Editor

9513 Posts
Sabuwar masana’antar samar da sikari da Sin ta gina a Habasha, ta fara aiki

Sabuwar masana’antar samar da sikari da Sin ta gina a Habasha, ta fara aiki

Daga CMG HAUSA Kamfanin samar da suga na ƙasar Habasha, ESC, ta bayyana cewa, sabuwar masana’tarta na samar da Suga ta Tana Bales No.1 sugar factory, ta fara aiki. Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, kamfanin ESC ya ce masana’atar sugan, wadda kamfanin gine-gine na CAMCE na ƙasar Sin ya gina, ta fara aikin samar da Suga a ranar Alhamis, bayan shafe watanni tana gudanar da shirye-shirye. An fara aikin ginin masana’atar sugar dake yankin Amhara na arewacin ƙasar ta gabashin Afrika ne a shekarar 2012, inda aka tsara kammalawa cikin watanni 18. Sai dai, aikin ginin bai…
Read More
Babban Taron APC: Za mu ba wa maraɗa kunya, inji Buhari

Babban Taron APC: Za mu ba wa maraɗa kunya, inji Buhari

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewar, jam’iyyar APC tana da kuzarin kawo maslaha dangane da bambance-bambance dake akwai a tsakanin ‘ya’yan ta kan lamuran zaɓen shugabannin ta da za a gudanar nan ba da jimawa ba. Shugaba Buhari, wanda ya yi adabon barin Abuja zuwa birnin Landan ta ƙasar Biritaniya a ranar Lahadi da ta gabata dangane da abinda ya kira, ‘Tuntuɓar kiwon lafiya’, ya ce la’akari da tanade-tanaden tsarin mulkin ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo zai riƙe madafun mulki yayin da ba ya nan. Jam’iyyar APC dai, ta dulmuya cikin rakacaniya ta…
Read More
Aikin shimfiɗa bututun gas ya cimma kashi 73 da kammaluwa – Darakta Ahmed

Aikin shimfiɗa bututun gas ya cimma kashi 73 da kammaluwa – Darakta Ahmed

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa kawo yanzu, aikin shimfiɗa bututun gas da gwamnatin Buhari ke yi daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano ya kai kashi 73.3 cikin 100 da kammaluwa. Darakta a sahen makamashin gas na Kamfanin Fetur na Ƙasa, Injiniya Abdulkadir Ahmed ne ya bayyana hakan a wajen wani taro da ya gudana ran 5 ga Maris. Ahmed ya ƙara da cewa, jihar Kaduna za ta ci moriyar wutar lantarki mai ƙarfin megawat 900 idan an kammala aikin. Idan dai za a iya tunawa, gwamnatin Buhari ta soma aiwatar da aikin shimfiɗa bututun gas ɗin ne tun a…
Read More
Ta rasu ran jajibirin aurenta

Ta rasu ran jajibirin aurenta

Daga BASHIR ISAH Bisa sahihan bayanan da Blueprint Manhaja ta samu, a yau Asabar ne ranar da aka tsayar don ɗaura auren Hajara wadda Allah Ya yi wa rasuwa a jiya Juma'a. Marigayiya Hajara mazaunin yankin Masaƙa ce cikin ƙaramar hukumar Karu, jihar Nasarawa, ta rasu ne bayan gajeriyar jinya. Kafin rasuwarta, Hajara 'Nurse' ce wadda al'umma ke amfana da ita. 'Yan'uwa, masoya da abokai na ci gaba da nuna alhinin wannan rashi tare da yi wa marigayiyar fatan samun Aljanna Firdausi.
Read More
Dakarun NDLEA sun kama ƙwayoyin Turamol 294,440 a jihohin Bauchi da Delta

Dakarun NDLEA sun kama ƙwayoyin Turamol 294,440 a jihohin Bauchi da Delta

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Dakarun Hukumar Yaƙi da Sha da Fatauci da Miyagun Ƙwayopyi (NDLEA) sun cafke ƙwayoyi masu yawan 294, 440 na Tramadol, Diazepam, Swinol, Rohyphnol da Exol-5, haɗe kuma da wasu muggan ƙwayoyin daban a samamen da suka yi a jihohin Delta da Bauchi da kuma filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Ikeja ta Legas. Jimlar mutanen da ake zargi 41 da ta’ammali da ƙwayoyin aka cafke a yayin farmakin daban-daban, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar,  Femi Babafemi ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi da ta gabata.…
Read More
NNPC da Ɗangote sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa gas don takin zamani

