07
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Har izuwa yanzu Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja bai tabbatar da karɓar ragamar shugabancin jam’iyyar APC na riƙon ƙwarya da tsare-tsare na musamman (CECPC) ba duk da cewa ya jagoranci wani taro a sakatariyar ƙasa a safiyar Litinin. Bello wanda ya zanta da manema labarai jim kaɗan bayan ya jagoranci taron APC a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin, ya ba da amsoshin tambayoyi masu ruɗani. Ya ce, “a taron, shugabannin jihohin sun yi rantsuwa a yau, kuma mun tattauna ci gaban da aka samu kan yarjejeniyar da kuma abin da…
