Editor

9513 Posts
Yanomami: Ƙabilar da ke ƙone gawar danginsu su cinye

Yanomami: Ƙabilar da ke ƙone gawar danginsu su cinye

Ƙabilar Yanomami wanda aka fi sani da ‘Senema’ ko ‘Yanam’ da aka fi samu a yankunan ƙasashen Brazil da Venezuela, a Kudancin Amurka, tana da wata al’ada mai ban mamaki ta ƙone duk wanda ya mutu a cikinta ta sarrafa ta cinye. ’Ya’yan wannan ƙabila ba su damu da abubuwan zamani ba, sun fi mai da hankali ga ci gaba da bin al’adunsu na gargajiya. Saɓanin yadda sauran ƙabilu ke binne mutum idan ya rasu, ƙabilar Yanomami ta bambanta na ƙonewa ne ta ci naman matacce, duk lokacin da ɗan uwansu ya mutu ko wani da ke zaune a yankunansu.…
Read More
An buɗe kasuwar Gwandu bayan shekaru 27 da gina ta

An buɗe kasuwar Gwandu bayan shekaru 27 da gina ta

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ranar Juma'ar da ta gabata ne aka buɗe kasuwar garin Gwandu bayan shekaru ashirin da bakwai da gininta. Wakilinmu ya yi tattaki zuwa garin na Gwandu inda ya zanta da Malam Abubakar Zaki daga cikin jagororin gudanarwa na 'yan kasuwar ƙaramar hukumar mulki ta Gwandu, ya bayyana cewa an daɗe da gina wannan kasuwar amma sai dai aka bar ta nan ba a dawo ba kimanin shekaru ashirin da bakwai Allah ya kawo lokacin da za ta soma ci. Ya yaba wa Alhaji Muhammadu Mode bisa ga irin ƙoƙarin sa na ganin an baro cikin…
Read More
WASIƘU: Miladiyya 2022

WASIƘU: Miladiyya 2022

*Marigayi Muhammad Awwal Musa: Mutum mai hagen nesa Assalmu alaikum. Ba don na isa ba, magana ce mai buƙatar mu ƙara nutsuwa mu ɗauko madubi ta fuskar addini mu ga ina ne matsalar ta ke, kuma ta ina gyaran zai wanzu a sauƙaƙe. Makon jiya ne mabiya addinin Kirista su kai bukukuwan ibadunsu. Bisa zamantakewa ta makwabtaka ko wasu huldodi ana samun wasu musulmai na bazama wajen gudanar da shagulgula tare da abokan zamanmu. Duk da kasancewa ni ba malami ba ne amma ya dace idan musulmi zai gudanar da komai ya tuntuɓi malamai, shin Halal da akasinta domin kar…
Read More
Me ya sa maza suke ƙara aure? (2)

Me ya sa maza suke ƙara aure? (2)

Daga AMINA YUSUF ALI Assalam, barkanmu da sake haɗuwa a wani makon mai albarka. Har yanzu muna kan maganar dalilan da suke sa maza ƙara aure. Wato dalilai waɗanda ba su da alaƙa kuma da matsalolin matansu na gida. Wanda ba sai na ƙara maimaita bayanin da na yi a makon da ya gabata ba, a game da aƙidar ƙaro aure. A wannan karon, za mu dubi ɓangaren maza, kamar yadda a makon jiya muka fi mai da hankali ga mata. Amma kafin mu yi hakan, za mu cikasa sauran dalilan da suke sa maza su ƙaro aure. A wancan…
Read More
‘Yan sanda sun damƙe mutumin da ya halaka matarsa a Sule Tankarkar

‘Yan sanda sun damƙe mutumin da ya halaka matarsa a Sule Tankarkar

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse 'Yan sanda a yankin ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar da ke yankin Masarautar Gumel a Jihar Jigawa sun damƙe wani mutun mai suna  Bulama Muntari Ubale ɗan shekara 65 a duniya bisa zarginsa da yi wa matarsa duka da sanda har ta ka ga ya halakata.  Asirin Bulama ya tonu ne bayan da wani maƙocinsu ya ji ihun matar tasa, inda maƙocin mai suna Yusuf Zubairu mai kimanin shekaru 26 ya kai agaji a Rugar Fulanin Mailefe da ke cikin ƙauyen Baldi, inda ya taras ya yinwa matar tasa mai suna Fatima Harɗo Dare 'yar…
Read More
Alamomin ƙurajen da ake hanzarta ganin likita

