Editor

9513 Posts
Ƙungiyar ɗaliban Zamfara ta ƙaddamar da sabbin shugabanni

Ƙungiyar ɗaliban Zamfara ta ƙaddamar da sabbin shugabanni

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa reshen jihar Zamfara (NUNSZAM) ta zaɓi sabon shugabanta. Sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa a jihar, Muhammad Bashir Kanto a jawabinsa na karɓar takardar shaidar cin zaɓe, ya yi alƙawarin ɗaukar kowa da kowa. Bashir Kanto ya ci gaba da cewa, haɗin kai da ci gaba a tsakanin mambobin ƙungiyar a matsayin mafi muhimmanci, yana mai jaddada cewa duk bambance-bambancen cikin gida da ke tsakanin mambobin ƙungiyar za a magance su a ƙarƙashin kulawar sa. "Za mu tabbatar da cewa an yi amfani da kowane mamba tare da magance bambance-bambancen siyasar mu…
Read More
Rikicin APC ya ci kujerar Sakataren Jam’iyya na Ƙasa, Akpanudoedehe

Rikicin APC ya ci kujerar Sakataren Jam’iyya na Ƙasa, Akpanudoedehe

Daga BASHIR ISAH Da alama dai wutar rikicin da ta kunnu a cikin jam'iyyar APC mai mulki na ci gaba da ruruwa kamar wutar daji, lamarin da har ya kai ga sakataren APC na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya ajiye muƙaminsa. Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna cewa, Akpanudoedehe ya miƙa takardar ajiye muƙaminsa ne ga muƙaddashin shugaban riƙo na APC, Gwamna Abubakar Sani Bello yayin wani mitin da kwamitin riƙon ya saba gudanarwa a babbar sakatariyar jam'iyya a Abuja. A ci gaba da bibiyar Blueprint Manhaja cikakken bayani na nan tafe.
Read More
Kotu ta tsige gwamnan Ebonyi da mataimakinsa don sun sauya sheƙa zuwa APC

Kotu ta tsige gwamnan Ebonyi da mataimakinsa don sun sauya sheƙa zuwa APC

Daga BASHIR ISAH A wannan Talatar Babbar Kotu mai zamanta a Abuja ta tsige gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi tare da mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe biyo bayan sauya sheƙa da suka yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Kotun ƙarƙashin Alƙali Inyang Ekwo ta ce, ƙuri'u 393,042 da Gwamna Umahi ya samu yayin zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a 2019 a jihar Ebonyi, mallakar PDP ne wanda ba zai yiwu a juya su ga APC ba. Don haka kotun ta ce tun da su biyun sun sauya sheƙa zuwa APC, hakan na nufin sun…
Read More
Zhao Lijian: Ya kamata a binciki ayyukan sojin Amurka masu nasaba da gwaje-gwajen ƙwayoyin halittu

Zhao Lijian: Ya kamata a binciki ayyukan sojin Amurka masu nasaba da gwaje-gwajen ƙwayoyin halittu

Dag CRI HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ce kamata ya yi a binciki ayyukan sojin Amurka, masu nasaba da makamai masu guba a gida da waje, domin sassan ƙasa da ƙasa su tantance abubuwan da Amurkan ke aiwatarwa. Zhao na wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da cibiyar gwaje gwajen ƙwayoyin halittu ta Amurka dake ƙasar Ukraine. Zhao Lijian, ya ce cibiyar gwaje gwajen mai nasaba da ayyukan soji ta Amurka dake Ukraine, ɗan ƙaramin ɓangare ne kawai na makamantan ta…
Read More
Ƙasar Sin na ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya tsaro a duniya

Ƙasar Sin na ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya tsaro a duniya

Daga CRI HAUSA Wani rahoton aiki da kotun kolin jama'a ta ƙasar Sin (SPC) ta fitar Talatar nan, na nuna cewa, ƙasar Sin na daya daga cikin ƙasashen da suka fi zaman lafiya a duniya. Rahoton wanda aka miƙa wa majalisar wakilan jama’ar ƙasar Sin domin tattaunwa, ya bayyana cewa, adadin manyan laifuffuka iri-iri guda takwas, kamar kisan kai, da fyaɗe da kuma satar mutane, ya ragu matuka, yayin yawan irin waɗannan laifuffuka da ke cikin laifuffuka duka shi ma ya ragu sosai A cewar rahoton kotun kolin, ƙasar Sin ta sanya hukunci mai tsauri kan laifuffukan da suka shafi…
Read More
Xi Jinping ya zanta da shugabannin Faransa da Jamus

