Editor

9513 Posts
Ƙarancin Abinci: Gwamnan Kano ya yi kira kan a sake buɗe iyakokin ƙasa

Ƙarancin Abinci: Gwamnan Kano ya yi kira kan a sake buɗe iyakokin ƙasa

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya taimaka ya sake buɗe iyakokin ƙasa don shigowa da kayan abinci wanda a cewarsa, hakan zai taimaka wajen daƙile ƙarancin abincin da ake fama da shi a ƙasa. Wannan kira na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wadda aka fitar jim kaɗan bayan da Gwamnan ya karɓi baƙuncin Kwantrola Janar na Hukumar Fasa-ƙwauri ta Ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, a Fadarr Gwamnatin Jihar da ke Kano. Gwamna Yusuf ya koka kan yunwar da ake…
Read More
Kin iya kunu?

Kin iya kunu?

Daga AMINA YUSUF ALI Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinku mai albarka na zamantakewa mai zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A makon da ya gabata mun yi batutuwa masu muhimmanci a game da aure da mu'amalar aure. A wannan mako kuma masu karatu mun kawo muku tsaraba daga madafi, musamman ma duba da ƙaratowar qatan azumi. Muna fatan Allah ya raya mu zuwa lokacin. A sha karatu lafiya. Kin iya kunu? Waɗannan kalmomi wasu kalmomi ne da suka yi shuhra a watannin baya a dandalin sada zumunta.…
Read More
SSANU, NASU sun fara yajin aikin gargaɗi

SSANU, NASU sun fara yajin aikin gargaɗi

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Nijeriya (SSANU) da ta NASU sun fara yajin aikin gargaɗi na mako guda don neman a biya su albashinsu na wata huɗu da ya maƙale bayan yajin aikin gama-gari a 2022. Ƙungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniyar shiga yajin aikin ne bayan taron da suka yi a Akure a ƙarshen makon da ya gabata. Yayin da yake karanta wa manema labarai sakamakon taronsu ran Litinin a Abuja, Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, ya ce sun yanke shiga yajin aikin bayan ƙure amfani da hanyoyin da suka dace ba tare da cimma buƙatarsu ba. “Idan Gwamnatin…
Read More
Lawal ya jagoranci taron Majalisar Zatarwa, ya buƙaci mambobi su yi aiki da gaskiya

Lawal ya jagoranci taron Majalisar Zatarwa, ya buƙaci mambobi su yi aiki da gaskiya

Daga BASHIR ISAH A zaman Majalisar Zartarwar jihar da ya jagoranta a ranar Litinin, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi kira ga mambobin majalisar da su yi aiki da gaskiya tare da sauke nauyin da rataya a wuyansu yadda ya kamata. Taron ya gudana ne a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, babban birnin jihar. Sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ta ce majalisar ta tattauna muhimman batutuwa da dama yayin zaman da suka haɗa da ƙudirin ciyar da jihar gaba, kiwon lafiya, batun ilimi, tsaro da sauransu. A cewar sanrwar,…
Read More
Ku yi wa Allah ku tallafa wa talakawan ƙasa, roƙon Tinubu ga su Ɗangote

Ku yi wa Allah ku tallafa wa talakawan ƙasa, roƙon Tinubu ga su Ɗangote

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi hamshaƙan 'yan kasuwar ƙasar, wato Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu da sauran masu ƙumbar susa, da su dubi Allah sannan su taimaka wa marasa galihu musamman a wannan wata na Ramadan. Tinubu ya yi wannan kira ne ranar Lahadi a Kano a wajen ƙaddamar da shinkafar da Santa Abdullahi Yari ya tanada don tallafa wa jama'a don girmamawa ga Shugaba Tinubu. Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa kuma hadiminsa, Abdulaziz Abdulaziz, inda ya yaba da karamcin da sanatan ya nuna masa. Ya ce an ƙaddamar da tallafin ne…
Read More
Dandalin shawara: Na reni ‘ya’ya uku da mijina ya haifa a waje ba tare da sani na ba