NNPC da Ɗangote sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa gas don takin zamani

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin rarraba man fetur na Nijeriya, NNPC, ta bayyana cewa, ta ƙulla yarjejeniya tare da kamfanin attajiri Ɗangote don ta dinga samar musu da gas.  Kamfanin NNPC, ya bayyana cewa, ɓangarorin biyu sun rattaba hannu a yarjejeniyar ne  A garin Abuja yayin taron a kan harkar makamashi na ƙasa karo na biyar. Wanda aka gudanar ranar Alhamis 3 ga watan Maris, 2022. Ɓangarorin da suka qulla yarjejeniya a tsakaninsu sun haɗa da, NNPC, Kamfanin Shell (SPDC), Kamfanin Gas na Total(GACN). Da ya ke faɗar albarkacin bakinsa game da  yarjejeniyar, Mele Kyari, shugaban Kamfanin NNPC ya bayyana…
Read More
Ƙaramin kwamitin siyasa da diflomasiyya na babban kwamitin tsakanin Sin da Nijeriya ya gudanar da taronsa na farko

Ƙaramin kwamitin siyasa da diflomasiyya na babban kwamitin tsakanin Sin da Nijeriya ya gudanar da taronsa na farko

Daga CMG HAUSA A ranar 10 ga watan Maris, ƙaramin kwamitin siyasa da diflomasiyya na babban kwamitin tsakanin ƙasashen Sin da Najeriya ya gudanar da taronsa na farko ta kafar bidiyo, wanda Deng Li, mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Sin, da Zubairu Dada, karamin ministan harkokin wajen Najeriya suka jagoranta. Ɓangarorin biyu sun yi nazari kan ci gaban da aka samu game da hulɗar dake tsakanin ƙasashen biyu, da kuma haɗin gwiwarsu a fannoni daban-daban, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan batun aiwatar da sakamakon da aka samu a taron ministoci karo na 8 na taron dandalin tattaunawar haɗin gwiwar…
Read More
Da yiwuwar mace ta yi gwamna a Kaduna, inji El-Rufai

Da yiwuwar mace ta yi gwamna a Kaduna, inji El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa, yana da yaƙinin cewa, mace za ta iya ɗarewa kujerar gwamna a jihar duba da yawan mata a Kadunan. Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a Kaduna a ranar Talata, El-Rufai ya ce mata su na da damar yin gwamna har kashi 50 cikin 100 duba da cewa sune su ka kwashi rabin al'ummar jihar. El-Rufai, wanda mataimakiyarsa mace ce, Hadiza Balarabe, ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da bai wa mata damarmaki daidai da maza. Ya ƙara da cewa gwamnatin…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta horas da matasa kan dabarun kula da abincin ‘yan gudun hijira a Keffi

Gwamnatin Tarayya ta horas da matasa kan dabarun kula da abincin ‘yan gudun hijira a Keffi

Daga BASHIR ISAH A ranar Larabar da ta gabata Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira da Waɗanda Rikici ya Ɗaiɗaita (NCFRMI) ta kammala shirin horar da gomman matasa a garin Keffi, jihar Nasarawa kan dabarun girke-girke don amfanin waɗanda rikici ya ɗaiɗaita. Shirin ya gudana ne a ƙarƙashin kulawar Kwamishinar Tarayya a ma'aikatar NCFRMI, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, inda aka horas da matasa kan dabarun sarrafa abinci ga waɗanda rikici ya ɗaiɗaita da suke zaune a garin Keffi. Shirin bada horon ya gudana ne na tsawon kwanaki biyar, wanda bayan kammalawa aka miƙa wa kowannensu shahadarsa tare da kayan aiki…
Read More
Babban taro: INEC ta ankarar da APC wasu dokoki

Babban taro: INEC ta ankarar da APC wasu dokoki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi fatali da wasiƙar gayyata zuwa wajen taron Majalisar Zartaswa (NEC) na gaggawa na jam'iyyar All Progressives Congress, (APC). Hukumar INEC ta bayyana cewa ta yi watsi da takardar ne saboda ba ta ga sa hannun Shugaban Riƙon Jam'iyyar APC da na Sakataren sa ba. Da yiwuwar yunƙurin cire Mai Mala Buni ƙarfi da yaji ya haifar da matsala a babban taron ƙasa da jam'iyyar ta shirya za ta yi a ƙarshen watan Maris ɗin nan. INEC, a wasiƙar da ta aike ranar 9 ga…
Read More