09
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD La Liga na nazarin wani bidiyo da ake zargin yana nuna wariyar launin fata ga Vinicius Jr a wasan da Real Madrid ta buga da Valencia a ƙarshen makon da ya gabata. Bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta na Intanet ya nuna yadda wani yaro mai goyon bayan Valencia ke jagorantar cin zarafin ɗan wasan. Vinicius ya zura ƙwallaye biyu a wasan da suka tashi 2-2 a ranar Asabar kuma ya yi murna ta hanyar ɗaga hannunsa sama. Ɗan wasan mai shekaru 23 ya fuskanci cin zarafi na wariyar launin fata sau da dama…
