Editor

9513 Posts
’Yan bindiga sun kashe makiyayi, sun kora shanu 50 a Filato

’Yan bindiga sun kashe makiyayi, sun kora shanu 50 a Filato

Daga BASHIR ISAH ‘Yan bindiga sun kashe makiyayi ɗaya da dabbobi guda 50 da suka haɗa da shanu da tumaki a wani hari da suka kai ranar Talata a yankin Fanzo da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Jihar Fialato. Alhaji Dan-Azumi, wanda ya rasa shanu 21 a harin, ya faɗa wa Daily Trust cewar, maharan sun ji wa wani makiyayi da ke kiwo a yankin rauni. Ya bayyana cewa, “Maharan sun faɗo yankin inda suka yi harbi da bindiga. Sun kashe makiya ɗaya sannan sun jikkata mutum ɗaya. “’Yan bindigar sun yi awon gaba da shanu aƙalla guda 50,…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da gomman yaran firamare a Kaduna

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da gomman yaran firamare a Kaduna

Daga BASHIR ISAH Jama’a sun shiga halin firgici da  ruɗani  a garin Kuriga da ke  ƙaramar hukuma Chikun a Jihar Kaduna bayan da ‘yan bndiga suka kai hari Makarantar Firamare ta Kuriga (1) da ke yankin inda suka yi awon gaba da gomman yara. Duk da dai babu tabbaci kan adadin yara da aka sace, sai dai mazauna yankin sun ce yaran za su kai kimanin su 100. Daily Trust ta kalato cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:20 na safe na ranar Alhamis. Wani mazaunin yankin mai suna Shitu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, in da ya…
Read More
Rashin kiyaye ƙa’idojin rubutu illa ce ga marubuci – Mubarak Jiƙamshi

Rashin kiyaye ƙa’idojin rubutu illa ce ga marubuci – Mubarak Jiƙamshi

"Manazarcin Hausa na samun tagomashi mai tsoka a harkar fashin baƙi ko tambihi" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mubarak Idris Jikamshi, matashin marubuci ne daga Jihar Katsina, duk da kasancewar bai fitar da wasu littattafai masu yawa ba, amma yana da gajerun labarai da dama da ya yi, wasu ma har ya shiga gasannin marubuta da su, a mataki daban-daban. Wani abu da ya bambanta Mubarak da sauran marubuta shi ne kishin da yake da shi a nazarin ilimin harshen Hausa da kula da kiyaye ƙa'idojin rubutu, don yanzu haka yana matakin fara digirinsa na biyu ne a harshen Hausa. Bayan…
Read More
Marigayi Mada Garin Aliyu Babba Ɗan Malam Muhammadu Sambo

Marigayi Mada Garin Aliyu Babba Ɗan Malam Muhammadu Sambo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD Asalin su Fulani ne da suka fito daga yankin Ningi ta Jihar Bauchi da zummar za su kai caffa a wajen Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo Tagammadahullahu birahamatihi a Sakkwato domin shiga dumu-dumu a cikin jihadin jaddada addinin Musulunci wanda Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo ya jagoranta. Sun zauna a wurare da dama kamar Ƙiru da Gwarzo (da ke Jihar Kano ta yau) da Matazu da Fawwa ( dake Jihar Katsina a halin yanzu) da kuma Wonaka da ke Jihar Zamfara ta yanzu, kafin daga bisani Malam Muhammadu Sambo ya jagorance su ya zuwa inda suke a halin yanzu.…
Read More
Da yawan matan da suka yi kwantai dogon buri ne sila – Fatima Danborno

Da yawan matan da suka yi kwantai dogon buri ne sila – Fatima Danborno

Hana lefe kawai ba zai iya samar da yawaitar yin aure tsakanin matasa ba - Saliha Zariya (Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS Idan mai karatu bai manta ba, mun faro tattaunawa kan muhimmancin lefe a Ƙasar Hausa, inda muke tattaunawa da Hajiya Saliha Abubakar Abdullahi Zariya da kuma Fatima Ibrahim Garba Danborno. A wannan satin za mu ɗora ne daga inda muka tsaya: MANHAJA: Wasu na ganin yin lefe kan taimaka wa miji bayan aure, domin ya ɗauke nauyin sutura na tsayin lokaci. Sis Fatima, me za ki iya cewa kan hakan? Yin lefe yana taimaka wa…
Read More
Ba jami’an CPG suka kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada ba – Gwamnatin Zamfara

