Editor

9513 Posts
Gyaran Dokar Zaɓe: Sanatoci sun ƙi amincewa da buƙatar Buhari

Gyaran Dokar Zaɓe: Sanatoci sun ƙi amincewa da buƙatar Buhari

Daga BASHIR ISAH A zamanta na ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da buƙatar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta neman yi wa Sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe kwaskwarima, sashen dokar da ya hana masu riƙe da muƙaman siyasa tsyawa takarar fidda gwani ba tare da sun ajiye muƙaman nasu ba. Bayan da Jagoran Majalisar, Yahaya Abdullahi (APC Kebbi ta Arewa) ya jagoranci muhawarar nazarin dokar a karo na biyu, a nan aka samu da yawa daga cikin sanatocin suka ƙi amincewa da buƙatar bayan da Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan ya gabatar musu da batun don yin ƙuri'a.
Read More
Laifi tudu, Amurka ta taka nata ta hangi wasu

Laifi tudu, Amurka ta taka nata ta hangi wasu

Daga AMINA XU Kwanan baya, majalisar gudanarwa ta ƙasar Sin ta fitar da rahoto game da matsalar kare haƙƙin Bil Adama ta Amurka cikin shekarar 2021, inda aka gabatar da alƙaluma masu ɗimbin yawa dake bayyana yadda yanayin kare haƙƙin bil-Adama a Amurka ke ƙara tsananta. Duk da zanga-zangar da al’ummar Amurka ke yi game da wannan matsala, amma ‘yan siyasar ƙasar sun yi biris da wannan matsala, inda suka mai da hakali wajen tsoma baki cikin harkokin kare haƙƙin Bil Adama na sauran ƙasashe. Lallai, ya kamata ‘yan siyasar Amurka su kalli kansu, su yi watsi da tunanin siyasantar…
Read More
Zama lafiya ya fi zama ɗan sarki

Zama lafiya ya fi zama ɗan sarki

Daga IBRAHIM YAYA Ƙasa ta kan amsa sunanta ne a duniya, ko dai saboda ci gaban da ta samu a fannin tattalin arziki, ko kasuwanci, ko bincike a fannin sararin samaniya ko, fasahar ƙere-ƙere da sauran fannoni. Amma duk da irin wannan ci gaba da ƙasa ta samu, idan har babu zaman lafiya, tamkar ci gaba ne irin na mai hakar rijiya. Ƙasashe irinsu Amurka dake ɗaukar kanta a matsayin ‘yar sandar duniya, ta kan bugi ƙirji a wasu lokuta ta riƙa ayyana kanta a matsayin ƙasar da babu kamar ta a dukkan fannoni a duniya. Sai dai ga mai…
Read More
Gaggauta goge bayanan ɗakin gwaje-gwaje ko me Amurka ke tsoro?

Gaggauta goge bayanan ɗakin gwaje-gwaje ko me Amurka ke tsoro?

Daga CMG HAUSA Ma’aikatar tsaron Rasha, ta ce a baya bayan nan ta gano bayanai game da wani shirin binciken ƙwayoyin halittu na ayyukan soji, wanda ƙasar Amurka ke samar da kuɗaɗen gudanarwa a ƙasar Ukraine, yayin da dakarun Rashan ke kutsawa Ukraine ɗin. To sai dai kuma ya zuwa ƙarshen wata Fabarairun da ya gabata, ofishin jakadancin Amurka a Ukraine, ya gaggauta goge dukkanin bayanai masu nasaba da ɗakin binciken na Amurka daga kan shafin sa na yanar gizo. Ko shakka babu wannan rufa rufa ta sanya tambayar ko me Amurka ke tsoro? Cikin ɗaruruwan ɗakunan gwaje gwajen kwayoyin…
Read More
Sin na goyon bayan tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine

Sin na goyon bayan tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta kafar bidiyo, da shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a jiya Talata, inda ya shaida musu cewa, Sin tana matuƙar damuwa game da ɓarkewar yaƙi a Turai, tana kuma goyon bayan tattaunawar wanzar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ta yadda za a kai ga haye wahalhalu, da cimma sakamako mai amfani. Kazalika shugaban na Sin ya ce yana goyon bayan ƙasashen Faransa da Jamus, a fannin samar da daidaito, da tsari mai inganci na wanzar da tsaron Turai, bisa moriyar nahiyar. Wannan ganawar…
Read More
Gwamnatin Kano za ta sake fasalin hukumomin Zakka da Hubsi