Dandalin shawara: Na reni ‘ya’ya uku da mijina ya haifa a waje ba tare da sani na ba

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Barka da safiya malama Aisha. Na san ba ki san ko wacce ce ni ba, sunana…………kuma na samu number ki ta hannun Hajiya…………ƙawata ce, lokacin da na ke mata bayanin halin da nake ciki ne, sai ta ce, ga number na kira ki, ke ce wadda ki ka zo har gida lokacin da matsalarta da……………..ta yi tsanani, ke ki ka taimaka har aka samu mafita. Malama Aisha, mijina ne can baya shekaru da yawa, shi da wani wan babanshi suka shigo da yamma, wan baban nasa ɗauke da jinjiri, suka ce a Masallacin unguwar…
Read More
Domin ku matan aure

Domin ku matan aure

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar al'umma Manhaja, sannunku da jimirin bibiyar mu. Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo ma ku wasu daga ci gaban kayan da za su samar da ni'ima dawamamma ga mace, kuma kayan da ta ke da tabbacin tsafta da lafiyar su, kasancewar ita da kanta ne zata dinga haɗawa. Sai dai kafin nan, zan so in yi amfani da wannan dama in janyo hankalin mata kan illar shan maganin mata da ke bayar da ni'ima ta ɗai rana. Mata ku guji amfani da maganin mata mai bayar…
Read More
Aiwatar da Rahoton Oronsaye zai rage wa gwamnati kashe kuxi – RMAFC

Aiwatar da Rahoton Oronsaye zai rage wa gwamnati kashe kuxi – RMAFC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Tarawa da Raba Kuɗin Shiga (RMAFC), ta yi ƙorafi kan maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da harkokin gwamnati. A baynin da ta fitar a ranar  Lahadi, RMAFC ta ce salon mulki mai tsada da da rashawa da sauransu na daga cikin dalilan da kan  haifar da kashe kuɗi mai yawa wajen gudanar da harkokin gwamnati. Don haka hukumar ta ce, tana da yaqinin kan cewa aiwatar da Rahoton Kwamitin Steve Oronsanye wanda Majalisar Zartarwa amince da shi kwanan nan, zai taimaka matuƙa wajen daidaita tattalin arzikin ƙasa da kuma kyautata rayuwar ’yan ƙasa. Shugaban…
Read More
Ku yi wa ma’aikata ƙarin albashi don ba su walwala, NLC ga Gwamnati

Ku yi wa ma’aikata ƙarin albashi don ba su walwala, NLC ga Gwamnati

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta ce ya zama wajibi gwamnati a dukkanin matakai ta yi ƙarin albashi domin bai wa ma'aikata damar yin rayuwa daidai da halin da ƙasa ke ciki. Shugaban NLC na Ƙasa Joe Ajaero, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da ƙungiyar ma'aikatan lafiya ta shirya a ƙarshen mako a Abuja. A ranar Alhamis da ta gabata NLC ta bayyana N709, 000 don a amince da shi a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a faɗin a ƙasar. A hannu guda, takwararta, TUC kuwa, N447,000 take hari ya zama mafi ƙarcin…
Read More
Jami’an tsaro sun kashe tsegerun IPOB 20, sun dagargaza sansanoninsu

Jami’an tsaro sun kashe tsegerun IPOB 20, sun dagargaza sansanoninsu

Daga BASHIR ISAH Dakarun haɗin gwiwa ƙarƙashin Operation Udoka da ya ƙunshi 'yan sanda, DSS da jami'an tsaron farin kaya na Civil Defence, sun kashe tsegerun IPOB/ESN mutum 20 a wani samamen da suka kai maɓuyar 'yan ta'addan da ke yankin Ƙaramar Hukumar Orsu a Jihar Imo. Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi. Ya ce, “Dakarun sun tada maɓuyar IPOB/ESN kimanin guda 50 a yankin, ciki har da babbar cibiyar 'yan ta'addan." Ya ƙara da cewa, “Jami'an sun kuma tarwatsa maɓuyarsu ta Buteuzor haɗa da…
Read More