Ta rasu ran jajibirin aurenta

Daga BASHIR ISAH

Bisa sahihan bayanan da Blueprint Manhaja ta samu, a yau Asabar ne ranar da aka tsayar don ɗaura auren Hajara wadda Allah Ya yi wa rasuwa a jiya Juma’a.

Marigayiya Hajara mazaunin yankin Masaƙa ce cikin ƙaramar hukumar Karu, jihar Nasarawa, ta rasu ne bayan gajeriyar jinya.

Kafin rasuwarta, Hajara ‘Nurse’ ce wadda al’umma ke amfana da ita.

‘Yan’uwa, masoya da abokai na ci gaba da nuna alhinin wannan rashi tare da yi wa marigayiyar fatan samun Aljanna Firdausi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *