Editor

9513 Posts
’Yan sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan fashin daji, Mai ‘Yan-mata a Zamfara

’Yan sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan fashin daji, Mai ‘Yan-mata a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da cafke wani ƙasurgumin ɗan fashin daji, Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai 'yanmata a jihar. Rundunar ta ce Mai 'yanmata, ɗan shekara 20 kacal da haihuwa, ya ƙware wajen garkuwa da mutane, fashin daji, satar shanu da sauran manyan laifuka a yankin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara. Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Zamfara, Ayuba N. Elkanah ne ya bayyana haka a taron manema labarai yayin da rundunar ta yi hoton ɗan ta'addan a ranar Laraba. A cewar kwamishinan, "a ranar 28…
Read More
Ƙananan hukumomin Bauchi sun fara cin gashin kansu, inji Gwamna Bala

Ƙananan hukumomin Bauchi sun fara cin gashin kansu, inji Gwamna Bala

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya shaidar cewa, ƙananan hukumomi ashirin na jiha a yanzu suna sarrafa kuɗaɗen su ne ba tare da wata katsalandan daga gwamnatin jiha ba, domin tun watan jiya na Nuwamba suka fara biyan albashin ma’aikatan su da kansu. Gwamnan ya ce, “Tuni muka ƙarfafa zuciyar mallaka wa ƙananan hukukomin jiha, muna basu dukkan ɗaukacin kuɗaɗen su, kuma tuni suka fara biyan albashin ma’aikatan su da kansu." Sanata Bala Mohammed ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake karɓar tawagar Kiristocin jihar Bauchi a fadar gwamnati, lokacin bukukuwan…
Read More
Sulhu ne samun zaman lafiyar Nijeriya – shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan’adam

Sulhu ne samun zaman lafiyar Nijeriya – shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan’adam

Daga HARUNA AKARADA a Kano Ɗaya daga cikin shuwagabannin kare haƙƙin ɗan adam na ƙungiyar nan ta ‘International Human Rights Today’, Kwamred Sa’id Bin Usman. Ya bayyana cewa, sulhu shi ne maslaha a Nijeriya.  Sa'id ya bayyana haka ne ranar Talatar da ta gabata a yayin  taron manema labarai inda wakilin Manhaja ya samu halarta.  Shugaban wannan hukumar ta kare haƙƙin ɗan Adam ya bayyana batun da ya fi mai da hankali a kansa wanda shi ne halin da al’umma suka samu kansu a ciki na matsalar tsaro. Inda ya ƙara da cewa: “Ita aikin hukumar kare haƙƙin ɗan Adam,…
Read More
Tsofaffin ɗaliban Kwalejin Kanta suna taka muhimmiyar rawa

Tsofaffin ɗaliban Kwalejin Kanta suna taka muhimmiyar rawa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Shugaban makarantar Kwalejin Kanta da ke Argungu a jihar Kebbi, Malam Hassan Yakubu ya yaba wa ƙungiyar tsofaffin ɗalibai bisa ga irin rawar da su ke takawa wajen kulawa da makarantar.Ya yi wannan bayani ne ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron shekara-shekara da ake gudanarwa a harabar makarantar. Malam Yakubu ya ce ya zama dole hukumar wannan makarantar ta yaba wa wannan ƙungiyar saboda a duk lokacin da wata buƙata ta taso tun kama daga shawara ya zuwa aikin ƙarfi da na  aljihu duk wanda aka kira domin gudunmawa yakan hanzarta aiwatar…
Read More
2021: Shekarar garkuwa da ’yan makaranta da hare-haren ’yan bindiga

2021: Shekarar garkuwa da ’yan makaranta da hare-haren ’yan bindiga

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Shekarar 2021 ba shekara ce mai daɗin tunawa ga miliyoyin ’yan Nijeriya ba, saboda irin abubuwa na tashin hankali, firgitarwa da taɓarɓarewar tsaro da suka faru a cikin shekarar. Wannan ba yana nufin kuma babu wani abu na farin ciki da ya faru a ƙasar ko a rayuwar wasu ’yan ƙasa da ba zai zama abin faranta rai idan sun tuna da shekarar 2021 ba. Amma dai ga akasarin ’yan Nijeriya ba a shiga shekarar da ƙafar dama ba. Idan abin mu yi ɗan tsokaci ne ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru cikin…
Read More
Nijeriya ta naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles

