Editor

9513 Posts
Dalilin da ya sa na cancanci zama Shugaban APC na Ƙasa – Al-Makura

Dalilin da ya sa na cancanci zama Shugaban APC na Ƙasa – Al-Makura

Daga IBRAHEEM HAMZA MUH’D a Lafia Sanata Umaru Tanko Al-Makura shi ne tsohon Gwamnan jihar Nasarawa kuma yana ɗaya daga cikin ’yan takarar kujerar Shugaban Jam'iyyar APC ta Ƙasa. Ya zanta da Wakilin jaridar Blueprint Manhaja, Ibraheem Hamza Muhammad kan takarar tasa. Ga yadda hirar tasu ta kasance: MANHAJA: Jam'iyyar APC za ta yi zaɓen fitar da sabbin shugabannin jam'iyya. Mene ne manufarka?Maƙasudin yin takarata ita ce, Ina ɗaya daga cikin iyayen jam'iyya, don daga Jam'iyyar CPC aka samar da ACP. Wato a turance ‘Merger’ kenan. Kuma mu na son ganin an ciyar da jam'iyyar gaba da mutumci. Na yi…
Read More
Zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar MOPPAN ya zo da sabon salo

Zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar MOPPAN ya zo da sabon salo

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano  Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya fim ta ƙasa, wato ‘Motion Picture Practitioners Associations of Nigeria’ (MOPPAN), ta gudanar da zaɓen sabbin shugabanninta bayan kammala wa'adin shugabancin shugabannin na tsawon shekaru biyu, kamar yadda tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada. Zaɓen dai an gudanar da shi ne a ranar Juma'ar da ta gabata a babban ɗakin taro na otel ɗin Ni'ima da ke cikin garin Kano. Taron, wanda kafin gudanar da shi aka fara da Babban Taron Ƙungiyar na Ƙasa, wato 'Congress', wanda a lokacin aka yi zaman Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Ƙungiyar, inda aka shafe…
Read More
Kannywood: Babban Kwamandan Hisbah ya watsa wa Shugaban Hukumar Finafinan Kano ƙasa a ido

Kannywood: Babban Kwamandan Hisbah ya watsa wa Shugaban Hukumar Finafinan Kano ƙasa a ido

Daga WAKILINMU a Kano A daidai lokacin da Shugaban Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba Afakallahu, bai halarci taron rantsarwa da liyafar cin abincin dare da Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya shirya wa sababbin zaɓaɓɓun shugabannin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa (MOPPAN) a Gidan Gwamnatin Jihar Kano ba, shi kuwa Babban Kwamandan Hisbah na Jihar ta Kano, Sheikh Harun Muhammad Ibn Sina, ya halarci taron ne, inda har ma gabatar da addu’o’i a wajen gangamin, ya na mai sanya albarka ga masu sana’ar ta shirya finafinan Hausa a Kano da ma ƙasa…
Read More
Uwa ta kai ɗanta kotu a Kano

Uwa ta kai ɗanta kotu a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masu iya magana na cewa, abinda ya koro ɓera ya faɗa wuta to ya fi wutar zafi. Wannan karin maganar ta yi daidai da lamarin da ya faru a Jihar Kano, yayin da mahaifiya, duk irin so da ƙaunar da uwa ke yi wa ɗanta, amma saboda wannan ya addabe ta, sai ta kai shi gaban alƙali domin a hukunta shi. Mahaifiyar, wacce a ka sakaya sunanta, ta maka ɗan cikin nata a kotun shari'ar Muslunci mai lamba 1 da ke Ƙofar Kudu a birnin Kano ranar Talatar da ta gabata. Cikin kuka, mahaifiyar…
Read More
Tasirin abokan miji a zaman aure

Tasirin abokan miji a zaman aure

Daga AMINA YUSUF ALI Masu karatu sannunmu da sake haɗuwa a wani makon a filin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da bayani a kan yadda abokan miji suke bayar da gudunmowa wajen ingantawa ko kuma rusa zaman aure.  Mun sani dole ɗan adam ya yi abota a rayuwarsa. Ba ma zai iya rayuwa babu abokan ba. Haka kamar yadda mace ke yin ƙawaye, haka shi ma namijin yana yin abokai. Wasu abokan tare ake tasowa tun ana ƙanana, har  samartaka, duka akan yi tare, har a yi aure.   To, bayan an…
Read More
Rikicin APC a Kano: Har yanzu tsuguno ba ta ƙare ba

