Editor

9513 Posts
Gwamnan Zamfara ya sha alwashin hukunta waɗanda suka kashe Sheikh Abubakar

Gwamnan Zamfara ya sha alwashin hukunta waɗanda suka kashe Sheikh Abubakar

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya lashi takobin hukunta waɗanda suka kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada a jihar. Wasu da ake zargin 'yan banga ne suka kashe malamin a makon jiya a garin Mada, cikin Ƙaramar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara. Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ran Juma'a cewa, Gwamna Lawal ya ziyarci garin Mada don yi musu ta'aziyya kan rasuwar malamin, inda a nan ya yi sallar Juma'a a babban masallacin garin. Ya ce, yayin da yake yi wa jama'a jawabi, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin zai yi…
Read More
Gwamnan Kano ya rantsar da sabbin alƙalan Babbar Kotun Jiha da na ɗaukaka ƙara

Gwamnan Kano ya rantsar da sabbin alƙalan Babbar Kotun Jiha da na ɗaukaka ƙara

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya rantsar da sabbin alƙalai a matakan kotunan jihar daban-daban. Alƙalan da rantsarwar ta shafa sun haɗa da alƙalan Babbar kotun Jiha guda tara da kuma alƙalan kotun ɗaukaka ƙara na shari'ar Musulunci guda uku huɗu, bayan da Hukumar Kula da Shari'a ta Ƙasa (NJC) da kuma Majalisar Dokokin Jihar Kano suka amince da naɗin nasu. Sanarwar da Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta ce, waɗanda aka naɗa a matsayin alƙalan Babbar Kotun Jihar su ne, Justice Fatima Adamu, Justice Musa Ahmad, Justice Hauwa Lawan,…
Read More
Na gamsu da yadda Kwastom suka daina wawashe kayan ‘yan kasuwa – Sarkin Kano

Na gamsu da yadda Kwastom suka daina wawashe kayan ‘yan kasuwa – Sarkin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nuna gamsuwarsa bisa yadda aka samu fahimtar juna tsakanin 'yan kasuwa da jami'an Hukumar Fasa-ƙwauri ta Ƙasa wajen sakar musu mara ba tare da barin shiga kasuwanni ana kwashe musu kaya. Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙoncin Shugaban hukumar na ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi a fadarsa. Ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na'isa, ya aike wa Manhaja ya ce, Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya ce a baya sun sha karɓar ƙorafe-ƙorafe na yan…
Read More
Rikicin siyasar Ribas: A shirye nake na sauka daga kujerar gwamna – Fubara

Rikicin siyasar Ribas: A shirye nake na sauka daga kujerar gwamna – Fubara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Sim Fubara na Jihar Ribas ya bayyana aniyarsa ta barin kujerarsa domin samun dorewar zaman lafiya a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da AIT a ranar Alhamis, 7 ga Maris, 2024. A cewarsa, babu wata sadaukarwa da ta zarce shi da zai biya domin samun nasarar jihar. Fubara ya ci gaba da cewa akwai abubuwan da zai iya yi waɗanda za su haifar da "rikicin gaba ɗaya". Duk da haka, ikonsa na kamewa ko da yana da iko. A yayin tattaunawar, Fubara ya ce, “Babu wata…
Read More
Yadda kamfanonin layin waya suka kulle layuka miliyan 40 saboda Lambar ’Yan Ƙasa

Yadda kamfanonin layin waya suka kulle layuka miliyan 40 saboda Lambar ’Yan Ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sama da layukan waya miliyan 40 ne kamfanonin sanadar na MTN, Airtel, Glo suka kulle a ƙarshen mako biyo bayan ƙarewar wa'adin ranar 28 ga Fabrairu, 2024 da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta bayar na tilasta wa masu amfani da layuka haɗawa da Lambobin Shaidar Ɗan Ƙasa, NIN. Hakan ya nuna an samu ƙaruwar miliyan 28 daga layukan waya miliyan 12 da aka fara shirin kullewa, biyo bayan umarnin NCC. A cikin sanarwar Disamba 2023, NCC ta buƙaci kamfanoin da su toshe layukan da ba a haɗa su da lambar NIN na masu su ba a…
Read More
Kuriga: Za mu ceto yaran da aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya – Gwamna Sani

