Editor

9513 Posts
Ministocin Wajen Sin da Italiya sun zanta game da halin da ake ciki a Ukraine

Ministocin Wajen Sin da Italiya sun zanta game da halin da ake ciki a Ukraine

Daga CMG HAUSA Babban ɗan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya zanta ta kafar bidiyo da takwaransa na Italiya Luigi Di Maio a yau Alhamis, inda suka yi musayar yawu game da halin da ake ciki a ƙasar Ukraine. Wang Yi ya jaddada cewa, batun tsaron Turai na cikin muhimman al’amura, masu nasaba da rikicin Ukraine. Ya ce kamata ya yi ƙasashen Turai su zurfafa shawarwari tsakanin su da Rasha, bisa yarjeniyoyin da aka cimma kawo yanzu, ta yadda hakan zai ba da damar fitar da tsarin tsaron Turai mai nagarta, da tasiri kuma mai…
Read More
Wang Yang ya buƙaci majalisar CPPCC ta bada gudummawar kyautata zaman rayuwar al’umma

Wang Yang ya buƙaci majalisar CPPCC ta bada gudummawar kyautata zaman rayuwar al’umma

Daga CMG HAUSA Shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta ƙasar Sin ta CPPCC Wang Yang, a yau Alhamis ya buƙaci majalisar da ta yi ƙoƙarin cimma muradun al’umma na samun ingantacciyar rayuwa, kana ya bayar da gudummawar kyautata zaman rayuwar al’umma. Wang Yang ya yi wannan tsokaci ne a wajen rufe taro na biyar na majalisasr CPPCC karo na 13. Ya ce ya kamata majalisar CPPCC ta sauke dukkan nauyin al’umma dake bisa wuyanta, inda ya buƙaci majalisar da ta saurari muryoyin al’umma domin share musu hawaye. Ya ƙara da cewa, ya kamata majalisar ta bayar da…
Read More
Tushen Zamfara da Zamfarawa

Tushen Zamfara da Zamfarawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Blueprint Manhaja ta binciko tare da tattaro bayanai daga wuraren daban-daban dangane da asalin Zamfara da Zamfarawa. Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin masarautun asali na Hausawa. Ta kasance ana lissafata ɗaya daga cikin Banza Bakwai waɗanda ba Hausawan asali ne ba. Dalilin hakan shi ne, ana ganin Bare-bari ne asalin Zamfara. Sarkin musulmi Muhammadu yana ganin Zamfarawa sun samu asali ne daga uba Bakatsine da uwa Bagobira. To su Zamfarawa sun kafa asalinsu daga Maguzawa maharba waɗanda sun zauna a yankin ƙasar Kano kafin zuwan Bagauda tun kafin zuwan Barbushe a Dutsen Dala. A nan…
Read More
Asalin ƙabilar Babur

Asalin ƙabilar Babur

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙabilar Babur tana danganta asalinta ne da Mutanen Yamen, don haka aka ruwaito cewa rundunar wasu mutane ne suka ƴi hijira daga ƙasar Yemen a wajajen shekara ta 600 miladiyya suka riski Ƙasar Sudan, sannan suka shigo cikin Sahara tare da sauka a yankin da Ƙabilar Babur ke rayuwa a yanzu cikin ƙasar Borno. Ba iya ƙabilar Babur ba, har ƙabilun Kanuri da Luguda da wasunsu da ke rayuwa a wannan yankin suna iƙirarin asalin kakanninsu daga Yemen suke. Gusawar zamani ne kurum ya sanya takamaimen tarihinsu ya sauya. Zuwa yanzu dai, ana samun ƙabilar Babur…
Read More
Don ƙwato wa mata ‘yanci na zama lauya – Amina Ladan Abubakar

Don ƙwato wa mata ‘yanci na zama lauya – Amina Ladan Abubakar

"Sarautar Magajiya Babba dama ce ta cikar burina" Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Idan a na maganar masu hidimta wa jama'a, to Hajiya Amina Ladan Abubakar ta shiga sahun matan, saboda gudunmawar da ta bayar ga cigaban mata ta fannoni da dama. Da yake alkhairi ba ya tafiya a banza, in da ka yi shi sai ka samu sakamakon sa. Don haka ba abin mamaki ba ne Hajiya Amina Ladan Abubakar ta samu sakamako na girmamawa, saboda Alkhairin da ta shuka. A kwanakin da suka gabata ne dai Mai Martaba Sarkin Tsibirin Gobir da ke Jamhuriyar Nijar ya duba dacewarta…
Read More
Dokar zaɓen Buhari da ta INEC

