06
Mar
06
Mar
Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Yayin da shirye-shiryen zaɓen shekara ta 2023 suka fara kankama, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Asabar da ta gabata ya ziyarci ubangidansa, tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da kuma fitaccen basarake na ƙasar Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo. Atiku, wanda ya isa gidan Olusegun Obasanjo da misalin ƙarfe 10 na safiyar wancan rana, sun yi ganawar ta sirri na kimanin awa guda. Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan ganawar tasu, Atiku ya ce, "na zo ganin ubangidana ne" amma bai ce komai akan lamarin da suka tattauna ba a lokacin…
06
Mar
Daga AMINA YUSUF ALI Tambayar wai me maza suke so wajen mata? Wannan tambaya ce mai cike da sarqaqiya wacce da wuya ta iya amsuwa kai tsaye. Domin yadda mata suka banbanta a ra'ayi, haka mazan ma suka banbanta domin banbancin 'yan adamtaka. Kodayake, dukkan maza sukan haɗu a kan wasu abubuwa da ake ganin kowannensu yana buƙata daga mace. Mata sun sha yin kuskuren namiji yana buƙatar kyawu ko surar halittar mace ne fiye da komai. Shi ya sa suka fi mayar da hankali wajen yi wa kansu kwaskwarima da gyara domin samun waccan soyayyar ta ɗa namiji. Sai…
06
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Duk da tabbacin da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya bayar na cewa za a kawo ƙarshen ƙarancin man fetur a ƙarshen watan Fabrairu, amma har yanzu ’yan Nijeriya na fuskantar wahalar samun man. Shugaban kamfanin mai na NNPC Mele Kyari, ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin man fetur a ranar 16 ga watan Fabrairu, inda ya bada tabbacin kawo ƙarshen ƙarancin man nan da mako guda. Ya shaida wa kwamitin cewa tuni kamfanin ya karɓi lita biliyan 2.1 da za a raba domin daidaita al’amura. Ƙaranci yana ƙara muni:Duk…
06
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Masarautar Saudiyya ta ɗage dakatar da zirga-zirgar jiragen saman Nijeriya a ƙasarta watanni uku bayan da ta sanya dokar hana fita sakamakon ɓullar cutar Korona. Sanarwar da ta ɗage haramcin an ba da ta ne a ranar Asabar inda Masarautar ta kuma cire takunkumin annobar Korona da yawa ta yadda za ta ba da damar aikin Hajji na 2022. A cewar sanarwar da aka gani a shafin Twitter na Saudi Gazette, Masarautar ta kuma ɗage dakatar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye da shigowa daga wasu ƙasashe 17. Waɗannan sun haɗa da Afirka ta Kudu, Namibiya,…
06
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga shekarar 2023, gwamnatin tarayya, a ƙarƙashin zaɓaɓɓun shugabannin ƙasa bakwai da za a yi a gaba, za ta ɗauki sama da shekaru 24 tana biyan bashin dala biliyan 3,593.42 da Nijeriya ta ciwo daga bankin Exim na ƙasar Sin a halin yanzu. Sai dai kuma, hakan zai yiwu ne kawai idan har Nijeriya ba ta sake karɓar wani lamuni daga ƙasashen Asiya ba kafin ƙarshen wa'adin mulkin wannan gwamnati da kuma wasu na gabanta. Fwamnatoci biyar da za a yi: Gwamnatocin da za su fara mulki daga 2023, 2027, 2031, 2035, 2039, 2043, da kuma…
06
Mar
Daga UMAR GARBA a Katsina Za a sake ba wa al'ummar Jihar Katsina damar yin rajistar gaggawa ta tatallafin annobar cutar Korona wato 'Rapid Response Register" a turance musamman ga mutanen da ba su samu damar yi ba tun da farko, inda za a fara rajistar ranar Litanin 7 ga Maris, 2022. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ofishin kula da rajistar mutane marasa ƙarfi na jihar wato SOCU, Marwana Abubakar Darma, ya fitar a madadin babban jami’in shirin a Jihar Katsina, Aliyu Isa Girka. Sanarwa ta bayyana cewa, mutanen da ke da…
06
Mar
DAGA MUHAMMADU MUJITABA Shugaban Ƙungiyar Malaman Sakandire ta Ƙasa reshen Jihar Kano (ASUSS), Kwamared Abdu Usman Yalo ya ce su malaman sakandire na Jihar Kano ba su da matsalar biyan albashi daga gwamnatin Kano ko matsalar rashin ƙarin girma, ya ce duk wata ana biyan su albashi tun tsohuwar gwamnati har zuwa gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ba su da matsalar rashin biyan albashi kamar yadda wasu jihohin ƙasar nan ke fuskantar matsala. Usman ya ƙara da cewa "ƙarin girma shi ma ba mu da matsala ana yi kamar yadda ya ke a ƙa`ida sau biyu a shekara, ana mana…
06
Mar
*Ministan Shari’a da Hukumar NDLEA sun garzaya kotu rana ɗaya*Me zai faru idan kotu ta amince da buƙatun ɓangarorin biyu? Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Daga dukkan alamu tsugunne ba ta ƙare wa fitaccen ɗan sandan Nijeriya nan, DCP Abba Kyari ba, inda a cikin makon nan mai ƙarewa gwamnatocin Nijeriya da Amurka ke cigaba da yi masa tara-tara a gaban kuyliya, don hukunta shi sakamakon zarge-zargen da suke yi masa masu alaqa da damfara da kuma laifin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, lamarin da ya sanya Hukumar FBI ta Amurka ke neman Kyari ruwa a jallo har ma ta…
05
Mar
Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin sadarwa na yanar gizo na Fesbuk wanda a yanzu ya rikiɗe ya koma Meta ya haramta wa ƙasar Rasha tallata kasuwanci a shafukansa. Wato dai dukkan kafafen yaɗa labarai mallakin ƙasar, kamfanin ya hana su tallata komai a dandalin na sada zumunta (Fesbuk). A yanzu haka ma dai Kamfanin na Fesbuk wanda aka fi sani da Meta ya dakatar shafukan wasu manyan kafofin yaɗa labarai mallakin ƙasar ta Rasha guda huɗu. Wannan jawabi na haramci ga ƙasar Rasha ya fito ne daga shafin Tiwita na shugaban sashen tsaro na kamfanin Meta (Fesbuk), Nathaniel Gleicher. Inda…
