10
Mar
Daga IBRAHIM HAMISU a Bauchi Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al'umma CITAD ta samar da wata 'bukkar Intanet", kana ta damƙawa al'ummar garin Jama'are da ke Jihar Bauchi, aka kuma ƙaddamar da ginin bukkar a hedkwatar Ƙaramar Hukumar Jama'are ranar Asabar da ta gabata. Babban Daraktan Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al'umma CITAD Engr. Yunusa Zakari Ya'u ya bayyana cewa a cikin wannan tsari mai taken Digital Hub za su gina ire-iren wannan bukka ta intanet guda 20 cikin shekara ɗaya a faɗin Nijeriya. Y. Z. ya ce: "Kwamfutocin da ke cikin wannan bukka ba kamar sauran kwamfutoci…
