai ɗauke da kayan taliya a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kano. Wannan na zuwa ne kimanin mako guda bayan da wasu jama'a suka daka wawa kan wata babbar mota mai ɗauke da kayan abinci a yankin Sulej, Jihar Neja. Majiyarmu ta ce motar BUA ɗin ta baro Kaduna ne da nufin zuwa Abuja inda 'yan daban suka tare hanya suka far mata. Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 3.15 na…
Read More
Sojojin Nijeriya na iya murƙushe ‘yan ta’adda – Gwamna Sule

Sojojin Nijeriya na iya murƙushe ‘yan ta’adda – Gwamna Sule

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce sojojin Nijeriya na da ƙarfin da za su iya lalata duk wasu masu ɗauke da makamai da ke dagula zaman lafiyar al’umma. Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a yayin gudanar da ayyukan jin daɗin jama’a na Afirka ta Yamma na 2023 na rundunar sojojin Nijeriya ta IV a ƙaramar hukumar Doma ta jihar. Gwamnan ya yaba da kokarin sojoji da sauran jami’an tsaro a yaƙin da suke yi da garkuwa da mutane, ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro a ƙasar nan.…
Read More