Ba jami’an CPG suka kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada ba – Gwamnatin Zamfara

*An kama waɗanda ake zargi Daga BASHIR ISAH Aƙalla 'yan banga 10 ne aka tsare bisa zargin kisan malamin addini a Jihar Zamfara. MANHAJA ta rawaito an kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada ne a ranar Talata a garin Mada da ke cikin yankin Ƙaramar Hukumar Gusau a jihar. Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya ce waɗanda hukuma ta kama 'yan banga ne ba jami'an bai wa al'umma kariya (CPG) ba. MANHAJA ta rawaito ana zargin jami'an CPG da yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada kisan gilla, lamarin da ya jefa al'ummar jihar cikin ruɗani. Sai dai sanarwar da Sulaiman…
Read More
Masu dukan mata ku tuba ku daina!

Masu dukan mata ku tuba ku daina!

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kwanaki wata marubuciya ta yi wani rubutu a shafinta na manhajar Facebook, inda ta bayyana takaicinta game da halayyar wasu azzaluman maza da ke cin zarafin matansu ta hanyar duka, abin da ya jawo muhawara mai zafi daga ɓangarori daban-daban, sakamakon yadda wannan mummunar halayya ke ci musu tuwo a ƙwarya. Mata da dama, musamman masu aure, suna kokawa da yadda wasu mazan ke kasa daurewa fushi da vacin ransu, da zarar matansu sun musu wani kuskure ko laifi sai su hau jibgarsu kamar jakuna, ba mutane ba. Wani lokaci ma idan abin ya zo…
Read More
Boko Haram ta ƙona gomman gidajen ‘yan gudun hijira a Borno

Boko Haram ta ƙona gomman gidajen ‘yan gudun hijira a Borno

Daga BASHIR ISAH Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari tare da ƙona gidaje sama da 25 da aka gina wa ‘yan gudun hijirar da suka koma matsuguninsu a yankin Ƙaramar Hukumar Dikwa a Jihar Borno. Daily Trust ta rawaito cewar, matsalar rashin tsaro ta sa mazauna Dikwa sun gudu sun bar gidajensu zuwa neman mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijira. Ta ƙara da cewa, kwanaki kaɗan bayan da suka yi garkuwa da wasu ‘yan gudun hijira da suka tafi neman itacen hura wuta a daji, ‘yan bindigar sun kuma kai hari a ƙauyen Gajibo inda…
Read More
EFCC ta kama manyan motoci 21 maƙare da kayan abincin fasaƙwauri a Borno

EFCC ta kama manyan motoci 21 maƙare da kayan abincin fasaƙwauri a Borno

Daga BASHIR ISAH Hukumar EFCC ta ce ta kama wasu manyan motoci guda 21 maƙare da kayan abinci da sauransu wanda aka yi nufin fitarwa zuwa N’djamena a Jamhuriyar Chadi da kuma Kamaru ba bisa ƙa’ida. Kakakin EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fita a ranar Talata, inda ya ce jami’an da ke aiki qarqashin ofishin hukumar na shiyyar Maiduguri ne suka kama motocin a yankunan Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama a Jihar Borno. Oyewale ya ce za a gurfanar da waɗannan aka kama da motocin a kotu da zarar an kammala bincike. A…
Read More
Batun aiwatar da rahoton ‘Oransaye’

Batun aiwatar da rahoton ‘Oransaye’

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye. Wannan na daga cikin abubuwan da aka cimmawa a taron Majalisar Zartarwar Tarayya na ranar Litinin 26 ga watan Fabrairu, wanda shugaba Tinubu ya jagoranta a Abuja. Rahoton Stephen Oransaye na shekarar 2012 ya bayar da shawarar haɗe wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati waɗanda ayyukan su ke da alaqa da juna, a wani mataki na rage kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati. Bayan taron Majalisar Zartarwar ne hukumomi suka fitar da sanarwa inda suka ce an yanke hukuncin aiwatar da rahoton Steve Oronsaye domin…
Read More