Xi Jinping ya zanta da shugabannin Faransa da Jamus

Daga CRI HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta kafar bidiyo da shugaba Emmanuel Macron na faransa, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da yammacin Talatar nan, inda suka maida hankali ga tattauna yanayin da ake ciki a ƙasar Ukraine. Yayin zantawar ta su, shugaba Macron da Mr. Scholz, sun gode wa gudummawar ƙasar Sin, don gane da tallafa wa manufar samar da agajin jin kai, sun kuma bayyana aniyar su ta ƙarfafa sadarwa, da tsare tsare tare da ɓangaren Sin, domin ingiza wanzar da zaman lafiya, da goyon bayan tattaunawa. A nasa ɓangaren, Xi Jinping ya jaddada…
Read More
Ministan Harkokin Wajen Sin ya tattauna ta wayar tarho da babban jami’in EU

Ministan Harkokin Wajen Sin ya tattauna ta wayar tarho da babban jami’in EU

CRI HAUSA Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, jiya Litinin ya tattauna ta wayar tarho da Josep Borrell, babban wakilin ƙungiyar Tarayyar Turai mai kula da harkokin ƙasashen waje da manufofin tsaro. A yayin tattaunawar tasu, Borrell ya bayyana ra'ayi da matsayin ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), kan halin da ake ciki a ƙasar Ukraine, inda ya ce, abu mafi muhimmanci a halin yanzu, shi ne tsagaita buɗe wuta tare da kauce wa hasarar rayuka. Yana mai cewa, EU na goyon bayan warware matsalar ta hanyar yin shawarwari. A nasa ɓangare kuwa, Wang Yi ya…
Read More
Kunya adon ‘ya mace: Ya abin ya ke a zamanin nan?

Kunya adon ‘ya mace: Ya abin ya ke a zamanin nan?

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Da fatan na same ku lafiya. Da farko yau zan fara miqa godiyata ga dukkan masu yaba mun da nuna jin daɗinsu yadda suke gamsuwa da wannan fili namu mai albarka. Muna godiya kuma muna jinjina wa masu bin mu sau da ƙafa.Yau za mu tavo yadda rayuwar yaranmu mata take son canja salo daga kunya zuwa fitsara. A da ɗiya mace da kunya aka san ta ba a san ta da buɗe baki ba, duk matsi ta ce saurayi yayi mata kaya, ko ya ba ta kuɗi ba. Subuhanallahi! ta yaya iyaye za su bar…
Read More
Mutane biyar sun mutu sanadiyyar ruftawar ƙasa a Kano

Mutane biyar sun mutu sanadiyyar ruftawar ƙasa a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Aƙalla mutane biyar ne su ka mutu a yayin da ƙasa ta rufta musu lokacin da su ke haƙar ta don yin gini. Mutane biyar ɗin mazauna ƙauyen Ƴanlami a ƙaramar hukumar Bichi sun gamu da ajalinsu a a ranar Asabar da ta gabata. Mutanen da su ka mutu sun haɗa da Muhammad Sulaiman mai shekaru 35, da Jibril Musa mai shekaru 30, sai Masa’udu Nasiru mai shekaru 25 sannan Jafaru Abdulwahab mai shekaru 30 sai kuma Alasan Abdulhamid mai shekaru 22 a duniya. Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar…
Read More
Jamhuriyar Benin za ta cigaba da tsare Igboho a asibiti

Jamhuriyar Benin za ta cigaba da tsare Igboho a asibiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan gwagwarmayar ƙabilar Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho Oosha, ya sake samun ’yancinsa bayan da hukumomin jamhuriyar Benin suka sake shi, bayan ya shafe kimanin watanni takwas a gidan yari. Babban Lauyan Igboho, Cif Yomi Alliyu SAN, ya tabbatar da hakan a ranar Litinin da yamma. Alliyu ya bayyana a cikin saƙon cewa Sunday Igboho ya sake samun ’yancin ne amma da sharaɗi zama a asibiti domin a kula da lafiyarsa a cikin Cotonou. Ya kuma bayyana cewa, sakin Igboho na cikin yarjejeniyar cewa kada ya bar cibiyar kiwon lafiya ko…
Read More