Editor

9513 Posts
Yaushe malaman jami’a za su daina yajin aiki a Nijeriya?

Yaushe malaman jami’a za su daina yajin aiki a Nijeriya?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wani al'amari da ke ci wa ’yan Nijeriya tuwo a ƙwarya, musamman iyaye da ɗaliban manyan makarantu shi ne yajin aikin ƙungiyar malaman jami'o'i ta ASUU, wanda ya qi ci ya ƙi cinyewa. Duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnati ta ce tana yi, na biyan wasu buƙatun ƙungiyar da ɗaukar matakai kan wasu matsalolin da ƙungiyar malaman take ƙorafi a kansu.  Yawan yaje yajen aiki da ƙungiyar malamai ta ASUU take tafiya kusan a kowacce shekara, ya fara ƙure iyayen yara da ƙungiyoyin ɗalibai, waɗanda ke zargin sakacin gwamnati da nuna halin ko-in-kula da ƙungiyar ASUU…
Read More
Ministan Ƙwadago ya bada tabbacin samun daidaito tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU

Ministan Ƙwadago ya bada tabbacin samun daidaito tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi a Nijeriya, Mista Chris Ngige ya na sa ran ƙungiyar ASUU ba za ta shafe tsawon wata guda tana yajin aiki ba. Dr. Chris Ngige yi wannan bayanin ne ga manema labarai bayan ya tashi daga wani taro da ya yi da shugabannin ASUU a Abuja. Dr. Chris Ngige ya ce sun cin ma matsaya a kan wasu abubuwa da dama, kuma an tsaida lokacin da za a aiwatar da alƙawuran da gwamnati ta yi wa ƙungiyar. A cewar ministan, wakilan ASUU sun yarda su tuntuɓi ‘ya‘yansu…
Read More
Ɗangote ya zarce mamallakin Chelsea a arziki

Ɗangote ya zarce mamallakin Chelsea a arziki

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai, mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Ɗangote, ya sake shillawa sama a cikin jerin sunayen mutanen da suka fi kowa arziki a Duniya. Domin kuwa rahotanni sun bayyana cewa, a yanzu haka ma sunan Ɗangote yana saman sunan Biloniyan attajirin nan na ƙasar Rasha, Roman Abramovich. Kuma mamallakin kamfanin ƙwallon ƙafa na Chelsea. Jaridar Bloomberg ta rawaito cewa, a  yanzu haka ƙarfin arzikin attajirin kuma biloniya, Aliko Dangote ya ƙara haɓaka da ƙarin, Dalar Amurka $934 abinda ya kai shi ga zama mutum na 83 ma fi arziki a…
Read More
Yajin aikin ASUU: Zaman sasantawa ya tunzura ministan ilimi

Yajin aikin ASUU: Zaman sasantawa ya tunzura ministan ilimi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Ministan Ilimi na Ƙasa, Mallam Adamu Adamu a ranar Litinin ce da ta gabata ya nuna tuzurin fushi, tare da fita daga ɗakin taron sasantawa tare da wakilan ɗaliban ƙasar nan (NANS) waɗanda suke yin bore bisa yawan shiga yajin aiki da ƙungiyar jami’o’in ƙasar nan (ASUU) suke yi. Ministan dai, ya shirya wani taro ne na ba-za-ta da shugabannin ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS), waɗanda suka yi cincirindo a mashigar ma’aikatar Ilimi ta tarayya (FME) da ke Abuja a ranar Linitin da ta gabata. Ɗaliban na ƙasa, sun nemi ministan ne da ya rufe…
Read More
Yadda gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ke cigaba da kankama a majalisa

Yadda gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ke cigaba da kankama a majalisa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Dattawan Nijeriya ta kaɗa ƙuri’a kan wasu sassa sittin da takwas na kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 da suka ƙi amincewa da ƙirƙirar wa mata kujera na musamman. “Ƙudirin ya nemi a samar da muƙamai na musamman ga mata a Majalisar Dattawa, Wakilai da Majalisar Jiha ta hanyar samar da kujeru guda na musamman a kowace jiha ta tarayya da kuma Babban Birnin Tarayya da aka keɓe wa mata kaɗai ba tare da la’akari da cancantarsu ta tsayawa takara ta kujerun sanatoci a kowace jiha da Abuja…
Read More
Hajjin 2022: Saudiyya ta buɗe ƙofa ga maniyyata daga sassan duniya

