Editor

9513 Posts
Hana mata muƙaman gwamnati koma-baya ne ga siyasar Nijeriya – Ibrahim Haruna

Hana mata muƙaman gwamnati koma-baya ne ga siyasar Nijeriya – Ibrahim Haruna

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Wani matashin ɗan siyasa a jihar Gombe kuma mai kishin ganin an bai wa mata wannan kaso na 35 cikin ɗari da suke hanƙoron nema a muƙaman gwamnati daban-daban da na siyasa, Alhaji Ibrahim Haruna Tukulma, shugaban ƙungiyar nan da ba ta gwamnati ba ta Arewar mu duniyar mu, ya ce hana su matsayin zai mayar da siyasar Nijeriya baya. Alhaji Ibrahim Haruna wanda har ila yau shi ne Sarkin Hausawan Tukulma, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a Gombe, inda ya ce mata ba ƙashin yasarwa ba…
Read More
Pakistan ga Turai: Mu ba bayinku ba ne da za ku ce sai mun yi tir da Rasha

Pakistan ga Turai: Mu ba bayinku ba ne da za ku ce sai mun yi tir da Rasha

Firaministan Ƙasar Pakistan, Imran Khan, ya yi allawadai da umarnin da da ƙasashen Yamacin Duniya (Turai da Amurka da sauransu) suke yi wa ƙasar Pakistan da su fito su yi tofin Allah tsine ga ƙasar Rasha saboda saɓaninta da ƙasar Yukiren. Inda Imran Khan ya mayar wa Gamayyar ƙasashen Turai (EU) martani cewa, ko tana tsammanin cewa, Pakistan baiwarta ce, da take ba ta umarni ta yanke hulɗa da ƙasar Rasha saboda rikicinta da Yukiren? A cikin wani rubutaccen saƙo na haɗin gwiwa da Ƙasashen Yammacin Duniya suka aike wa da Ƙasar Pakistan a farkon watan nan na Maris 2022,…
Read More
Za mu koma Ukraine idan yaƙi ya lafa

Za mu koma Ukraine idan yaƙi ya lafa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Mamaye Ukraine da Rasha ta yi ba wani sabon labari ba ne a ’yan kwanakin nan. Kazalika, batun ƙasashe na jigilar jama’arsu da ke Ukraine shi ma labari ne da duk mai bibiyar labaru ya san an yi haka ko a na cigaba da yin hakan. Abin takaicin shi ne yadda ’yan Afirka ko a ce baƙaƙen fata su ka fuskanci ƙalaubalen nuna mu su wariya wajen isa tudun mun tsira daga tsakiyar inda a ke fargabar saukar makamai masu linzami zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da Ukraine. Wasu daga ɗaliban Nijeriya sun ba da tabbacin…
Read More
Komai da ruwanka: Yadda na ke tauna taura biyu a Kannywood da Nollywood – Usman Uzee

Komai da ruwanka: Yadda na ke tauna taura biyu a Kannywood da Nollywood – Usman Uzee

Daga AMINA YUSUF ALI Hausawa dai kan ce, wai taura biyu ba ta taunuwa lokaci guda a cikin baki. To, amma ba haka ba ne ga Jarumi furodusa wanda ya ke taka rawa a fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da kuma takwararta ta Kudancin Nijeriya, wato, Nollywood. Usman Uzee ɗan asalin Jihar Kwara ne, amma girman Jihar Kaduna ne. Ya yi digirinsa kala biyu a ɓangaren fannin siyasa da kuma harshen Ingilishi a jami'o'in Abuja da kuma Jos. Sannan ya cigaba da karatunsa a Afirka ta Kudu. Ya shiga harkar fim a shekarar 2003 a matsayin mai kwalliya. Usman ya…
Read More
Mawaƙi Salisu Mariri zai angonce yau Juma’a

Mawaƙi Salisu Mariri zai angonce yau Juma’a

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Idan Allah ya kaimu ƙarfe 2:30 na wannan rana ta Juma'a, za a ɗaura auren mawaƙi, jarumi kuma furodusa a masana'antar Kannywwod, Salisu Nuhu Mariri, tare da amaryarsa, Maryam Muhammad, a unguwar Rigasa da ke garin Kaduna. Kamar yadda katin gayyatar auren ya sanar, matashin jarumin yana gayyatar 'yan uwa da abokai da kuma dukkan masoyansa zuwa wajen wannan ɗaurin auren, kuma ga duk wanda bai samu damar zuwa ba, sai ya taya su da addu'ar Allah ya ba su zaman lafiya. Shi dai Salisu Nuhu Mariri, yana cikin mawaƙan harkar fim sama da shekaru…
Read More
MOPPAN ta shirya taron wayar da kai kan amfanin soshiyal midiya

