09
Jan
Daga WAKILINMU A tsakanin watannin Yuni da Yulin bara ya kamata a yi gasar, amma annobar Korona ta sa aka ɗage zuwa bana. Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta nahiyar Afirka CAF ta ce kashi 60 zuwa 80 na ’yan kallo za a bari su shiga filayen wasanni da za a kara gasar cin kofin nahiyar na AFCON. Matakin a cewar hukumar na da nasaba da annobar COVID-19. Cikin wata sanarwa da ta fitar, CAF ta ce bayan wata tattaunawa da ta yi da hukumomin cikin gida na Kamaru, sun cimma matsaya akan cewa kowanne filin wasa za a bar ‘yan kallo…
