06
Feb
Babbar kotun jihar Kaduna da ke zama a unguwar Dogarawa ta garin Zariya, ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar da ake yi wa Abubakar Halliru bisa zargin hannunsa a garkuwa da wata ’yar uwarsa zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu 2022. Ana dai tuhumar Abubakar Halliru kan zargin kai wata ’yar uwarsa wajen masu garkuwa da mutane domin karvar kuɗin fansa. A yayin da take bayar da shaidar abin da ya faru a tsakaninta da Abubakar Halliru, Hajiya Binta Muhammad ta yi wa kotu bayanin cewa, shi wanda ake tuhumar ɗan uwanta ne kuma ta amince da shi matuƙa…
