Editor

9513 Posts
Tinubu ga ’yan Nijeriya: Ba zan yi gaggawa wajen sake fasalin ƙasa ba

Tinubu ga ’yan Nijeriya: Ba zan yi gaggawa wajen sake fasalin ƙasa ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta sake fasalin ƙasar kamar yadda ya yi alƙawari tun da farko, amma ya lura cewa dole ne a aza harsashi mai kyau. Tinubu ya bayar da wannan tabbacin ne a wata ziyarar da ya kai wa jagoran ƙungiyar siyasa da zamantakewar al’ummar Yarabawa ta ƙasa, Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, a Akure, Jihar Ondo ranar Laraba. Bayan ganawar sirri da wasu zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar, sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na kasa, Mista Jare Ajayi, ya ruwaito shugaban qasar na tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa zai…
Read More
Ramadan: Ɗangote ya ƙudiri aniyar tallafa wa mabuƙata da kayan abinci

Ramadan: Ɗangote ya ƙudiri aniyar tallafa wa mabuƙata da kayan abinci

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hamshaƙin mai arzikin nan Alhaji Aliko Ɗangote mai son tallafawa al'ummar ƙasar nan don sauƙaƙa musu daga halin matsin tattakin arzikin da ake ciki zai tallafawa mabuƙata da kayan abinci kyauta don yin azumin watan Ramadan cikin walwala. Ɗiyarsa Hajiya Fatima Aliko Ɗangote ce ta bayyana hakan, yayin wani taron ganawa da 'yan jaridu na Arewacin Nijeriya da ya gudana a birnin Kano. Hajiya Fatima ta ce mahaifinta ya jima yana gudanar da ayyuka domin kyautata rayuwar al'ummar Jihar Kano, shi ya sa a wannan lokaci ya ƙudiri aniyar tallafawa mabuƙata da kayan abinci sakamakon…
Read More
Uwargidan gwamnan Kebbi ta tallafa wa mata da Naira miliyan 10

Uwargidan gwamnan Kebbi ta tallafa wa mata da Naira miliyan 10

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Uwargidan gwamnan Kebbi Hajiya Zainab Nasir ta tallafawa mata masu ƙananan sana'o'i da Naira milliyan goma a ƙarƙashin hukumar SMEDAN. Uwargidan Gwamnan ta bayar da wannan tallafin ne a lokacin da take halartar taron Ramadan Funfair da ya gudana ranar Lahadi a babban ɗakin taro dake Shugaban Ƙasa wato Presidential Lodge dake cikin garin Birnin Kebbi. Da take jawabi a wurin taron, uwargidan Gwamnan ta bayar da umarnin cewar dukkanin matan da suka halarci taron da sana'o'insu da a tabbatar sun samu wani kaso a cikin gudunmawar kuɗin da ta bayar. Haka kuma ta…
Read More
Jama’a sun wawashe rumbun kayan abinci a Abuja

Jama’a sun wawashe rumbun kayan abinci a Abuja

Daga BASHIR ISAH Wasu mazauna yankin Abuja sun kai mamaye rumbun ajiyar kayan abinci mallakar Hukumar Bada Agajijn Gaggawa ta Nijeriya warehouse belonging (NEMA). MANHAJA ta kalato hakan ya faru ne da safiyar Lahadi a yankin Karimo, Phase 3. Rahotanni sun ce mutane sun kwashi kayayyakin abinci da dama waɗanda ke ajiye a rumbun. Hakan ba ya rasa nasaba da ƙuncin rayuwar da ake fuskanta a ƙasa wanda ya kai ga sayen abinci na gagara talakawa saboda hauhawar farashi.
Read More
Gwamnatin Kano ta dakatar da bikin naɗin sarauta a Masarautar Bichi

Gwamnatin Kano ta dakatar da bikin naɗin sarauta a Masarautar Bichi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da gudanar da babban bikin gargajiya na masarautar Bichi mako guda kafin bikin. Majalisar Masarautar Bichi a wata wasiƙa ta hannun Sakataren Masarautar, mai kwanan wata 2 ga Fabrairu, 2024, ta sanar da gwamnatin jihar game da shirin gudanar da bikin naɗin sarauta mai cike da tarihi wanda aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga Maris, 2024. Bikin, wanda shi ne irinsa mafi girma a Masarautar, za a yi shi ne don ɗaukaka Hakimi, Alhaji Salisu Ado Bayero tare da ba wa wasu fitattun ’yan asalin jihar sarauta…
Read More
Tinubu ga ’yan Nijeriya: Wahalarku ba za ta tashi a banza ba

