Editor

9513 Posts
Zargin Cushen Kasafi: Ningi na fuskantar haɗarin dakatarwa daga Majalisa

Zargin Cushen Kasafi: Ningi na fuskantar haɗarin dakatarwa daga Majalisa

*Gobe Majalisa za ta yi zama kan zargin Daga BASHIR ISAH Ya zuwa ranar Talata,12 ga Maris, ake sa ran Majalisar Dattawa za ta yi zama kan zargin da Sanata Abdul Ningi (PDP Bauchi ta Tsakiya) ya yi inda ya ce an yi cushe a kasafin 2024. A hirar da BBC Hausa ta yi da shi a ƙarshen mako, an jiyo Sanata Ningi ya yi zargin cewa, kasafin 2024 da Majalisa ta amince da shi tiriliyan N25 ne, amma wanda ake aiki da shi tiriliyan N28.7. Ya ce, “A karon farko a tarihin Nijeriya, yau muna amfani da kasafi guda…
Read More
Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fama da yunwa a duniya

Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fama da yunwa a duniya

Rahotanni daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa sama da mutane miliyan 113 a faɗin ƙasashe 53 ne suka fuskanci matsananciyar yunwa a shekarar da ya gabata a sanadiyyar yaƙe-yaƙe, annoba da kuma matsalolin tattalin arziki wanda ke haddasa ƙarancin abinci. Aqalla ’yan Nijeriya miliyan 25 ne ke fama da yunwa, yayin da mutane miliyan 9.3 ke fama da matsanancin ƙarancin abinci, wanda hakan ya sa ake ta samun zanga-zanga da fasa rumbunan adana abinci a wasu sassan ƙasar, daidai lokacin da ƙasar ke tsaka da fama da tashen-tashen hankula na masu ɗauke da makamai. Nijeriya na fuskantar rikici daga…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Sodangi ya riga mu gidan gaskiya

Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Sodangi ya riga mu gidan gaskiya

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa Sanata Abubakar Danso Sdangi rasuwa. Ya rasu ne ranar Lahadi da daddare, inda ya bar duniya yana da shekara 70. A halin rayuwarsa, Marigayin jigo ne a jam'iyyar APC a shiyyar Nasarawa ta Yamma. Kuma shi ne Shugaban Kwamitin Neman zaɓe na Gwamna Abdullahi Sule a 2023. Ya wakilci shiyyar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawa na tsawon shekara 12.
Read More
Gobara ta tashi a tashar lantarki a Kano

Gobara ta tashi a tashar lantarki a Kano

Daga BASGIR ISAH Tashar wutar lantarkin da ke Dan’Agundi a Jihar Kano ta kama da wuta a ranar Lahadi. A cewar wani jami'in Kamfanin Lantarki (TCN) a Kano, gobarar ta shafi wasu manyan tiransifoma da ke tashar. Ya ce, “Ni ma ba na ofis, yanzun nan ake sanar da ni wutar ta shafi tiransifoma biyu, amma guda daga ciki na aiki. "Haka nan akwai wani guda da ba a fara aiki da shi ba, shi ma wutar ba ta shafe shi ba." Da yake amsa tambaya, jami'in ya ce abin da ya faru ba zai hana tashar ci gaba da…
Read More
Ku mayar wa ‘yan kasuwa kayan abinci da kuka ƙwace, umarnin Tinubu ga Hukumar Kwastom

Ku mayar wa ‘yan kasuwa kayan abinci da kuka ƙwace, umarnin Tinubu ga Hukumar Kwastom

Daga UMAR GARBA a Katsina Babban Kwantorola na Hukumar Hana Fasa-ƙwauri ta Ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce Shugaban Ƙasa asa Bola Ahmed Tinubu, ya ba wa hukumar umarni a kan ta mayar da kayan abinci da ta ƙwace daga hannun wasu 'yan kasuwa don sake kai su kasuwanni a sayar wa 'yan ƙasa. Shugaban hukumar ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a garin Kwangwalam dake iyakar ƙaramar hukumar Mai'adua a jihar Katsina. A cewarsa, umarnin mayar da kayan abincin, wani jinƙai ne daga Shugaba Tinubu da kuma tabbatar da cewa al'umar ƙasar…
Read More
Tinubu ya hana likitoci tafiya hutu ƙetare

Tinubu ya hana likitoci tafiya hutu ƙetare

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta sanya dokar hana fita hutu ga likitoci da ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan kiwon lafiya da sukan ƙetare zuwa yin hutu a waje. Ƙaramin Ministan Lafiya, Dokta Tunji Alausa, shi ne ya bayyana haka ranar Asabar a Abeokuta. Ya ce daga yanzu, dole ma'aikatan lafiya da ke zuwa ƙetare neman aiki su yi nurabus kafin su tafi. Ya ƙara da cewa, wannan umarni na ƙunshe ne cikin umarnin da Shugaban Ƙasa Tinubu ya bayar. A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne domin magance ƙalubalen da ake fuskanta a ɓangaren kula da…
Read More
An ga watan Ramadan a Saudiyya

An ga watan Ramadan a Saudiyya

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙolin Saudiyya ta ce gobe Litinin shi ne zai zama 1 ga watan Ramadan na 1445 biyo bayan ganin jinjirin watan da aka yi da yammacin Lahadi. Da wannan ake sa ran al'ummar musulmin ƙasar su tashi da azumi a ƙasa kamar yadda jaridar Arab News ta rawaito.
Read More
A ƙara haƙuri game da ƙarancin wuta – Mininstan Lantarki ga ‘yan Nijeriya

A ƙara haƙuri game da ƙarancin wuta – Mininstan Lantarki ga ‘yan Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan ma'aikatar samar da hasken wutar lantarki a Nijeriya, Bayo Adelabu ya ce yana cike da damuwa kan yadda ɓangaren samar da wuta ke ci gaba da taɓarɓarewar a faɗin ƙasar. Ministan na lantarki ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya nuna vacin ransa kan raguwar wutar lantarki da ake samu duk da irin ƙoƙari da ake yi a ɓangaren. “Dangane da haka ne na gayyaci shugabannin kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) da kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC), da kuma Babban…
Read More
Alhaji Abdulrahman Aliyu ya zama Sarkin Fulanin Dakwa na farko a Abuja

Alhaji Abdulrahman Aliyu ya zama Sarkin Fulanin Dakwa na farko a Abuja

Daga DAUDA USMAN a Legas A ranar Asabar ta makon jiya majalisar mai Martaba Sarkin Dakwa a Abuja, Alhaji Dakta Alhassan Musa Baba Chikuri ta yi naɗe-naɗen hakimanta a garin Abuja. Alhaji Abdulrahaman Ishak Bin Aliyu Dotsa yana ɗaya daga cikin waɗanda majalisar ta naɗa, inda da amincewar Sarkin na garin Dakwa Dakta Alhaji Alhassan Musa Baba majalisar ta naɗa Alhaji Abdulrahaman Ishak Bin Aliyu a matsayin sabon Sarkin Fulanin garin Dakwa na farko. Taron naɗe-naɗen sarautun wanda ya gudana a harabar fadar mai martaba Sarkin Dakwa Alhaji Alhassan Musa a ranar Asabar ɗin ƙarshen makon jiya. Taron ya samu…
Read More