Editor

9513 Posts
Ghana na bikin cika shekara 67 da samu ‘yancin kai

Ghana na bikin cika shekara 67 da samu ‘yancin kai

Daga BASHIR ISAH A wannan Larabar ƙasar Ghana ke bikin cika shekara 67 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Ghana ta shafe shekara 83 a ƙarƙashin Turawan mulkin mallaka kafin daga bisani ta samu 'yancin kanta. Shugaban ƙasar na farko, Dr Kwame Nkrumah, ya bayyana samun 'yancin ƙasar a matsayin babban cigaba gane da shugabancin ƙasar. Ranar 6 ga Maris ta kowace shekara Ghana ke bikin ranar zagayowar samun 'yancin kai. Bikin wannan karon zai gudana ne a dandalin Youth Resource Centre da ke Koforidua. A 2017 ne Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya ɗauki matakin jujjuya in…
Read More
Ramadan: Al’ummar Kebbi za su yi azumi cikin wadatar wutar lantarki

Ramadan: Al’ummar Kebbi za su yi azumi cikin wadatar wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kebbi, Gwamna Nasir Idris, ya yi zama da kamfanin lantarki KAEDCO inda suka tattauna yadda za a samar da wutar lantarki na sa'o'i 24 kulli yaumi a faɗin jihar yayin watan Ramadan mai zuwa. Da yake jawabi yayin tattaunawar, Gwamna Idris ya nuna matuƙar damuwa kan yadda ake fana da ƙarancin wutar lantarki a jihar. Ya ce sun cimma yarjejeniya da KADECO kan yadda za a tabbatar da wadatar wutar yayin azumin Ramadan domin bai wa al'ummar jihar damar yin azumi da cikin walwala. “Na gayyaci Manajin Darakta na KAEDCO don tattaunawa. Akwai buƙatar mu…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ana zargin CPG da kashe fitaccen malami a Zamfara

Da Ɗumi-ɗumi: Ana zargin CPG da kashe fitaccen malami a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Ana zargin Dakarun Tsaron Al’ummar Jihar Zamfara (CPG) da yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin a jihar, Sheik Abubakar Hassan Mada yankan rago. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an na CPG sun yi dirar mikiya ne a gidan marigayin dake garin Mada ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar Talata inda suka ɗauke shi zuwa wajen garin. An ce jami’an sun tafi da shi domin yi masa tambayoyi dangane da matsalar rashin tsaro a yankin. Wani mazaunin garin Mada da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, jami’an CPG sun je…
Read More
Babban ƙalubale a Nijeriya

Babban ƙalubale a Nijeriya

Daga NAFI'U SALISU Akwai abubuwa da dama waɗanda suke faruwa a ƙasar nan, waɗanda sune babban ƙalubalen da yake hana mu zama lafiya da kwanciyar hankali tare da ci gaban kanmu da kanmu. Daga lokacin da muka yi tunani mai kyau, kuma muka ɗaura ɗamarar gyarawa, to ko shakka babu al'amurranmu za su sauya.. Kafin mu yi kuka da hawaye ko babu hawaye, yana da kyau mu fara dubawa mu ga menene dalilin yin kukan namu? Domin kuwa komai da yake faruwa a rayuwa yana da dalili, babu wani abu da ke faruwa haka kawai ba tare da sila ba.…
Read More
Ma’aurata ku matso

Ma’aurata ku matso

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake saduwa a wani makon a shafinku mai albarka na zamantakewa. Da ke zuwar muku kowanne mako a jaridarku ta Blueprint Manhaja. A wannan karon muna tafe da wani batu mai nauyi da muka yi bincike a kansa muka gano yana da matuƙar tasiri wajen gyarawa da rusa aure. Kodayake, a ƙasar Hausa wannan magana ce mai ɗan nauyi, amma a binciken da muka yi a 'yan shekarun nan matsala jima'i na daga cikin matsalolin da suke lalata rayuwar aure. Ire-iren matsalolin sun haɗa da rashin ita kanta mu'amalar aure, rashin lafiyar gaɓoɓin…
Read More
Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Nijeriya za ta tura tawaga Nijar

Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Nijeriya za ta tura tawaga Nijar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Sanatocin Jihohin Arewacin Nijeriya ta ce za ta tura wakilanta jamhuriyyar Nijar, domin ganawa da shugabannin mulkin sojin ƙasar, kan yadda za a mayar da mulki ga farar hula. Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne, bayan sanar da janye takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar da Mali da kuma Burkina Faso waɗanda sojoji ke jan ragamar mulkin su. Kakakin ƙungiyar sanatocin, Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce ƙungiyar za ta tura tawagar ba tare da vata lokaci ba. Janye takunkuman da ECOWAS ta yi zai sake buɗe harkokin cinikayya da zai taimaka…
Read More
Mutum 12 sun mutu, 28 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Zaria – Hukuma

Mutum 12 sun mutu, 28 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Zaria – Hukuma

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa ta ce aƙalla mutum 12 sun mutu sannan 28 sun tagayyara sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da su a babbar hanyar Zaria zuwa Kano. Shugaban hukumar na Jihar Kaduna, Kabir Nadabo ne ya bayyana haka a ranar Litinin. Nadabo ya ce hatsarin ya auku ne a yankin ƙauyen Tashar Yari da misalin ƙarfe 7:36 na safe Ya ce tirelar da lamarin ya shafa mai lambar rijista KTG 454 ZZ na kan hanyarta ta zuwa Kano ne inda ta gamu da hatsari. Ya bayyana cewa, yin obatekin ba bisa ƙa'ida ba da…
Read More
Ina da saurin yin kuka, shi ya sa na fi son rol ɗin tausayi – Sarauniya Zully

Ina da saurin yin kuka, shi ya sa na fi son rol ɗin tausayi – Sarauniya Zully

Daga IBRAHIM HAMISU Zaliha Ishaq Abdullah da a ka fi sani da Sarauniya Zully, jaruma ce a Masana'antar Kannywood kuma ƴan jarida ce, a tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu a Jos, za ku ji tarihinta, da kuma shekarun da ta yi a Kannywood, da kuma yadda take haɗa aikin jarida da kuma yin fim, ku biyo mu don jin yadda tattaunawar ta kasance: MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanka ga masu karatunmu? SARAUNIYA ZULLY: Sunana Zaliha Ishaq Abdallah (Sarauniya Zully). Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?Ni 'yar Jihar Adamawa ce. A can aka haife ni sannan…
Read More
Shawara ga ‘yan uwa mata

Shawara ga ‘yan uwa mata

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI Assalamu alaikum. 'Yan uwa mata barkanmu da wannan lokaci. Allah Ya shirya mana zuri'a bakiɗaya. Zan yi amfani da wannan damar da na samu wurin yi mana tuni da kuma lurar da mu kan muhimmancin tarbiyya musamman a wannan zamanin da muka samu kanmu. Shawarata gare mu 'yan uwa mata dukka, duba da irin yanayin da muke ciki yanzun na taɓarɓarewar tarbiyya, 'yan uwa mu farka daga barci, mu san qima da darajojin da Allah SWT yai mana ba kaɗan ba ne, mu san ciwon kanmu, mu tashi tsaye wajen ganin ɗiyanmu sun samu tarbiyya ta…
Read More
Alaƙar kayan ƙarin ni’ima da ciwon sanyi

Alaƙar kayan ƙarin ni’ima da ciwon sanyi

Daga AISHA ASAS A 'yan kwanakin baya mun yi darasi mai tsayi da ya shafi ciwon sanyi, abinda ke kawo shi, ma'anar sa, alamomi da sauransu. Kuma a taƙaice mun faɗa cewa, tushe-tushe, ko saka wasu abubuwa a farji da sunan gyara na iya zama silar gayyatar ciwon sanyi. A wannan satin za mu buɗe wannan darasi da amsa tambayar alaƙar da ke tsakanin kayan mata, ko ince hakin maye ko magungunan ƙarin ni'ima da ciwon sanyi. Idan mun soma da ainahin kayan da ake haɗawa da sunan ƙarawa mace ni'ima, za mu tarar ababe ne da suka haɗa ababe…
Read More