Hajjin 2022: Saudiyya ta buɗe ƙofa ga maniyyata daga sassan duniya

Daga BASHIR ISAH Bayan shekaru biyu a jere da hana 'yan ƙetare zuwa aikin Hajji da Umarah a Saudiyya da gwamnatin ƙasar ta yi a matsayin wani mataki na yaƙi da annobar korona, yanzu dai Masarautar Saudiyya ta bada sanarwar cewa za ta buɗe ƙofofin masallatan Makka da Madina ga mahajjata daga sassan duniya don aikin Hajji da Umara na shekarar 2022. Tun farko, Saudiyya ta sanar a ranar Asabar da ta gabata cewa ta ɗage dokar nan ta bada tazara a tsakanin juna a cikin masallacin Harami da Madina. Cikin wani taƙaitaccen jawabi da ya gabatar, Imam Sheikh Abdullah…
Read More
Filayen gasar Olympics na lokacin sanyi za su ingiza cigaban wasannin ƙankara na Sin

Filayen gasar Olympics na lokacin sanyi za su ingiza cigaban wasannin ƙankara na Sin

Daga CRI HAUSA A ranar 4 ga wata, an ƙaddamar da gasar Olympics ta lokacin sanyi da kuma taro karo na 5 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar Sin ta 13 a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar, wasu mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta ƙasar waɗanda ke halartar taron sun bayyana cewa, Beijing ne birni na farko a faɗin duniya, wanda ya shirya gasar Olympics na lokacin zafi da na lokacin sanyi, don haka an gina wasu filayen wasa da ɗakunan wasa da dama a birnin, duk waɗannan za su taka rawa kan…
Read More
Kafofin watsa labaran ƙasa da ƙasa: Taruka biyu na Sin na da babbar ma’ana ga zamantakewar al’ummun duniya

Kafofin watsa labaran ƙasa da ƙasa: Taruka biyu na Sin na da babbar ma’ana ga zamantakewar al’ummun duniya

Da CRI HAUSA Kamfanin watsa labarai na ƙasar Kenya wato KBC, ya gabatar da wani sharhi dake cewa, taruka biyu na ƙasar Sin waɗanda ke gudana a birnin Beijing na ƙasar suna jawo hankalin al’ummun ƙasashen duniya matuƙa, musamman ma batun dake shafar shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya, saboda shawarar tana amfanar dukka duniya, har ma tana taka muhimmiyar rawa wajen cuɗanyar tattalin arzikin duniya. Sharhin ya ƙara cewa, ƙasar Sin abokiyar cinikayya mafi girma ta ƙasashen Afirka ce, wadda ke zuba jari mafi yawa a nahiyar, musamman ma a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, ƙasashen Afirka suna…
Read More
Ministan Harkokin Wajen Sin ya tattauna ta wayar tarho da Sakataren Harkokin Wajen Amurka game da hulɗar ƙasashen biyu da kuma batun Ukraine

Ministan Harkokin Wajen Sin ya tattauna ta wayar tarho da Sakataren Harkokin Wajen Amurka game da hulɗar ƙasashen biyu da kuma batun Ukraine

Daga CRI HAUSA Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar, Wang Yi, a ranar Asabar ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, game da hulɗar dake tsakanin Sin da Amurka da kuma batutuwan dake shafar Ukraine bisa gayyatar da Blinken ya yi masa. Wang ya ce a halin yanzu, babban abinda hulɗar dake tsakanin Sin da Amurka za ta fi mayar da hankali shine, batun daga matsayi da kuma aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma matsaya kansu a taron da suka gudanar ta kafar bidiyo, ya ƙara da cewa,…
Read More
MOPPAN da NFVCB za su gudanar da taron yini biyu a Kano

MOPPAN da NFVCB za su gudanar da taron yini biyu a Kano

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar masu shirya fina-finai MOPPAN a taƙaice ta ce, ta shirya gudanar da taron yini biyu ga masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai don bunƙasa harkar. Sanarwar manema labarai da MOPPAN ta fitar ta hannun jami'inta na hulɗa da jama'a na ƙasa, Al-Amin Ciroma, ta nuna taron na haɗin gwiwa ne tsakanin MOPPAN da Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa (NFVCB). Sanarwar ta ce taron na yini biyu ne kuma zai gudana ne a ranakun 9 da 10 ga Maris, 2022 a birnin Kano. Taron wanda zai maida hankalin wajen tattauna harkar fina-finai a soshiyal midiya,…
Read More