Rikicin APC a Kano: Har yanzu tsuguno ba ta ƙare ba

A matayin wani yunƙuri na neman kashe wutar rikicin jam'iyyar APC da ke ci gaba da ruruwa a jihar Kano, Gwamnan Yobe kuma shugaban riƙo na APC na ƙasa, Mai Mala Buni, ya sake ganawa da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau. Ganawar wadda aka shafe kusan sa'o'i shida ana yin ta, ta gudana ne a masaukin gwamnan Yobe da ke birnin tarayya, Abuja. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna yayin zaman, kowane ɓangare ya gabatar da buƙatunsa tare da shawarwarin kan yadda za a shawo kan rashin jituwar da ke tsakani.…
Read More
Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya sheƙa zuwa ADC

Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya sheƙa zuwa ADC

Fitaccen malamin nan na Kano kuma Shugaban Majalisar Malamai na Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar 'African Democratic Congress' (ADC). Shugaban jam'iyyar ADC na Kano, Musa Shuaibu Ungogo ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, inda ya ce Sheikh Ibrahim Khalil ya koma ADC ne tare da Dr. Saidu Ahmad Dukawa. Ungogo ya ce Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya sheƙarsa zuwa ADC ne tare da wasu shaihinnan malamai su takwas don ceto Kano daga matsalar rashin jagoranci nagari da barace-barace da kuma shaye-shaye na miyagun ƙwayoyi. Ya ƙara da cewa, nan ba da daɗewa ba babban…
Read More
Sarkin Jama’are, Muhammadu Wabi III ya kwanta dama

Sarkin Jama’are, Muhammadu Wabi III ya kwanta dama

Allah Ya yi wa Sarkin Jama’are, Alhaji Ahmad Muhammadu Wabi III rasuwa. Marigyin ya rasu ne bayan fama da rashi lafiya. Manhaja ta fahimci cewa Sarkin ya rasu ne da tsakar daren ranar Lahadi, bayan da ya shafe shekara 50 a kan sarauta. Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya talatin da biyar. Sa'ilin da yake sanar da rasuwar sarkin, Gadodamasun Jama’are, Alhaji Salleh Malla ya ce haƙiƙa wannan babban rashi ne ga masarautar Jama'are, jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya.
Read More
Nijeriya ta amince Kamfanin jiragen Emirates su koma aiki a ƙasar

Nijeriya ta amince Kamfanin jiragen Emirates su koma aiki a ƙasar

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Najeriya ta amince jiragen kamfanin sufurin jirgin sama na Emirates da ke Dubai su koma jigila a ƙasar kowane lokaci daga yanzu. A yayin da kamfanin jirgin Air Peace da ke Nijeriyar shi ma ya ce zai koma safara zuwa Dubai, daga ranar1 ga watan Maris na 2022. Sanarwar tana ƙunshe ne a wata wasiƙa da Hukumar Kula da Sufurin Jirgin Sama ta Najeriya (NCAA) mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Captain Musa Nuhu ta rubuta wa shugaban hukumar sufurin jirgin sama ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Saif Mohammed Al Suwaid. A wasiƙar, hukumar ta Najeriya…
Read More
Rasha za ta ci gaba da tsayawa kan bakarta kan lamarin Ukraine

Rasha za ta ci gaba da tsayawa kan bakarta kan lamarin Ukraine

Sakataren harakokin wajen Amurka Antoni Blinken, ya buƙaci Rasha da ta gaggauta bada haɗin kai don sauƙaƙa wutar rikicin da ke ƙara ruruwa tsakanin ta da Ukraine a yunƙurin da ta ke yi na mamaye ta. Blinken wanda ke waɗannan kalamai a yayin tattaunawar sa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov, inda ya ce hanyar da Rasha za ta bi wajen sauƙaƙa wannan al’amari kuwa shi ne, janye dakarun da ta jibge kan Iyakar Ukraine. Blinken ya kuma jadadda cewa, duk wani yunƙuri na ci gaba da mamaye Ukraine daga Rasha, zai janyowa ƙasar tashin hankali ta ɓangarori mabanbanta, inda…
Read More