Editor

9513 Posts
2023: Ba zan bayyana wanda na ke so ba don kada a ɓatar da shi – Buhari

2023: Ba zan bayyana wanda na ke so ba don kada a ɓatar da shi – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da ɗan takara ɗaya da zuciyarsa ta raja’a akan shi ya gaje shi. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a hira da ya yi da talbijin ɗin Channels TV a Abuja ranar Laraba. ”Ba ni da wanda na ke so ƙarara ya gaje ni a 2023, idan ma akwai to zan bar shi a can cikin zuciyata kawai domin idan na faɗi kila gobe a neme shi a rasa." Wa’adin mulkin Buhari zai kare ne a cikin shekarar 2023, wannan ya sa tun daga yanzu…
Read More
Hana Ighalo wakiltar Nijeriya: Eguavoen ya mayar da martani ga Al-Shabab

Hana Ighalo wakiltar Nijeriya: Eguavoen ya mayar da martani ga Al-Shabab

Daga WAKILINMU Kocin riƙon ƙwarya na Super Eagles, Augustine Eguavoen, ya ce, yana da ƙwarin gwiwar cewa Odion Ighalo zai haɗa kai da sauran ‘yan wasan da za su buga gasar kofin Afrika ta 2021. Ƙungiyar Al Shabab ta Ighalo ta ƙi sakinsa a domin fafata gasar. Wannan ya sa tsohon ɗan wasan Manchester United da Watford ya shiga tsakanin kulob da ƙasar. An ruwaito Ighalo yana Nijeriya kuma yana da wa’adin tabbatar da kasancewarsa. “Da fatan Odion ya zo,” inji Eguavoen a wani taron manema labarai a ranar Talatar da ta gabata. Ana kyautata zaton cewa gogaggen ɗan wasan…
Read More
Amurka ta buƙaci kamfanonin sadarwa su dakatar da aikin fasahar 5G

Amurka ta buƙaci kamfanonin sadarwa su dakatar da aikin fasahar 5G

Hukumomin Amurka sun nemi kamfanonin sadarwa na AT&T da Verizon da su jinkirta aikin sadarwar 5G har tsawon makonni biyu, yayin da ake ganin rashin tabbas game da katsalandan ga muhimman kayayyakin kariya na jiragen sama. Tuni dai kamfanonin suka fitar da sanarwar cewa sun fara nazartar wannan buƙata ta gwamnatin Amurka. A ranar 5 ga watan Disamba ne Amurka ta fitar da fasahar sadarwar wayar tafi-da-gidanka, amma aka jinkirta zuwa ranar 5 ga watan Janairu bayan da manyan kamfanonin sararin samaniyar Airbus da Boeing suka nuna damuwa game da katsalandan da na'urorin da jiragen ke amfani da su wajen…
Read More
Jirgin Tukano: Amurka ta fara yi wa Buhari barazana

Jirgin Tukano: Amurka ta fara yi wa Buhari barazana

…Bayan Malami ya ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A wani yanayi na kawo tarnaƙi ga ƙoƙarin da Shugaban Nijeriya Muhammadu ke yi wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaron ƙasar, musamman ma ’yan bindiga, waɗanda suka suka warwatsu a faɗin ƙasar suna yi wa ’yan Nijeriya kisan kiyashi, Gwamnatin Amurka ta yi barazana ga Shugaba Buharin kan amfani da fitaccen jirgin yaƙin nan da ta sayar wa Nijeriya na Super Tucano (Tukano) a kan ’yan bindigar bayan da Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya sanar da ayyana su ’yan bindigar…
Read More
ECOWAS ta ba wa Najeriya mafita kan tafiyar hawainiya a sashen noma

ECOWAS ta ba wa Najeriya mafita kan tafiyar hawainiya a sashen noma

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban sashen harkar noma na gamayyar ƙungiyoyin Afirka ta Yamma (ECOWAS), Dakta Ernest Aubee ya yi kira ga Nijeriya da ta magance tafiyar hawainiyar da sashen noma yake yi a ƙasar. A cewar Ernest Aubee, wannan shi ne kaɗai abinda zai kawo mafita a kan matsalolin da suke kewaye da fataucin hatsin da ƙasar ta noma a tsakaninta da ƙasashen yankin na Afirka ta Yamma. Wasu daga cikin matsalolin da a cewar sa auke kawo cikas sun haɗa da, jinkirta motocin kayan abincin daga shiga bodar wasu ƙasashen, biyan maƙudan kuɗaɗen da ake yi kafin a…
Read More
An rufe kasuwanni a Jihar Oyo saboda rasuwar basarake