MOPPAN ta shirya taron wayar da kai kan amfanin soshiyal midiya

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato Motion Picture Practitioners Associations of Nigeria, tare da haɗin gwiwar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, sun shirya taron wayar da kan masu sana’ar ta shirin fim a kan yin amfani da soshiyal midiya ga ’yan Masana'antar Kannywwod. Taron na wuni guda, wanda aka gudanar da shi a ranar Alhamis, 10 ga Maris, 2022, a ɗakin taro na Kannywwod TV da ke titin Muhammadu Buhari a Birnin Kano, ya samu halartar masu gudanar da harkar fim da suke dukkan jihohi na Arewacin Nijeriya da ma…
Read More
Tabbatar da yanke hukunci don daƙile cin hanci da rashawa a Nijeriya

Tabbatar da yanke hukunci don daƙile cin hanci da rashawa a Nijeriya

Hukuncin da aka yanke wa tsohuwar ministar albarkatun ruwa, Sarah Reng Ochekpe, tare da wasu mutane biyu a baya-bayan nan, wani muhimmin cigaba ne a yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya. Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta kama su ne a ranar 22 ga watan Fabrairun 2022 a kan tuhume-tuhumen da ake yi masu. Sauran mutane biyun da aka yankewa hukuncin sune Evan Leo Sunday Jitong da Raymond Dabo, waɗanda suka kasance mataimakin darakta a yaƙin neman zaɓen Goodluck/Sambo 2015 da kuma tsohon shugaban riƙo na jam’iyyar PDP a jihar…
Read More
Ƙasar Sin ta ciri tuta a fannin kyautata rayuwar masu buƙata ta musamman

Ƙasar Sin ta ciri tuta a fannin kyautata rayuwar masu buƙata ta musamman

Daga SAMINU ALHASSAN Ko shakka babu, mutane masu buƙata ta musamman dake zaune cikin al’ummun duniya, muhimmin bangare ne na jama’ar dake matuƙar buƙatar kulawa, da lura da agaji, kasancewar su mutane da ba za su iya yin wasu abubuwa na buƙatun rayuwa da kan su ba. Lura da haka ne ya sa hukumomi a matakai daban daban, ke yin kiraye kiraye ga masu ruwa da tsaki, don gane da buƙatar kara lura da buƙatun masu nakasa. Bisa hakan ya sa a nan ƙasar Sin, mahukuntan ƙasar ke gudanar da manufofi daki daki, na shawo kan matsaloli da wannan rukuni…
Read More
An samu haɗarin tankar mai a Legas

An samu haɗarin tankar mai a Legas

Daga WAKILINMU Haɗarin ya auku ne a ranar Alhamis a yankin Cocin MFM da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan. Bayanai sun tabbatar cewa an samu hasarar rayuka sakamakon haɗarin wanda ba a kai ga tantance adadinsu ba. Ko a Larabar da ta gaba an samun makamancin wannan haɗarin a Legas inda gobara ta tashi ta laƙume wani gidan mai a daidai lokacin da ake sauke mai daga tankar mai.
Read More
Lokaci ya yi da Turai za ta fice daga tarkon Amurka!

Lokaci ya yi da Turai za ta fice daga tarkon Amurka!

Daga CMG HAUSA A jiya Laraba bisa agogon Amurka, majalissar wakilan ƙasar ta kaɗa ƙuri’u, na hana shigar da ɗanyen mai da iskar gas da kwal na ƙasar Rasha cikin Amurka. Ya zuwa yanzu, wannan shi ne mataki mafi tsauri da Amurka ta ɗauka cikin jerin takunkumai kan Rasha. To sai dai kuma, al’ummun nahiyar Turai na kallon matakin a matsayin takunkumi kan Turai maimakon Rasha! Ko shakka babu, ra’ayin na su na kan turba. Tun bayan ɓarkewar rikicin Rasha da Ukraine, ba tare da la’akari da tarihin matsalolin Ukraine ba, da irin tasirin da ƙara matsawar NATO zuwa gabashi…
Read More