Kuriga: Za mu ceto yaran da aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya – Gwamna Sani

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya sha alwashin ceto ɗaliban firamaren da 'yan fashin daji suka yi garkuwa da su a yankin Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a jihar. Ya sha alwashin ne a ranar Alhamis sa'ilin da ya ziyarci yankin domin jajanta musu kan abin da ya faru. Ya ce ba a tabbatar da haƙiƙanin adadin yaran da aka sacen ba, amma cewa gwamnati na aiki tare da hukumar makarantar da ma al'ummar yankin wajen gano yawan yaran da aka yi awon gaba da su ɗin. Ya ƙara da cewa, “Za a kafa kwamitin tsaro…
Read More
Ahmed Musa ya dakatar da kwantiraginsa da Sivasspor ta Turkiyya

Ahmed Musa ya dakatar da kwantiraginsa da Sivasspor ta Turkiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rahotanni sun bayyana cewa kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ya soke kwantiraginsa da ƙungiyar Sivasspor ta Turkiyya. An kawo ƙarshen kwantiragin tsakanin Musa da Sivasspor ta hanyar yarjejeniya. Ɗan wasan mai shekaru 31 ya ɗauki matakin ne bayan ƙungiyar ta kasa biyan albashin sa na watanni shida da suka gabata. Ɗan wasan gaba ya riga ya fara aiki don komawa wani kulob a lokacin bazara. Musa ya koma Sivasspor daga wata ƙungiyar Turkiyya Fatih Karagumruk a shekarar 2022. Ya buga wasanni tara a ƙungiyar ba tare da samun nasarar zura ƙwallo ko ɗaya a raga…
Read More
Yadda Kakakin majalisar Bauchi ya koma muƙaminsa bayan yin murabus  

Yadda Kakakin majalisar Bauchi ya koma muƙaminsa bayan yin murabus  

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Tsohon Kakakin Majalisar Dokoki Jihar Bauchi wanda a zaɓen gama-gari na ranar 18 ga watan Maris ta shekarar da ta gabata 2023 ya tsaya takarar zaɓen wa'adin wakilci zango na biyu, amma ya faɗi zaɓen, a ranar Laraba ya sake ɗare wa kujerar da ta shugabancin majalisar, sakamakon zaɓen cike gurbi da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta yi a ranar 3 ga watan Fabrairu da ya gabata.  Ɗan takarar shiga majalisar dokoki na jam'iyyar APC daga mazaɓar Ningi ta Tsakiya, Malam Khalid Ningi, shine ya ƙalubalancin zaɓen na tsohon kakakin majalisa Abubakar Yakubu…
Read More
Abinda ya sa Sanusi fashewa da kuka a ta’aziyyar Shugaban bankin Access

Abinda ya sa Sanusi fashewa da kuka a ta’aziyyar Shugaban bankin Access

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmawa a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.  Yayin da yake jawabi a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami'an bankin da ya rasu a wani hatsarin jirgi tare da iyalinsa a Amurka, sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwar mista Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa. “Na yi tunanin zan riga mista Herbert rasuwa. duka mun san irin kirkinsa, da biyayyarsa," inji Muhammadu Sanusi ll, lokacin da…
Read More
An sace ’yan firamare sama da 100 a Kaduna

An sace ’yan firamare sama da 100 a Kaduna

…Sojoji sun yi wa ’yan ta'adda ruwan wuta a Katsina da Zamfara Daga MAHDI M. MUHAMMAD An sace ɗaliban firamare da na sakandare sama da 100 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna. Kawo yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da aka sace, amma mazauna yankin sun ce kusan 100 ne. Rahotanni sun ce shugaban makarantar da wasu ma’aikatan makarantar na cikin waɗanda abin ya shafa. An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:20 na safe a lokacin da ɗaliban ke taro (assembly) na ranar Alhamis. Ɗaliban sakandare sun koma…
Read More