An rufe kasuwanni a Jihar Oyo saboda rasuwar basarake

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar litinin ɗin da ta gabata ne dai aka tashi da umarnin a rufe dukkan kasuwanni a jihar Oyo domin nuna girmamawa da alhini ga rasuwar Sarkin Ibadan ta jihar Oyo, (Olubadan); Oba Saliu Adetunji. Wannan umarni na rufe dukkan kasuwannin faɗin jihar ya fito ne daga babban shugaban kasuwanni na jihar ta Oyo, Asiwaju Yekini Abass wanda aka fi sani da YK Abass. Umarnin ya biyo bayan wani taron gaggawa na shugabannin kasuwanni na jihar da babban shugaban kasuwannin, YK Abass ya kira a ranar Lahadin da ta gabata. Wato jim kaɗan bayan mutuwar…
Read More
Har yanzu dai ta na jika kan batun matsalolin aure!

Har yanzu dai ta na jika kan batun matsalolin aure!

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Jama'a Assalamu Alaikum. Ina neman afuwa da dogon lokaci da na ɗauka ba a ji ni ba, rai da jini. Ga mu yau ma cikin filinmu mai albarka, filin tarbiyya. Har yau dai ba ta sake zani ba! Muna cikin yanayi na matsalolin na yadda auratayya take tafiya a wannan zamani. Har yanzu muna cin karo da matsalolin auratayya na yaranmu dake faman rushewa kamar wutar daji, wanda kullum kukan iyaye dai wannan matsalar. Ni a iya kaina na ci karo da wannan kyasa-kyasan fiye da ashirin wallahi cikin sati biyu kacal. Ya ilahil alamina! daga…
Read More
Barace-baracen ƙananan yara a tituna abin dubawa ne

Barace-baracen ƙananan yara a tituna abin dubawa ne

Ga duk mai dubi zuwa ga yadda aka jefa ƙananan Yara cikin harkar barace- barace, musamman a biranen ƙasar nan zai ga cewa akwai sosar zuciya mutaƙa, musamman ganin yadda yaran ke fama da wahala, sannan ga ɓata sunan Hausawa da abin ke jawowa. Akwai abubuwa da dama, waɗanda idan mutum ya yi dubi zuwa garesu za su dagula masa rayuwa ya ma rasa abin da ke masa daɗi, musamman idan aka duba yadda wasu abubuwa ke jawo wa rayuwar al’ummar da abin ya shafa. Wasu daga cikin waɗannan abubuwa, waɗanda kuma za mu iya cewa babu wani mai farin…
Read More
Babu ɗan siyasar da ya taimaki Kannywood kamar Sanata Barau – Sani Indomie

Babu ɗan siyasar da ya taimaki Kannywood kamar Sanata Barau – Sani Indomie

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A daidai lokacin da guguwar siyasar 2023 ta fara kaɗawa, su ma' yan fim da su ke shiga harkar siyasa sun fara motsi domin ganin harkar ba ta bar su a baya ba. Sani Ali Abubakar, wanda aka fi sani da Furodusa Sani Indomie yana ɗaya daga cikin 'yan fim da su ke shiga harkar siyasa, don haka ne mu ka ji ta bakin sa kan irin matakin da za su ɗauka dangane da zave mai zuwa don ganin sun samar wa da masana'antar cigaban da a ke buƙata, in da ya fara da cewar.…
Read More
An cafke malamin addini da ƙoƙon kan mutum

An cafke malamin addini da ƙoƙon kan mutum

Daga WAKILINMU Wani wanda ya kira kansa malamin addinin Musulunci mai shekaru 55, Tunde Olayiwola, ya amsa cewa ya sayo sabon ƙoƙon kan ɗan'adama a Ajabbale, Oka a jihar Ondo. Olayiwola, wanda ’yan sanda na jihar Ondo suka yi holensa ya ce, ya sayo kan bil adaman ne domin a yi masa asirin kuɗi. A hirar da ka yi da shi, wanda ake zargin da ya bayyana cewa, shi ɗan asalin garin Osogbo ne a jihar Osun, ya ce, ya siya ƙoƙon ne kan kuɗi Naira 60,000 domin a masa asiri. Ya ce, “wani mutum da muka haɗu a wurin…
Read More