Nijeriya ta naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles

Daga WAKILINMU Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bayar da sanarwar naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles a ranar Laraba. Hukumar ta ce, Jose Peseiro wanda ɗan asalin ƙasar Portugal ne shi zai maye gurbin Gernat Rohr da ta kora. Tuni NFF ta naɗa Augustine Eguavoen a matsayin kocin riƙon ƙwarya domin ya ja ragamar Super Eagles a yayin da ake shirin soma gasar cin kofin Afirka. A cikin sanarwar da ta fitar NFF ranar Laraba ta ce kwamitin zartarwata ne ya amince da naɗa Peseiro ne bayan raba gari da Gernot Rohr. “Kwamitin ya amince…
Read More
An ja layin yaƙin siyasa tsakanina da kai – Mataimakin Gwamnan Zamfara ga Gwamna Matawalle

An ja layin yaƙin siyasa tsakanina da kai – Mataimakin Gwamnan Zamfara ga Gwamna Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rikicin siyasa a Jihar Zamfara ya ƙara ruruwa bayan da Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu ya ke gaya wa Gwamna Bello Matawalle cewa an ja layin yaƙi tsakanin su. Da ya ke jawabi a ƙarshen zaɓen shugabannin jam'iyar PDP na jiha a ranar Litinin da ta gabata da daddare, mataimakin gwamnan ya ce "yanzu fa ba ɗaga ƙafa." "Da ga yau, an ja layin yaƙi. Idan an kashe mutane kuma gwamnati ta yi shiru, to mu za mu yi magana. Idan gwamnati ta ƙi buɗe makarantu, za mu yi magana. "Hakazalika za mu magantu…
Read More
Idan ka cika namiji ka fito lokacin harin ‘yan ta’adda a garinku, inji Masari

Idan ka cika namiji ka fito lokacin harin ‘yan ta’adda a garinku, inji Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ƙalubalanci al'ummar jihar akan su daina ɓoyewa cikin gidajensu idan 'yan bindiga sun kawo hari a garuruwansu, madadin hakan ya buƙaci al'umar jihar da su fito su tunkari 'yan bindigar a duk lokacin da suke aikin ta'addanci a jihar. Masari ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin Muhammadu Buhari da ke zama fadar gwamnatin jihar Katsina a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai. "Idan kai namiji ne ka fito da dare mana lokacin da 'yan ta'adda suka kawo hari ba wai ka ɓoye ba da…
Read More
An ƙaddamar da kwamitin bikin miƙa sanda ga Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya

An ƙaddamar da kwamitin bikin miƙa sanda ga Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya

Daga BILKISU YUSUF ALI Ranar Asabar, 18 ga Disamba, 2021, aka ƙaddamar da kwamitocin da za su jagorancin bikin bayar da sanda na Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji (Dr) Aliyu Ibrahim Gaya (Kirmau Mai Gabas) a ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano kuma Wazirin Gaya, Alhaji Usman Alhaji. Taron da aka yi a ɗakin taro na Africa House da ke Gidan Gwamnatin Jihar Kano, an fara shi kusan ƙarfe 3:00 na rana. Sarkin Malaman Gaya, Sheikh (Dr) Yusuf Ali ne ya buɗe taron da addu’a. Daga nan sai jagoran taron, Alhaji Usman Alhaji, ya yi taƙaitaccen bayani kan maƙasudin taron…
Read More
Rubutu makaranta ce babba, inji Kabiru Jammaje

Rubutu makaranta ce babba, inji Kabiru Jammaje

"Ina da burin samar da abin da za a riƙa tunawa da ni" Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano  Idan ana maganar matasan da suka bayar da gudummawar su a duniyar marubutan littattafai da kuma yaɗa ilimi a cikin jama'a, to kuwa za a iya saka Kabiru Musa Jammaje a sahun gaba. Domin kuwa shi marubuci ne wanda ya fita daban a cikin marubutan da mu ke da su a ƙasar nan. Domin kuwa baya ga littattafai masu yawa da ya rubuta, ya yi amfani da damar in da faɗaɗa rubutun na sa zuwa aji na koyar da darasin Turanci domin…
Read More