Tinubu ga ’yan Nijeriya: Wahalarku ba za ta tashi a banza ba

*Shugaban ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziki a kansa Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki cikakken alhakin taɓarɓarewar tattalin arzikin da 'yan Nijeriya ke fuskanta tare da tabbatar wa 'yan ƙasar cewa, wahalhalun da suke fama da shi ba zai faɗi wasa banza ba. Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin ƙungiyar Afenifere a gidan Pa Reuben Fasoranti da ke Akure, Jihar Ondo, a ranar Laraba, 28 ga Fabrairu, 2024. A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaban…
Read More
Ramadan: Gwamnan Kebbi ya bai wa Izala miliyan N10 don tafsir

Ramadan: Gwamnan Kebbi ya bai wa Izala miliyan N10 don tafsir

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya bai wa ƙungiyar Izala mai shalkwata a Jos Naira miliyan goma don gudanar da harkokin tafsir na watan Ramadan da ke tafe. Gwamnan ya bayyana bayar da wannan gudunmawar ne a lokacin gudanar wani babban taron shekara-shekara da ƙungiyar Izala da ke da shalkwata a Jos ke gudanarwa a lokacin karatowar  azumin watan Ramadan wanda ya gudana a babban masallacin Juma'a dake tsohuwar mayanka a cikin garin Birnin Kebbi babban birnin jihar. Da yake jawabi a madadin Maigirma Gwamna, wakilin Gwamnan kuma Kwamishinan ayyuka na musamman Honorabul…
Read More
Masarautar Jama’a ta naɗa wa ’ya’yanta huɗu sarautu

Masarautar Jama’a ta naɗa wa ’ya’yanta huɗu sarautu

Daga ABUBAKAR LABARAN a Kafanchan Masarautan Jama'a da take Ƙaramar Hukumar Jama'a a Jihar Kaduna ta naɗa wa wasu 'ya'yanta huɗu waɗanda suka cancanta sarautun gargajiya. A lokacin da yake naɗa musu sarautun a fadarsa dake Kafanchan a ƙarshen mako, Sarkin Jama'a, Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu ya bayyana cewa an zaɓi waɗanda aka yi wa naɗin ne saboda cancantarsu a bisa ƙoƙarin kawo ci gaban masarautan da suke yi. A dalilin haka Sarkin ya yi kira da su ƙara hoɓɓasa bisa abinda suka saba yi saboda ciyar da masarautar gaba. A nata jawabin, babbar baƙuwa a wajen bikin naɗin, mataimakiyar…
Read More
Jarumi a Nollywood, Mr Ibu ya rasu yana da shekara 62

Jarumi a Nollywood, Mr Ibu ya rasu yana da shekara 62

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa jarumi a masana'antar shirya finafinai ta Nollywood, John Okafor da aka fi sani da Mr Ibu, rasuwa. Tashar Channels Television ce ta bayyana mutuwar jarumin a ranar Asabar. Majiya ta kusa da marigayin ta shaida wa Channels Television cewa, a ranar Asabar da rana jarumin ya riga mu gidan gaskiya a wani asibitin Lekki da ke Legas. Marigayin mai shekara 62, an garzaya da shi asibiti ne kusan mako guda da ya gabata sakamakon rashin lafiya. A shekarar da ta gabata aka yi wa jarumin aiki inda aka cire masa ƙafa guda sakamakon…
Read More
Rashin ɗa’a: An dakatar da Ronaldo wasa ɗaya a Al-Nassr

Rashin ɗa’a: An dakatar da Ronaldo wasa ɗaya a Al-Nassr

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An dakatar da ɗan ƙwallon Al-Nassr Cristiano Ronaldo daga buga wasa ɗaya saboda tanka wa ’yan kallo a wasan da suka doke Al-Shabab a gasar ƙwallon Saudiyya. Magoya bayan Al-Shaabab sun yi ta ihun sunan 'Messi', mutumin da ya kasance babban abokin hamayyar Ronaldo. Al-Nassr ta samu nasara a wasan da ci uku da biyu a birnin Riyadh. Kyaftin ɗin Portugal mai shekaru 39, ya rufe kunnensa sannan ya yi wata alama da hannu. Hukumar ƙwallon Saudiyya - SAFF ta kuma ci tarar Ronaldo ɗin Riyal dubu 30. Kwamitin ɗa'a na ƙwallon Saudiyyar ya ce Ronaldo…
Read More