Alamomin ƙurajen da ake hanzarta ganin likita

Daga AMINA YUSUF ALI Idan ƙuraje suka zo tattare da waɗannan matsaloli, wajibi a dangana da likita. Duk da dai yawanci ƙananan ƙuraje ba abin damuwa ba ne sosai, amma duk wanda ya ke fama da waɗannan alamomin nan, ya je ya ga likita kai-tsaye kawai: Ciwon maƙogoroCiwon gaɓoɓiIdan wani ƙwaro ko wata dabba ta cije ka gabanin su fito.4  Jajayen layuka ko dabbare-dabbare a gefen ƙurajen.Gefen ƙurajen yana raɗaɗiIdan ƙurajen suna ɗurar ruwa6  Launin fatar ya canza.Maƙogoro ya dinga buɗewa da ƙyar tare da jin wahalar numfashi. Zafi mai tsanani a ƙurajen. Zazzaɓi mai zafiKumburin fuska ko na wani waje a…
Read More
ACCF ta gudanar da babban taron bita

ACCF ta gudanar da babban taron bita

Daga ABUBAKAR M. TAHIR a Haɗeja Ƙungiyar Cigaban garin Auyo mai Suna ‘Auyo Concerned Citizens Forum’ (ACCF) a Turance, ta gudanar da babban taron shekarar 2021 a ɗakin taron da ke sakatariyar mulki ta ƙaramar hukumar. Taron wanda aka fara shi ranar Lahadi 26 ga watan Disamba wanda aka ƙarƙare shi 27 ga wata ya samu halartar ɗimbin al'ummar yanki, ’yan siyasa, masu aarauta, ’yan kasuwa dama ’yan bokon garin. Da farko an gabatar da kasida mai ɗauke da manufofin zauren dama nasarorin ɗaya samu wanda Shugaban Ƙungiyar, Injiniya Garba Adamu ya gabatar. Cikin jawabin nasa, ya bayyana cewa, sun…
Read More
Ƙungiyar IDDEP ta ba da tallafin yi wa yara kaciya a Kano

Ƙungiyar IDDEP ta ba da tallafin yi wa yara kaciya a Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Aƙalla yara 450 ne suka samu tallafin yi musu kaciya kyauta daga Ƙungiyar tallafa wa mabuƙata ta IDDEP, wato ‘Insana Deger Veren Dernekler’ tare da kulawar Cibiyar bincike da yaɗa ilimi ta Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, wato ‘Sheikh Muhammad Nasiru Kabara Research Center’. Da Malam Askiya Nasiru Kabara ya ke Jagoranta. Wannan dai shi ne Karo na shida da ƙungiyar ta saba yin wannan aiki na kaciyar yara a duk shekara, wanda Kuma a wannan shekarar aka samu ƙarin yaran da a ke yi wa daga 300 zuwa 450. Shugabar ƙungiyar ɓangaren mata da yara,…
Read More
Da kaji biyu na fara kiwo har na kai 150 – Zainab Aqeela

Da kaji biyu na fara kiwo har na kai 150 – Zainab Aqeela

"Soshiyal midiya kwalba ce, idan ka so ka zuba giya ko lemu" Daga UMAR GARBA, a Katsina Zainab Lawal Abdulƙadir wadda aka fi sani da Aqeela, matashiya ce kuma 'yar kasuwa, bayan nan ta kan gabatar da shirye-shiryen faɗakarwa, nishaɗantarwa gami da ilmintarwa a kafafen sada zumunta na zamani wato 'Social media'. Ta yi fice a tsakanin matasa maza da mata bawai a Jihar Katsina ba kaɗai har da sauran jihohin arewacin Nijeriya. Wakilin Manhaja a Katsina ya tattauna da Zainab Aqeela akan batutuwan da suka shafi kasuwancinta, alaƙarta da matasa da kuma yadda ta ke gabatar da shirye-shiryen da…
Read More
Asalin Ƙabilar Ibira

Asalin Ƙabilar Ibira

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kalmar ‘Ebira’ kalma ce da ke wakiltar yare, mutane, da kuma yanki (Okene da Suberu, 2013; Segun, 2013; Lukman, 2015). Wannan kalma tana da ma’ana ta kyakkyawar ɗabi’a’ (Segun da Samuel, 2010; Audu, 2010; Kwekudee, 2014). An siffanta al'ummar Ibira da cewa su mutane ne masu kyawawan halaye da suka haɗa da karvar baƙi, kulawa, mutuntaka, biyayya, jarumtaka, juriya, haƙuri, aiki tuƙuru, da sauransu (Audu, 2010; Kwekudee, 2014). Wannan yare na Ibira ya kasu kusan kashi shida; akwai Ibira Tawo (Ebira Tao) waɗanda su ne mafiya yawa da suke warwatse a kusan dukkan jahohi takwas ɗin…
Read More