05
Mar
Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta samu nasarar tantance ma'aikatan jihar da suka yi ritaya 3,079 a ƙoƙarin da take yi na ganin ta warware bashin giradutin da ake bin gwamnatocin da suka gabata. Rabon tsoffin ma'aikatan jihar da samun haƙƙinsu na giraduti tun a shekarar 2011, kamar yadda sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris ta nuna. Sulaiman ya ce kawo yanzu an biya masu karɓar fansho a matakin jiha da ƙananan hukumomi su 1746 kuɗi N2,312,841,065.08. Ya ce a Juma'ar da ta gabata aka fara biyan kashi na…