Gwamnatin Kano za ta sake fasalin hukumomin Zakka da Hubsi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da sake fasalin hukumar Zakka da Hubsi ta jihar Kano, inda ta bayyana Dr. Ibrahim Mu’azzam Mai-Bushira a matsayin Shugaban Zartarwa. Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talatar makon jiya, a ƙarshen taron majalisar da aka gudanar a ɗakin taro na Africa House dake fadar gwamnatin Kano. A cewar sanarwar mambobin sun haɗa da Dr. Abdulmutallab Ahmed a matsayin kwamishina na ɗaya, Dr. Lawi Sheikh Atiq kwamishina na biyu na hukumar. Garba ya kuma lissafa…
Read More
Ƙungiya ta nuna qin amincewa da ƙudirin majalisa na gabatar da kadarorin iyalan ma’aikatan banki

Ƙungiya ta nuna qin amincewa da ƙudirin majalisa na gabatar da kadarorin iyalan ma’aikatan banki

Daga AMINA YUSUF ALI Wani sabon ƙuduri da 'yan majalisa suka shigar a  kan ma'aikatan banki a Nijeriya na sanya dokar dukkan ma'aikatan Banki su bayyana kadarorinsu da na mata ko mijinsu da kuma na 'ya'yansu. Ƙungiyar akawu (Ma'aikatan banki) ta Nijeriya ita kuma a nata ɓangaren, ta bayyana tsananin ƙin jininta a kan wannan sabuwar doka da ake son tabbatarwa a Nijeriya. Wacce ta tilasta wa duk wani ma'aikacin/ma'aikaciyar banki su gabatar da dukkan kadarorin da iyalansu suka mallaka.  Kuma a halin da ake ciki har hukumar nan ta yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin…
Read More
Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda da ya gurfanar da Abba Kyari, Joseph Egbunike, ya riga mu gidan gaskiya

Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda da ya gurfanar da Abba Kyari, Joseph Egbunike, ya riga mu gidan gaskiya

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Sufeto-Janar na 'Yan Sanda kuma shugaban sashen binciken manyan laifuka na Rundunar 'Yan Sanda ta Ƙasa (FCID), Joseph Egbunike ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda jaridar SaharaReporters ta ruwaito. Bayanai sun nuna Egbunike ya yanke jiki ne ya faɗi a cikin ofishinsa da ke Abuja a jiya Talata wanda daga nan kuma rai ya yi halinsa. Kafin mutuwarsa, Egbunike shi ne mai kula da sashen bincike mafi girma na rundunar 'yan sandan Nijeriya. Aikin sashen da marigayin ya riƙe ya haɗa da binciken manyan laifuffuka da gurfanar da masu aikata mayan laifuka a ciki da…
Read More
Zaɓar mace ko namijin aure (I)

Zaɓar mace ko namijin aure (I)

Assalam. Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan wasiƙa zuwa ga ’yan uwana matasa a wannan jarida mai albarka ta Blueprint Manhaja. A Musulunci an yi umarni ne da a yi aure ba domin biyan buƙata ta duniya ko ta sha'awa ba kawai, akwai buƙata ta gina al'umma saliha da za ta ci gaba da ɗaukar nauyin isar da saƙon Allah a duk faɗin Duniya, wanda wannan yana buƙatar taimakekeniya tsakanin ma'aurata, sa'annan akwai samun nutsuwa ta ruhi da ɗan Adam yana buqatarsa wanda an sanya shi ne ya zamanto ta hanyar zamantakewa tsakanin miji da…
Read More
PDP ta maye gurbin Gwamna Umahi da Igariwey

PDP ta maye gurbin Gwamna Umahi da Igariwey

Daga BASHIR ISAH Biyo bayan hukuncin tsige gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi da mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe da Babbar Kotun Abuja ta yi a jiya Talata, jam'iyyar PDP ta bayyana sunayen Hon. Iduma Igariwey da Fred Udeogu don maye gurbinsu. Shugaban PDP na ƙasa, Sanata Dr Iyorchia Ayu, ya ce jam'iyyar ta miƙa sunayen waɗanda ta zaɓo ɗin ne don maye gurbin tsigaggun ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC). Ayu ya bayyana hakan ne ga manema labarai ran Talata a Abuja. Kotu ta tsige Gwamna David Umahi tare da mataimakinsa, Dr Eric Kelechi Igwe bisa dalilin sauya sheƙa da…
Read More