Dokar zaɓen Buhari da ta INEC

Ta tabbata dai shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan amincewa da dokokin zaɓe kuma kwana kaɗan sai ga wani jadawali na hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta sanya ranaku da lokuttan zaɓe mai zuwa na 2023. Hakan duk wani cigaba ne kuma ko shakka ba bu waccen doka ta zaɓe daga ɓangaren zartarwa da ita kanta hukumar zaɓen alamu ne waɗanda ke nuna zahiri an ɗauki hanyar gyara wacce talakka zai yi zaɓe bisa zaɓin shi. Amma har haka adalci ne mai gyara duk wata doka musamman ta zamantakewa domin duk wata doka da mutane za su zauna…
Read More
Mun horar da masu ruwa da tsaki kan ilimin dabarun kare kai – DPRC

Mun horar da masu ruwa da tsaki kan ilimin dabarun kare kai – DPRC

Daga  MUHAMMAD MUJITABA a Kano Cibiyar Cigaba da Ayyuka na Musamman da Binkice akan Harkar Ilimi (DPRC), sun shirya bita ta musamman ga masu ruwa da tsaki kan ilimin dabarun kare kai daga matsalar tsaro da garkuwa da mutane a makarantu da maaikatu da sauransu, waɗanda suka futo daga jihar Kano da Jigawa kamar yadda jamii mai bada shawara da dabaru a wannan cibiya Sulaiman Muhammad  ya bayyana a wajen wannan bita wanda aka gabatar a Birnin Kanon Dabo a eanar Alhamis ɗin makon jiya. Har ila yau ya ce wannan cibiya tana yin wannan ayyuka na wayar da kai…
Read More
Yadda gasar karatun Alƙur’ani ta gudana a Legas

Yadda gasar karatun Alƙur’ani ta gudana a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Wata ƙungiya mai suna, Lajnatul Musabuƙatul Ƙur'anil Kareem a ƙarƙashin ƙungiyar jama'atul Izalatul bidi'a reshen jihar Legas, ta gudanar da gasar karatun Al-Ƙura'ani Mai tsarki a jihar Legas.  Taron musbaƙar ya gudana ne a unguwar Agege ta jihar Legas. Hakazalika, taron ya samu halartar waɗansu daga cikin Makarantun Islamiyyoyi na cikin garin legas da kewayenta bakiɗaya. Ɗaliban sun kasu kashi-kashi. Akwai waɗanda za su yi gasar karatun izifi sittin, da masu gasar karanta Izifi ashirin, da sauransu.   Maƙasudin taron shi ne, don a ƙara zaburar da ɗaliban a wajen neman ilimin addinin musulunci da Kuma…
Read More
A ƙarshe, APC ta miƙa kujerar shugaban jam’iyya ga Arewa-ta-tsakiya

A ƙarshe, APC ta miƙa kujerar shugaban jam’iyya ga Arewa-ta-tsakiya

*Ta amince da tsarin karɓa-kaarɓa Daga BASHIR ISAH Yayin da lokacin babban taronta na ƙasa ke daɗa ƙaratowa, jam'iyyar APC ta miƙa kujerar shugabancin jam'iyya ga shiyyar Arewa-ta-tsakiya, sannan kujerar Sakataren Jam'iyya na Ƙasa ga shiyyar Kudu-maso-yamma. Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Jam'iyyar, Salihu Na’inna Ɗambatta ya fitar ta nuna shiyyar Kudu-maso-gabas ne zai samar da mataimakin shugaban jam'iyya na ƙasa, yayin da shiyyar Kudu-maso-kudu za ta samar da sakataren yaɗa labarai na ƙasa da sauransu. A halin da ake ciki dai Kwamitin riƙo da shirya babban taron APC (CECPC) ya amince da tsarin karɓa-karɓa dangane da babban taron…
Read More
Yadda gobara ta kaƙume gidan mai a Legas

Yadda gobara ta kaƙume gidan mai a Legas

Daga BASHIR ISAH A ranar Laraba aka samu tashin gobara a gidan man Mobil da ke Alakara, Idi Oro, Mushin a birnin Legas. Bayanai sun nuna gobarar ta tashi ne da tsakar rana daidai lokacin da ake ƙoƙarin sauke fetur da aka kawo wa gidan man. An ce gobarar ta faɗaɗa har zuwa wani bene mai hawa uku da ke kusa da gidan man. A cewar Hukumar Bada Agajin Gaggawa (NEMA), babu wanda ya ji ciwo, haka ma babu hasarar rai sakamakon gobarar. Ya zuwa haɗa wannan labari, an ga jami'an kwana-kwana suna ta ƙoƙarin kashe gobarar a nan gidan…
Read More