Editor

9513 Posts
Ƙasashen ECOWAS na shirin yanke mu’amala da Ƙasar Mali

Ƙasashen ECOWAS na shirin yanke mu’amala da Ƙasar Mali

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta yamma ECOWAS, za ta ƙaƙaba wa mulkin soji a Mali takunkumi, yayin da ƙasashe mambobin ƙungiyar za su janye dukkan jakadunsu da kuma rufe iyakokin ƙasa da na sama da ƙasar. Wannan wani ɓangare ne na sakamakon Babban Taron Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatin ECOWAS da aka gudanar a Lahadin da ta gabata a Accra, babban birnin Ƙasar Ghana. Babban mataimaki na musamman ga Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya kan harkokin yaɗa labarai, Laolu Akande ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Ƙasashen ECOWAS za su…
Read More
Yadda ƙungiyar KAHOSSA 97 ta tallafa wa mambobinta marasa ƙarfi

Yadda ƙungiyar KAHOSSA 97 ta tallafa wa mambobinta marasa ƙarfi

Daga ABUBAKAR M. TAHIR a Jigawa Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar Sakandaren Kimiyya da Fasaha da ke garin Kafin Hausa aji na shekarar 1997 ta gudanar da babban taronta na shekara a makarantar koyon jinya da ke garin Haɗejia. Taron da ya samu halartar ’yan ƙungiyar daga jihohi Kano, Jigawa, Yobe da Bauchi ya samu halartar Shugaban Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa (NITDA), Malam Kashifu Inuwa da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Gumel. Da yake jawabi ga manema labarai, Shugaban hukumar NITDA, Malam Kashifu Inuwa ya bayyana cewa, sun saba gudanar da irin wannan taro duk shekara wanda suke yin zumunci da…
Read More
Yadda ‘Super Tucano’ ya tilasta wa ISWAP naɗa sabbin kwamandodji

Yadda ‘Super Tucano’ ya tilasta wa ISWAP naɗa sabbin kwamandodji

Daga BASHIR ISAH A halin da ake ci ƙungiyar ISWAP ta yi wa shugabancinta kwaskwarima inda ta naɗa wasu 'ya'yanta a muƙamai daban-daban don ci gaba da jan ragamar ƙungiyar. Ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon hasarar kwamandojin da ta tafka biyo bayan hare-haren da jirgin yaƙi na Super Tucano ya kai wa mayaƙan ISWAP kwnan nan wanda ya yi sanadiyar mutuwar kwamandoji da mayaƙan ƙungiyar da dama. Jaridar PRNigeria ta kalato cewa, taron kwanaki biyu da 'yan ISWAP suka gudanar ƙarƙashin jagorancin Sani Shuwaram, ya samu halarcin 'yan Majalisar Shura da kwamandojin 'yan ta'adda daga yankin Marte da…
Read More
‘Arewa Media Writers’ ta gargaɗi matasa kan yaɗa labaran ƙarya

‘Arewa Media Writers’ ta gargaɗi matasa kan yaɗa labaran ƙarya

Daga HARUNA UMAR a Jos Reshen ƙungiyar ‘Arewa media writers’ na jihar Filato da ke fafutukar kawo sauyi a harkar rubuce-rubuce ta kafofin sada zumunta, ta gabatar da babban taron ta na ƙarshen shekarar 2021 don ƙara wa juna sani a kan muhimmancin sarrafa na'ura mai ƙwaƙwalwa ta hanyar yaɗa labarai da gudanar da kasuwanci ta yanar gizo. Taron da ya samu wakilcin manyan marubuta, ’yan jaridu, ƙungiyoyin addini, na siyasa da na cigaban al'umma daga ciki da wajen garin Jos, ya gudana ne  a ɗakin taro na ‘Abba na Shehu Unity Hall’ da ke Babban Birnin Jihar Filato. A lokacin…
Read More
Jikinmu lokacin hunturu

Jikinmu lokacin hunturu

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu, Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. A yi min afuwa na shiru da a ka ji, hakan ya faru ne sakamakon tarin ayyuka da su ka yi min yawa. Amma yanzu alhamdulillah! Duba da lokacin da muke ciki yanzu, wato lokacin hunturu, rubutun yau zai mayar da hankali wajen bayani akan yadda jikin dan adam ke gudanar da al’amuransa lokacin sanyi; da kuma shawarwari kan yadda…
Read More
Yadda Birrai suka fusata suka kashe karnuka 250

Yadda Birrai suka fusata suka kashe karnuka 250

Birrai a wani birnin Indiya sun kashe karnuka 250, tare da jefo su daga saman manyan benaye da bishiyoyi, kamar yadda kafar labarai ta News18 ta ruwaito. Mazauna yankin Labool, wani gari ne mai kimanin mutum 5,000 da ke da nisan mil 300 a gabas da birnin Mumbai, sun shaida wa News18 cewa, birrai sun fara ɗaukar fansa ne a watan jiya bayan da wasu karnuka suka kashe wani ɗan biri ɗaya. Mazauna yankin sun ce, tun daga lokacin ne birrai suka fara farautar karnuka ta yadda da zarar sun hango su sai su ja su zuwa saman dogayen gine-gine…
Read More
Zargin fyaɗe: An garƙame makarantun islamiyya biyu a Kaduna

Zargin fyaɗe: An garƙame makarantun islamiyya biyu a Kaduna

Daga WAKILINMU Hukumar Kula da Ingancin Makarantun na jihar Kaduna (KSSQA), a makon da ya gabata ta rufe makarantun Islamiyya biyu a jihar har sai masha Allahu kan zargin yi wa ɗalibai fyaɗe da yi wa wata ɗalibar ciki. An rufe ɗaya daga cikin makarantun mai suna Madrasatul Ulumul Deeniya wa Tahfizul Qur’an a Rigasa ne kan zargin yi wa wata yarinya mai shekaru shida fyaɗe a harabar makarantar. Ɗayan makarantar Islamiyyar kuma tana Tsohon Masallacin Juma’a ne na Kachia, a ƙaramar hukumar Kachia na jihar Kaduna, shi ma an rufe shi ka zargin wani mallami mai shekaru 50 da…
Read More
Buhari ya zaɓi sabbin shugabannin hukumar kamfanin NNPC

Buhari ya zaɓi sabbin shugabannin hukumar kamfanin NNPC

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaba Buhari ya zaɓi sababbin shugabannin hukumar kamfanin NNPC. Shugaban ƙasar Nijeriya, Muhammadu ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai a sabon kamfanin NNPC. Shugaban ya yi wannan naɗi ne da amfani da damar ikon da sashe na 59(2) na sabuwar dokar man fetur a kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar (2021) ya ba shi. Kakakin Fadar Shugaban ƙasar, Mista Femi Adeshina shi ya tabbatar da wannnan labari ranar Larabar da ta wuce a Abuja. A cewar sa, an naɗa wasu muƙamai kamar haka: Shugabar Kwamitin ita ce Sanata Margret Chuba Okadigbo, sai Mele Kolo Kyari, a matsayin…
Read More